Chapter 20

593 41 1
                                    


Hurray!🎉🎉 happy page 20 guys🎊🎊🎈🎈

~~~

"Mommy pls ki tashi kici abinci ko yaya ne kisha magungunanki" Wafah tayi maganar tana zaune gefen gadon Mommy ta juya baya.

"Wafah" Ta kira sunanta.

"Na'am Mommy"

"Ni 'yar mitsitsiyar yarinya ce ko mey kika maida ni?"

"A'a Mommy amma fa Mommy kinsan rashin shan magungunannan matsala ne kuma bama jin dad'in ganinki..cikin wannan halin" Ta 'kare maganar kamar zatai kuka.

Shiru Mommy tayi tana jin tausayin yaran nata dan su kansu suna bu'katar rarrashi,suna yin iya 'ko'karinsu na suga tasha maganin hawan jininta daya tsananta a kwanakinnan.

"Kije zansha"

"Tahm" Ta fad'a kafin ta fita daga d'akin.

Seda ta tabbata ta fita sannan ta mi'ke zaune,tray d'in dake kan drawer ta kallo gefe ga magunguna.Hakan seya tuna mata da Shettima wani lokaci da dad'ewa befi 9 ba sanda tayi rashin lafiya tana kwance a gado ya kawo mata abinci da magani akan tray d'in.Ba jimawa da shigowar tashi kuma sega Appa shima ya shigo ,haka suka sata a gaba dole taci abinci tasha magani.

Presently

Hawayene ya 'kwaranyo a idanunta , ta dubi d'akin empty kamar hakan be ta'ba faruwa ba.Hakannan ta share hawayen ta jawo tray d'in ta soma 'ko'karin cin abincin ,da'kyar take had'iyar lomar tana ci tana share hawaye,tana so ta tursasa kanta ci saboda su Walida ,hakan ba 'karamin dad'i zey musu ba ,tana so ta dawo musu da walwalarsu ta da.

_______________________


Amrah ba kamar koyaushe ba yau tasa waya a gaba tana jiran kira na Barrister ,she can't wait a fitar mata da Shettiman ta.

Se wajen 5pm sega kiransa ya shigo tana daga parlour wayar na d'akin kamar 'kiftawar ido tayi sauri ta shiga d'akin kafin ta katse ta amsa.

"Assalamu Alaykum"

"Waalaikumussalam" Ya amsa fuskarsa d'auke da murmushi.

"Kazo?" Tayi saurin tambaya cikeda zumud'i.

Kasalallan murmushi yayi jin tambayar da tayi masa.

"Yes ina 'kofar gida"

"Gani".Tayi saurin ajje wayar tana sauri ta zira milk colour hijab d'inta.

Ganin Ummi bata tsakar gida ta fice a ranta tana fad'in idan ta dawo zatai mata bayanin komai.

Idanunta a 'kasa ta fita tana ganinsa tsaye jikin motarsa ta gefen ido,kunya duk ta lilli'beta tana jin haushin marinsa datai na rannan.

Har ya 'karaso inda take bata d'ago ta kallesa ba.

" Ina wuni"Ta gaisheshi.

"Mun wuni lafiya".

" Long time no see"Ya fad'a.

Itade shiru tayi batace komai ba tana jira ya soma maganar dake tafe dashi.

"Already jiya minyi magana Amrah ,sede kin manta baki tambayeni wane tukuicin za'a bani ba"Idonsa a kanta yai wannan maganar bako 'kifta ido.

D'an dumm taji a jikinta ba tare da ta fuskanci maganar tashi ba tace"Tukuice kamar ya?" Se yanzu ta d'ago ta kallesa.Suna had'a ido ta sauke nata.

"Nasan kin manta da batun tukuici wanda ya kamata ace jiya dana fad'a miki 'kuduri na kin tuna amma ba damuwa ,daman shiya kawo ni nan".

"Ni a ganina bazan iya biyanka wannan taimakon da zakai ba sede nayi maka kyakkyawar addu'a da godiya"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now