Chapter 44

561 47 0
                                    

           _*My ppl kuna 'kullen ciki da dariya,harda masu yiwa  Aunty Hannatu karaya goma😱*_
 

   8:36am agogon bangon d'akin ya nuna be zaci yayi bacci tsahon lokaci haka ba,kamar yadda ya qudura yau gari na wayewa zey jajibi abokinsa ya kaishi gida.Sanda ya shiga d'akinsa baya nan yayi tunanin ko yana bayi ,ganin 15min ya shige yasa ya duba sede ga mamakinsa Shettima baya ciki ,parlor ya fito nan ma baya nan gidan kaf ya karad'e baya ciki.Shiko ina yayi? Kuma gashi de motarsa tana inda take a compound d'in gidan.Allah yasa de ba tafiya yayi ba wani wajen inda baza'a sameshi ba tunda yaji jiya yana ce masa zey kaishi gida.Sosai Ahmad ya shiga damuwa cikin sauri ya d'akko key d'in mota ya fita dubashi.

      Gani yake kamar baze 'karasa gida ba ,traffic data tsareshi  a titin da ko rabin tafiyar beba haka ya sauka daga d'an sahun ya sallemeshi.Da'kyar yake numfashi inda Allah ya taimaka ma babu rana sosai garin lumshi-lumshi ne. Sosai ya galabaita kawai tafiya yake burinsa yaga Mommy kafin ya mutu ,the more yana 'kara saurin tafiyarsa the more yana jigata tari ya fara cin 'karfinsa yana tafe hannunsa a 'kirji ,tafiya mey tsaho yayi kafin ya ganshi a 'kofar gate d'in gidansu gidan da beyi tunanin sake dawowa ba.A gaggauce ya tura 'kofar Allah yasa a bud'e take,kamar zey kifa haka yake takawa.Baba mey gadi yana d'akinsa yajiyo shigowar mutum aiko ya fito cikeda mamaki da farinciki lokaci guda kafin ya 'karasa harya shige ciki.

      Walida,Sa'adatu,Husna da Wafah duka suna d'aki jugum jugum kowa beyi isashshen bacci ba gwara Husna datake yarinya bata gama mallakar hankalinta ba.

      Mommy da kuwa daren jiya kwana tayi tana kai kukanta wajen Ubangiji,tana zaune kan abin sallah kamar wadda aka 'bincina zimbir ta mi'ke,tamkar ana bata order ta fita daga d'akin ta fita zuwa parlour. Marmar tayi da ido tanaso ta tabbatar gizo yake mata ko kuwa gaskene.

    Zuwa yanzu 'kafarsa ta gaza iya takawa babu sauran energy a jikinsa.Dayake doguwar  abaya ce a jikinta seda ta d'an tattare ta  dan gani take kamar bazata iya sauka daga benen ba,kamar wal'kiya na ganta a gabansa.

    "Shett.." Bata 'karasa ba saboda sulalewa 'kasa dataga yana shirin yi, a tare suka zube 'kasa kafin Baba mai gadi ya taresa ta  kan'kame d'anta a jikinta rabinsa a kan cinyarta tamkar d'an baby ta ru'kun'kumeshi kamar zata maida shi ciki.Hawaye tuni ya wanke mata fuska ,extremely tausayin d'anta ne kawai yake ratsa ta .Ganin yadda fuskarsa ta kod'e yayi wani fari fat ,babu tantama Shettynta baida lafiya amma tun yaushe? Meye sameshi ? Duk a dalilinta?

    "Shettyna?"Ta d'ora hannunta kan fuskarshi ,kallonta kawai yake bakinsa yana motsi amma ba'a jin meyake fad'i.

     " Dan Allah ka yafemin ,Shettima nasan komai bana bu'katar bayaninka ........bakai komai ba Shettima ...nasani bakada laifin komai d'ana.... bazan sake bari ka tafi ba kaji Shettyna?"

       Maimakon amsa se hawaye ne ya gangaro daga idanunsa,a wahalce ya sakar da guntun murmushi yana girgiza mata kai wanda bata fahimci mey yake nufi da hakan ba seda ya d'aga hannunsa na hagu da 'kyar ya d'ora a kumatunta yana share mata hawaye,'karshen karyewa zuciyarta tayi ada kukanta bame sauti bane amma yanzu kukanta ya tsananta kamar 'karamar yarinya.

      "Ki ..bari ...pls"Yayi maganar can ciki da 'kyar ake fahimta .

  
    Yanaso ya sake magana amma ya kasa sake fad'in komai ga duhu-duhu dayake neman rife ganinsa.Cikin rikici ta fara kiran sunansa ganin yadda idanunsa yake 'ka'k'kafewa,hannunsa dake fuskarta ne ya fad'i 'kasa kafin idanunsa su rufe.

      "Shettima! Shettima!" Ta shiga girgiza shi.

    Dede lokacin su Wafah suka sakko 'kasa ,kowa ya shiga rud'ani Baba mey gadi ne ya bada gudumawa aka sashi a mota Mommy tana baya da d'anta Walida a gaba mey gadi a gidan driver Wafah aka barta dasu Sa'adatu da suke ta sharar kuka.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now