Chapter 19

580 44 0
                                    

Fiddausy wannan shafin naki ne ke kad'ai ina jin dad'i yadda kike comments akan littafinnan.Ana tare✌

~~~

Mommy tana d'aki zaune kan sallaya ta jingina kai da gado.Maganar bacci babu ita tun bayan rasuwar Appa bacci ya qaurace mata a ido.

Wani abu daya sake tayan mata da hankali shine yadda wasu daga cikin 'yan uwan Appa suka rufe ido su a lalle Mommy tana da hannu a cikin wannan lamarin dama ta ciki na ciki a koyaushe gani suke Mommy ta malleke d'an uwansu komai d'anta Shettima ,suna samun labari na poison da aka gani d'akin Shettima suka gasgata yanzu a halin da ake ciki suna son mi'ka case d'in court.

Goggo da Kawu ne kad'ai suke goyon bayan su Mommy hakan ya samo asali ne da kasancewar Kawu d'an goggo ne 'kanwar mahaifiyar Appa dan haka cousin suke da Appa.Sukuwa sauran da suke uwa d'aya uba d'aya da Appa sune masu nema a biwa d'an uwanansu ha'kkinsa fafur sun rufe ido su Mommy ta kashe musu d'an uwa.

________________________

"Zan iya yin komai a kanki muddin hakan ze zamo farinciki a gareki.Barr Kamal.

Tana kwance hawaye ne kawai ya tsiyayo a idanunta ,wayar ta ajje gefe ba tare da ta fahimci sa'kon ba.

Yau kwana uku bata ji muryar Shettima ba balle sanya shi a idanunta.Ummi taje yiwa Mommy jaje itakuwa 'kin zuwa tayi dan tasan muddin taje ba abinda zey hanata yin kuka.

***

Aunty tana d'akinta daga jikin window ta hangi shigowar mutum cikin gidan bayan da Baba mey gadi ya bud'e masa 'kofa.Sanye yake cikin suit black da necktie grey.

" Ya 'karaso kenan"Ta fad'a.

Maida labile tayi ta rufe ta yafa mayafi ta fita, a premises ta iskeshi.Ganinta yasa yayi murmushin gefen fuska kafin ya 'karasa.

"Barrister Kamal .I. Al'kali" Ta fad'i sunansa tana 'kare masa kallo.

"Haka sunan yake"Ya fad'a.

" Nayi tsammanin zuwan ka da wuri ,wannan lawyer akwai late "

Murmushi yayi yace"Wannan matar akwai zumud'i"

Shiru tayi bata sake fad'ar wani abun akai ba ta chanja topic dan ta lura idan ta fad'i A seya fad'i B.

"Ina so ka....."

"Fad'a 'bata lokaci na riga da nasan komai base kinyi min bayani ba"

"Don't fail me ,ka tabbata ka fad'i a case d'innan"

"Hmm yanzu de ina. ...."Ya murza yatsinsa biyu alamar $.

" Toh ai ka bari na gabatar da kai gurin mahaifiyarsa koh?"

"Haka".

Iso tayi masa zuwa parlourn ba'ki inda ya kasance a yanzu ba kowa ciki ,fita tayi zuwa d'akin Mommy.

A kan dadduma ta tarar da ita tayi raising palm alamar addu'a take.Ta'be baki tayi tayi sallama.

Ganin Aunty yasa tayi d'an guntun murmushi tace ta 'karaso.

" Dama zuwa nayi na sanar miki lawyer yazo"Tayi maganar bayan ta zauna kan couch.

"Auntyn yara kina ganin..."

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now