Chapter 10

934 74 0
                                    

   Kamar yadda tayi tsammani tana juyowa taga Shetty abinda take gudun de ya faru.

     Tana tsaye ya 'karaso inda take fuskarsa d'auke da 'kayataccen murmushi yace.

     "Wai yanzu saliha kika zama ne ko duk boarding d'ince bata sake ki ba?".

     Shiru tayi bata ce ko 'kala ba ta 'ki bari su had'a ido.

    " Ina kika shiga tun d'azu ana ta hotuna babu ke?"Ya sauya wata tambayar.

   "D'akin Mami" Ta amsa a ta'kaice.

     "Rowar 'kwalliyar taki kike mana?"

      "Amrah!" Tajiyo Mami ta 'kwala mata kira.

      Cikin sauri bata ce komai ba tayi sauri ta 'karasa kitchen d'in ta barshi a tsaye.

   Kallo ya bita dashi yana murmushi kamar wani soko.

    A kitchen ta tarar da Walida dasu Ummie se wasu 'yan mata da bata sansu ba guda biyu.Trays ta gani dayawa an jera cups cikeda fura da nono.

    "Irin wannan 'kyau haka Amrah shine tun d'azu kika 'buya a d'aki ba'kyaso aga 'kwalliyar taki"

    "A'a ba haka bane ban dad'e da gama shiryawa bane"

     "Kunga wannan hirar ba 'karewa zatai ba ,yanzu ku d'auki wannan ku fara mi'kawa ba'ki".Ummie ta fad'a tana nuna musu trays d'in.

    Dukansu kowa ya d'auka d'aya suka fita suna 'yan hirarrakinsu banda Amrah da hankalinta baya gurin.

    Shettima kawai take ta tunawa ganinsa cikin manya kaya da be fiya sawa ba.Light blue shadda ce mey aiki tanfatsetse da hularsa ta tsaya dass se walwali take.

     " His smile... His eyes...his jokes..."

     "Amrah kula" Walida ta fad'a.

    Da sauri ta dawo daga nisan tunaninta seyanzu ta lura da pillar data kusa buga,murmushi ta saki involuntary tayi sauri ta tari inda suke.

         -----------

       Amrah wajajen 6pm ganin Ummie zata tafi gida ta  yafa gyale itama da niyyar binta su tafi aikam Mommy ta hanata tafiya ,maganar Walida ma kad'ai ta isheta ta zauna.Haka tana kallo Ummie ta tafi,tana cikin 'yan matan biki a d'akinsu Wafah amma ta'ki sakewa sede idan anyi abin dariya ta murmusa  gashi charge d'in wayarta ya 'kare ba game kuma duk charger na d'akinsu Walida a jone sike da wayoyi.

       Har 'karfe 12:45am suna hira bame shirin kwanciya (kunsan irin hirar 'yan matan amarya) wannan tace waccen tace.Wata daga cikin 'yan matan ce ta tambayi Amrah  'karfe nawa ganin phone d'inta a hannu.

    "Wayar babu charge" Ta bata amsa.

    Walida dake zaune tace "Ba charge kikai shiru kuma?"

     Mi'kewa tayi ta kar'bi wayar Amrahn ta duba a cikin chargers na wajen zata cire ta wata waya meshi ta hayayya'ko.
 
    "Befi 20% fa nake dashi ba zaki ciremin".

     " Dallah chan  karki cinyeni na tuna ma,keda charging naki bame lassese ba itako nata mey lasses confirm se wayarta ta chargu idan anayi har sama da 100% tata se anyi mata"Walida ta fad'a tana mayar mata da charge d'in.
   
    "Bari na kai miki wajen yaya Shettima".
      
    Dariya suka qyalqyale dashi  danko dayawa sunyiwa maganar fassara wasu kuma basu d'arfo komai ba.Itade Amrah fatanta Allah yasa Walida ta tsaya da maganar a iya haka karta sake d'orawa da wani abun dan ko a yanzu jitake kamar ta nitse a 'kasa."

    (My ppl ku wace fassarar kukayi??👀)

      Tana fita ta wuce d'akin Shettima tayi knock,kusan sau biyu ba respond dan haka ta murd'a handle ta shiga.Yana bacci ta ganshi kan gado ,wajen drawer na charger d'insa taje dukda taga wayarsa na charging amma ta tsige tasa ta Amrah sannan ta komo d'aki ta tarar sun fara shirin kwanciya....

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now