Chapter 59

746 49 4
                                    


*So sorry my ppl 2days ana samun 'yan mishkila ne,ga WATTPAD ma yana rashin M*

        Kanta a sunkuyen zuciyarta na harbawa ta amsa sallamar cikin siririyar muryarta.

    Yana sanye da ash colour shadda hularsa tayi matching da kayan.Yau de gashi ga Amrahnsa finally ta zamo matarsa abinda ya fidda rai a da, be ta'ba kawo wa zasu kasance tare ba.

     Takawa yayi zuwa inda take daga gefenta ya zauna yana kallonta,mayafin daya rufe fuskar tata ya d'age zuwa saman kanta murmushin fuskarsa ya sake fad'ad'a.

    A kunyace ta sake yin 'kasa da ido ,ita kanta tana mamakin yadda Shettima yake mata kwarjini sekace ba abokinnan nata ba.

    "My star light ki taimaki zuciya taga wannan kyakkyawar fuskar da kyau".

     Yatsun hannunta kawai ta shiga wasa dasu bata ce komai ba.

     Dama da alwalar ta saboda haka dayace zasi sallah kawai takalmin 'kafar ta cire ya shinfid'a musu dadduma suka gabatar da sallah sukai adduo'i.

    Fita yayi ya zauna 'kasa kitchen ledoji guda biyu daya shigo dasu ya d'akko plate ya zube gasassan kazar dake ciki ya d'ora a tray ya ciro sanyayyen fura daga d'ayan ledar a cikin fridge kuma ya ciro juice shima sannan ya d'ora da glass cup guda biyu.

     Tana zaune inda ya batta kan daddumar,opposite da ita ya zauna bayan ya ajje trayn.
    
      "Wanne kike so fura ko juice?"

       " A'a ni bana jin yunwa". Tayi maganar tare da girgiza kai,tana 'kare maganar se hamma ba tare data shirya mata ba.Dama tana jin yunwar dan tun wajen 2 rabonta da abinci.

    Murmushi yayi mai d'an sauti kafin yace"Gaskiya ta bayyana".

    Murmushi da kunya ce ta had'e mata lokaci guda.

    Seda ya d'an nad'e  hannun rigarsa ya d'ibi naman ya kai bakinta "Ahh".

    Kamar bazata bud'e bakin ba kuma seta bud'e,seda ya tabbata ta 'koshi ya barta ya d'auki juice d'in ya bata furar kwa tace ta 'koshi.Shikuwa furar kawai yasha beci kazan ba,bayan ya wanke hannunsa a bayi ya sauka 'kasa ya maida trayn ya dawo.

     Kafin ya dawo ta tashi ta shiga bathroom d'in ta wanke fuskarta ta dawo ta koma kan sallayar.

     Beyi tunanin sake ganinta kan daddumar ba amma ya ganta again ta zagaye hannunta kan gwiwa tamkar wata ba'kuwa kodayake ba'kuwar ce amma ta dindindin😁

     " Amarya har yanzu de nan d'in de"Yayi maganar yana wani murmushi.

     Yanzu ma wata hammar ta sake yi yanzu amma de ta barci ce.

    "Bacci?"

     Kai ta gid'a alamar eh."Zaki bacci yanzunnan kuwa amma a bari cikin ya d'an fad'a koh?"
     
     "Eh".Ta fad'a.

      " Toh taso mu zauna ki bani labari kafin ki kwanta".Ya mi'ka mata hannunsa.

     Seda ta d'anyi jim sannan tasa hannunta a tafin hannunsa ta mi'ke tsaye bata ankara ba taji ta fad'a jikinsa.Nan da nan ta shiga warware ido ta kasa motsi ,ita dama abinda take gudu kenan.

     "Mrs Shettima easy mana labari fa kawai nace kiban jibi yadda kika firgice dama haka Amarya takewa ango?"

      Hannunsa d'aya ya zagaye waist d'inta d'aya kuma yana ri'ke da hannunta.

     "Bacci fa nake ji". Ta tuna masa.

      " Nima ai baccin nake ji".

       Raurau ta shiga da ido har yanzu bata dena raba idanu ba.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now