Chapter 49

649 48 7
                                    

     
        *_LABARIN AL-AMEEN(Kamal)_*

         
          Mun taso a gidan mu mu biyar, maza hud'u mace d'aya.Akwai Umar,ni (Hafiz),Kamal (Real Kamal), Al-ameen(Kamal namu but Fake) se Yusra auta.Tun tasowarmu da Al-ameen(Kamal) muka fara fuskantar wani abu gameda shi wanda ya banbantashi da sauran mutane.

      Shi ba'a ta'ba yin fad'a dashi ya ha'kura ba tare da ya d'au mataki ba komai girman wanda ko yai fad'a da shi d'in,ko malamansa na makaranta idan sukai masa fad'a ko gyara akan wani abu nashi seya rama ko ba'a lokacin ba.Ya kasance mey son kansa duk abinda ya gani na wani inde zuciyarsa tana so seya 'kwata ,gashi baida sabo shi duk dad'ewarka dashi watarana zey watsar da kai ,abu kad'an zey had'a shi da abokinsa toh daga ranar zey dena sonsa idan ba'ai wasa ba ya zama ma'kiyinsa ,ba a iya mutanen waje abun ya tsaya ba harta mu yayyinsa da muka d'aresa inde za'a ce mun masa gyara ko fad'a toh baze kyale mu ba seya rama ko a 'boye ne sede daga baya ka  ga yayi maka 'barna ta wani abu dayake mallakinka.

      Mahaifinmu ya kasance mey zafi ba ruwansa da kai yarone muddin kayi ba dede ba ko yaga kana wata d'abi'ar da batai masa ba toh bazaku shirya dashi ba yata tsangwamarka kenan harse ka daina.Toh haka ne ya faru akan Al-ameen (Kamal),se ya zamana a kodaushe mahaifinmu cikin tsangwamarsa yake tun tasowarsa da 'karancin shekaru da basu wuce 10 ba ,se ake ganin kamar mahaifinmu baya son yaronne harma wani lokacin suna samun sa'bani da mahaifiyarmu akan hakan.Shiyasa ita kuma take biyewa Al-ameen(Kamal) duk abinda yake so zatai masa tunda tana ganin kamar mahaifinmu baya qaunarsa harma shi Al-ameen d'in ya gane hakan ,ko abinci wasu lokutan babanmu baya bari yaci a table damu saboda cin abincin nasa seya zama da wani irin salo ,seya nutsu yaga kowa ya zuba a plate nashi yana ci seya za'bi na wanda yayi masa yace shi zey ci wani sa'ain harna 'kanwarsa Yusrah seya 'kwace.Gwara mu manya ne wataran muna ha'kura mu bashi koma bamu bashi ba Mahaifiyarmu tana samu shiko mahaifinmu yace sam baze yuwu ba inde baze dinga cin nashi ba toh sede ya ha'kura. Akwai wani lokacin da Mahaifinmu yayi masa fad'a bayan yaga fitarsa aiki ya shiga d'akinsa wasu takardu masu mahimmanci ya d'auko ya 'konasu aiko mahaifinmu be barsa ba seda ya zane sa ranar mahifiyarmu ranta ya 'baci kowa zuciyarsa ba dad'i.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now