Chapter 43

549 44 0
                                    

       
        Kamal da suka shiga asibiti emergency suka rankaya ya bari a d'orata a gado kafin a shiga d'aki da ita ko sauraronsu ya'ki da kanshi ya kwantar da ita a gadon d'akin seda 'kyar ya fita daga d'aki ya tabbatar da mace zata duba lafiyarta.Minti goma da shigar da ita likitar  ta fito.

    "Ki gaya min meya faru da ita ya take Amrahta karki ce mini zata barni..." Ya shiga jero mata tambayoyi.

    "Yalla'bai ka kwantar da hankalinka zata farka nan bada dad'ewa ba ma..." Katseta yayi da "Toh meya sameta?"

   "Gaskiya ina ganin miscarriage ne...."

     "Dakata ,karki 'karasa mey ba'kin baki watoh kina zato ne ma baki tambatar ba saboda da'ki'kanci haka aka koya miki aiki?"

    "Mallam...daga ina maka bayani ...baka ko bari kaji ragowar maganar ta ba Yaya zamu tabbatar idan ba'ai scanning ba?"

    "What's going on Dr" Wani daga jikin jami'an lafiya ya tambaya sanda ya 'karaso wajen.

   Bayanin duk abinda ya faru tayi masa jin tace scanning dama fanninsa neh matashin "Yalla'bai ba damuwa ka 'kara ha'kuri yanzunna zanyi mata scanning kaga se'a tabba....."

     "Uwarka zaka tambatar ? Kai sagari dakai ,kai zan bari ka ta'ba min mata Allah ya sittira".Yana gama fad'in haka ya fad'a d'akin suka bishi da kallo baki sake.

    Haka ya kinkimo abarsa ya fice musu daga asibitin ba wanda ya tsaida shi,haka ya sanyata a mota ya bar asibitin wani clinic ya kaita direct wajen scanning aka nufa da ita,daru ya sa seya shiga d'akin scanning d'in.

    Nan d'in ma wani matashine zeyi scanning Kamal yana tsaye yana kallon gudun ruwansa ya gama arranging d'insa so yake yaga hannun da zey ta'ba masa Amrah.

      "Kada ka kuskura ka d'ora 'kazamin hannunka a jikinta".'karasowa yayi wajen gadon " Matsa ai nima zan iya nasan harkar lafiya ba ban sani ba ka fad'a min duk yadda zanyi  ya amshe abin da za'ake mulmulawa a cikin.

   Dayake matashin mey sau'kin kaine kuma yana tunanin ko duk de zafin kishi ne seyai  masa bayani.

      "Juya"

       Abinka da besan mey yake wakana a ultrasound  (machine dayake nuna hoton) ba kawai kalla yake"Mey hakan yake nufi?"

     Shi daya san kan aikin ya gano babu ciki a tare da ita ya gama zubewa."Yalla'bai  babu ....

    "Babu mey?"

      "Wannan it's a complete abortion babu wani abu dayai saura dan haka ba damuwa zasu bata 'yan wasu magungunan ne" Ya 'kare maganar hankali kwance dan be kawo wani abu a rai ba shi a tunaninsa ai murna ma zasu base an mata wankin ciki ba ko wata d'awainyar tunda arbotion d'in yazo da sau'ki.

      _Tun yaushe Amrahn sa take da cikinsa jininsa be sani ba ,his love of his life amma yanzu sun rasa babynsu pretty kamar Amrahnsa_

    Harya gamo d'asko yarda babynsu take ma yadda zasu raine ta,tuna cewa ance masa cikin ya zube yasa ya dawo daga duniyar tunani.

       Kallon daya soma jifan matashin dashi yasa ya sha jinin jikinsa wani abu daya bashi tsoro ganin yana tunkaroshi ,baya baya ya dinga ja har seda ya kaisa bango.

    Hannu biyu yasa ya ma'kure wuyansa cikeda azaba  ya soma magana."Yalla'bai mey nayi meye a ciki kaifa kai scanning d'in"

    "Meyasa zakace d'an mu ya mutu?"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now