Chapter 47

660 46 4
                                    

    
       Ummi ce ta bud'u baki tace "Kin'ki cewa komai ki bud'e baki kiyi magana".

    " A rabu da ita idan ta'ki magana bari na kira Kamal d'in a waya"Abba yayi maganar yana ciro wayarsa a aljihu"

    Aunty Mirah duk ta shiga hargitsi ta rasa gane kan lamarin ,idan bata manta ba sanda sukai waya da Amrah data tambayeta waye zey kasheta sunan Kamal  ta ambata.

       Ummi ce ta maida kallonta kan Aunty mirah dake zaune kan wata kujera a d'akin."Amirah a ina kuka had'u ne ?"Ta tambaya tunda de d'azu taga suka rabu da ita.

    Abba sau biyu yana kiran wayar Kamal d'in amma a kashe ake cewa "Kinga Kamal d'in ma wayarsa a kashe"

    "D'azu bayan mun ajje ki mun koma gida ban shiga gida ba naji rurin
wayarki ,dana duba senaga Amrah ce ta kira ,koda na d'aga senaji tana kuka tana cewa azo a taimaketa wani zey kasheta sunan danaji ta ambata Kamal,nida maigidana muka je gidan nata bayan tayi masa kwatance a cikin wannan yanayin nima na sameta ta kulle kanta a baya seda mukaje ta fito shine na kawota gida, shikuma mijina na baroshi a can shida wancen mutumin da yake 'ko'karin kasheta".

    Jinjina kai kawai suke kowa da abinda yake tunani ,abin ya d'aure musu kai dukansu saboda sunan da Aunty Mirah ta ambata d'in.

    " Abinda ban gane ba shi Kamal d'in ne wai zey kasheta? "Abba yayi tambayar.

    " Sunan data fad'a min kenan amma kuma maigidana ba da haka ya kira sunan Wanda muka tarar a gidan ba"

    Ta sake rikitar dasu, Ummi ce ta sake maida kallonta kan Amrah."Ki fad'a mana meyake faruwa!"

   "Tunda ta'ki fad'a bari na barku da ita wata'kila zatai magana". Cewar Abba ya fita daga d'akin.

    Aunty Mirah ma tashi tayi zata fitan Ummi ta tsaidata." Koma ki zauna ke d'in ba'kuwar mu ce?,keda kuka je har gidan nata mey kuma zata 'boye miki?".

     Dawowa tayi ta zauna kamar yadda Ummi ta bu'kata d'in.

     Kamar wacce aka d'ora mata dutse a baki haka ta soma magana cikin rawar murya.Ummi tun tana tsaye harta zaune gefen gadon ,labari ta shiga zayyano mata tun farko had'uwarta ma da Kamal d'in har e zuwa sanda ya bujuro mata da maganar aurensu. Daga Ummi har Aunty Mirah jinjina kai sike suna mamakin wannan lamari ,daga baya Aunty Mirah itama hawaye ta shiga yi tausayin Amrah ya kamata    matu'ka.

       Da'kyar ta iya 'karasa labarin saboda kuka dayaci 'karfinta Ummi kuwa tuni ta 'kule haushin Amrah ya cikata batasan wani wawancinne yasa ta'ki sanar musu ba suda suke iyayenta.
     

       "Kukan kuma na meye? Bayan kekika siyawa kanki yayi kyau tunda ke daga sama kika duro bakida wanda zaki fad'awa ,iyayenki zaki 'boyewa irin wanna zancen saboda sakarci da wauta irin taki ,'yar shekara 15 bazatai wannan abun ba wani seya d'auka yarinyar 'kauyace tamkar bakida ilimi!"

   Ummi kamar zata ari baki haka ta dinga sibirbid'o fad'a ranta ba 'karamin 'baci yayi ba kamar zata kaiwa Amrah duka.

   "Ai Amirah da kun barta baku je gidan ba kinga seya yi miki irin yadda yayiwa magen koh? A gidannan wani irin tambaya ce banyi miki ba akan aurensa amma kika nuna kefa kina so ashe ke kinsan kin d'akko ruwan dafa kanki ke gaki mey wayo har kinsan ki 'boyewa wa iyayenki abu mu da muka haifeki".

     " Ummi dan Allah kiyi ha'kuri duk abinda zey faru ya riga da ya faru yanzu gode Allah zami daya ta'kaita abin ya tsaya a haka".Aunty Mirah ta fad'a tana share hawaye.

    An d'auki kusan 3min d'akin shiru ba abinda ake ji se sheshshe'kar kukanta ,zafi  goma da ashirin wasu kukan data dad'e tana had'iyewa yau kuma sun kunce ga ciwon jiki harma da mararta dake zugi ga fad'an Ummi.

TAGAYYARA(Complete)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt