Chapter 15

637 54 0
                                    

~~~

      Cikin ikon Allah su Mommy suka isa kd lafiya,Appa ta fara kira ta fad'a masa sannan Shettima se Aunty da Ummien Amrah.

      Shettima duk gidan yaji ba dad'i ya kira Amrah suka sha hirarsu.

        
     ***

     "Yake masoyiyata ina fatan kina cikin 'koshin lafiya ,ina ro'konki da ki taimakeni ki fito naga kyakkyawar fuskarki ko zan samu sukuni"Sa'kon Barr Kamal ya shigo wayarta.

     "Aiko sede bazaka samu sukunin ba".Tayi deleting text d'in.

             ★★★

    Washegari da yammacin asabar gidan ba kowa Aunty Hannatu bata nan Rahinatu da Husna ma sun fita se Shettima kawai dake d'aki system d'insa na gabansa yana danne-danne yaji shigowar Appa mey gadi ya bud'e masa gate.Tashi yayi ya le'ka window yaga Appanne dan haka ya d'akko data d'insa a drawer da Appa yace ya bashi domin sama masa gurbin aiki.Wata zuciyarce tace ya bari se anjima lokacin Appa ya d'an huta.

     1hr..2½hr ya bar abinda yake ya d'auki takardun zuwa sashen Appa.Sau biyu yayi knocking ba respond dan haka ya murd'a handle d'in yaci sa'a a bud'e 'kofar take.

     Wani irin tashi tsigar jikinsa tayi ganin Appa a kwance kan gado rigingine da completed kayansa kamar yanzu ya shigo kawai takalmine babu a 'kafarsa.

     A sanyaye Shettima yayi sallama amma ba amsa,gwiwa a sanyaye ya 'karasa jikin gadon.A take ya saki takardun dake 'kunshe a file yayi saurin 'karasa kan gadon.Abinda ya gani yasa tunaninsa ya d'auke na lokacin guda gefe guda kuma zuciyarsa tana fad'a masa 'karya ne.Kumface cike a bakin Appa harta gangaro ha'barsa.

     " Ap..pa..."Ya girgiza kafad'arsa.

      "Ap..pa ka tashi" Ya sake fad'a.

    Ganin da gaske de ko numfashi baya yi ya soma 'ko'karin d'aukansa amma sam ya kasa saboda Appa yana da jiki kansa kawai ya iya tallofawa,seda taimakon mey gadi suka sakashi a mota,tu'kin yake kawai badan yana ganin hanya ba, da ikon Allah suka 'karasa asibiti.Emergency akai dashi ya rasa inda zesa kansa mey gadi yana ta 'ko'karin kwantar da hankalinsa amma ya kasa.

     Ya dafa kai ya sauke ya zauna ya tashi ya rasa inda zey tsindima kansa lissafinsa ya jagule ,be ta'ba shiga tashin hankali ba irin yau.Baba mey gadi ne ya dafa kafad'arsa hakan yasa ya juya yaga doctor d'in ya fito daga d'akin da aka shiga da Appa.

     "Doctor.. ya ya..ke babu komai ko?" Ya jefo masa wannan tambayar.

     Likitan kansa jikinsa yayi li'kis ,soyake ya nemo kalmar da zata dace da abinda zey fad'a ko wannan saurayin zey samu relief.

    "Likita meya sami Alhaji?" Baba mey gadi ya tambaya.

    "Ina baku ha'kuri da abinda zan fad'a,wannan patient mun rasashi Allah ya kar'bi abinsa"

    "Innalillahi wainna ilaihirraji'un" Baba mey gadi ya furta.

   Shima likitan hakan ya fad'a ,Shettima jikin bango ya jingina dan 'kafarsa ta kasa d'aukansa tafin hannunsa ya d'ora ya rife bakinsa.Kuka ma idan yayishi zey samu sau'ki amma babu ko kukan duk wasu ilahirin injina na jikinsa masu kai za'konni seda yaji sun tsaya bayaji baya gani idan mafarki yake baya burin ya sake yin makamancinsa dan Allah ya tashi.Wannan shine abinda kawai yake ji a 'kwa'kwalwarsa.

        -------------------------

    Suna zaune a parlour sunyi jugum -jugum shida Uncles d'insa guda biyu,'karfe 9:30pm ,Aunty tana d'aki itada su Rahinatu da wasu matan 'yan uwa dasu goggo se basu baki sike siyi shiru amma sin'ki sassautawa hakan yasa ma Kawu yasa su koma sama muddin suna ganin gawar Appa bazasu bar kukan ba.

    Babban tashin hankali Mommy batada labari har yanzu sede Uncle yayi waya da driver ya sanar masa duk yadda ake ciki,su komo a gobe as early as  he can amma karya fad'awa Mommy.

   Itade Mommy tunda driver yace mata gobe zasu koma hankalinta ya kasa kwanciya ta tambayeshi dalili ya'ki fad'a kawai de yace mata Kawu ne yace su dawo jikin goggo ne, dan haka ta kira number Appa ba'ai switched off ta Shettima ma kashe,Aunty ma a kashe Rahinatu a kunne amma bata d'aga ba.

     Maganar doctor ce ta tsaye masa a rai sanda yake magana dasu kawu bayan sinje asibiti"Poison patient d'in yasha"

     Da duhu-duhu suka d'akko hanyar kano kowa zuciyarsa na sa'ke-sa'ke yawanci tunaninsa ma ko Goggon mutuwa tayi amma de ba wanda ya fad'i tunaninsa,ji sike kamar siyi tsalle su gansu a kano.

      ***
     
       Seda suka iso kano wani sabon tsoron ya sake ahigar Mommy kawai daurewa take amma jikjnta ya gama mutuwa ba abinda yafi damunta kamar rahin d'aga wayar tasu at least de ai wani ya d'aga.

     Mey gadi a sanyaye ya bud'e gate driver ya danna kan mota suka shiga,kowa a 'kage yake ya fito ba 'bata lokaci suka firfito.

     Ganin mutane dake gidansu zey basu amsar rasuwa ce amma waya rasu? Goggo itace amsar kowannensu.Wafah da Walida suka ri'ke hannayen juna Sa'adatu tana ra'be jikin Mami ,jugum-jugum family na kallonsu an rasa ta ina za'a soma musu.Babban yayan Mommy da Kawu ne suka tare Kawu ya wuce da yara ciki,Yayan Mommy kuma ya tisata a Baba suka bi ta 'kofar baya.

      A parloun ba'ki ya zaunar da Mommy,haka ya daddage ya soma mata bayani mey kashe ilahirin jiki.

      Yaran ma ta haka aka zaunar dasu aka sanar musu ana yi ana lallashinsu dukda kuwa a lokacin ba aiki zeba.

      ***

    Yayan Mommy tashi yayi ya bata guri dan ya kasa jure ganin halin da ta shiga,Shettima ne ya sakko d'aga d'aki dayaji su Mommy sin dawo,parlourn ba'kin ya nufa inda aka fad'a masa tananan.

    Ashe dama kukan nasa yana ma'kale a wuya ganin Mommy yasa shi fashewa da wani irin rikitaccen kika mey tsuma jiki,cikeda tausaywa juna ya fad'a jikasibitin rungumeshi😭

     Na kasa arasawa nima kukan nake....mey yake shirin faruwa? taya Appa yasha poison? How ? Why?

    Comment

Dijensy❤

    

     

    

    

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now