Chapter 65

717 44 1
                                    

  
      Zuwa yanzu yaransu Walida da Wafah sunyi wayo sosai ,'yar wajen Wafah nada  wata bakwai  d'an Walida Ameer ya shiga wata na hud'u yaran gwanin sha'awa sunyi 'yan ku'bul-ku'bul.

   Amrah a yanzu itama ta soma sha'awar samun nata babyn,se ma idan taje gidansu ko suka had'u a school idan taga yaran setaji  dama itama tana da nata.Tun abin baya damunta yanzu ta soma sawa a ranta wani sa'in zuciyarta tana 'kesa mata kode itama tayo Umminta ne 'kila itanma dama haihuwa d'aya Allah ya nifeta tayi watoh idan ta tuna ta ta'ba yin 'bari a gidan Kamal kenan hakan yana nufin d'a d'aya zatai kuma gashi cikin ya zube mean yanzu bazata sake samun wani ba?

     "Ya Allah". Ta furta tana daga kwance ta jingina kanta a pillow,'kwallar data taru a idanunta ce ta gangaro.
    
      " Amrah".Ya kira sunanta yana daga tsaye jikin 'kofar d'akin.

         Hannu tasa tayi saurin goge hawayen ta mi'ke zaune tana 'kwa'kwolo murmushi."Ka dawo ?"Ta fad'a tana duban agogon taga 2:30pm wanda ba lokacin dawowarsa bane.

    "Mey kike tunani haka bakiji ko shigowata ba? nayi sallama ma baki amsa ba"Yayi maganar yana takowa inda take.

    Saurin girgiza kai tayi tana fad'in " A'a banji bane,sannu da dawowa".

   Daga bakin gadon ya zauna gefe da ita yana 'ko'karin gano wani abu a fuskarta tayi saurin kawar da idanunta amma tuni ya gano tayi kuka.

   "Kuka ? Meya faru babyna?"Yayi maganar yana aza hannunsa biyu a fuskarta.

    " Babu".

     "Haka kawai se ayi kuka ba wani abu,bama wannan ba tun kafin na fita dama na lura dake ba yanda na saba ganinki ba koyaushe mey akai miki? Koh ni nayi laifin?"

    Kai ta girgiza ba tare data ce komai ba.

    "Toh ko makarantarce ta isheki?"

     "A'a".

      " Toh ki fad'a min I'm here for you ,kinsan matsalarki ta shafeni koh?"

   
   "Ba period d'ina bane yazo yau ba".Yanda tayi maganar kamar zatai kuka.

    Idanuwa ya zuba mata yana kallonta shide yasan bata ta'ba irin haka ba akan period kuma ma ai dama a lissafen lokacin zuwan shi d'inne.

    " Toh matsalane gameda hakan kuma Amrah? Ina dama lokacinsa neh?"

    Bata iya sake fad'ar wani abu ba se hawaye tarr kamar an kunna fanfo,kwana biyar dataga ta 'kara  tayi tunanin koda bayani amma kuma segashi yau ta tashi dashi shiyasa gabad'aya hankalinta ya sake tashi ta sake gasgata abinda zuciyarta ke fad'a mata.

    "Innalillahi meye hakan Amrah ? Mey ne na kukan ? Mey kike tunani?"

    "Ni bazan ....samu.... baby ba kenan".Yadda tayi maganar a rarrabe ta  'kare da jan hanci tana goge hawayen da bayan hannu.

     " Wannan shine daliilin dayasa kike 'barnatar da hawayenki? lalle".Ya ma rasa mey zece.

    "Toh ke waya fad'a miki haka? Duk wanda kiga ya haihu Allah ne ya bashi haka wanda be haihu ba Allah ne ya tsara masa hakan ba dan baya sonsa ba ,har yaushe ma akai dad'ewar da zaki dinga wannan tunanin? Ni kinganni ban ta'ba wannan tunanin ba ,ke har kin gaji da cin amarcin haka?" Ya 'kare maganar tare da 'bincininta a 'kwi'bi cikeda zolaya.

    Murmushin daba ta shirya ba ya su'buce,damuwarta taji ta nema ta rasa harma taji haushin kanta na wannan tunanin abinda ma ko shekara biyu ba'ai ba a 'kalla bazasu wuce 1year da watanni ba'kwai da aure ba.

   
   "Kin manta?" Ya tambayeta yana d'age gira.

   "Mey?"

     "Bakiga na dawo da wuri ba?"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now