Chapter 66

742 44 1
                                    


     Kowa yana jiran tsammani kud'in waya se kuka sike Wafah ma taji bini-bini se si kiran Mami suji  koh ta haihun  amma shiru ,Mommy ce kad'ai bata da labari sede tana ta tsammanin kiran Shettima kamar yadda ya saba yana kiranta kusan kullum su gaisa  amma yau taji shiru.Itanma tana kiran Amrah taji jikinta sede yau wayar bata shiga ,wayar Shetyyman ta gwada kira taji tana shiga ba'a d'agawa.Sam hankalinta ya kasa kwanciya  doctor ne ma yake d'an kwantar mata da hankali yace ta bari anjima ta sake kira.Haka de harta kwanta batai wayar dasu ba tunda su acan lokacin ba d'aya bane da nan.

    Amrah zuwa yanzu ta dena cewa uffan ita tama saddaqar tace mutuwa zatai ,har 'karfe hud'u na yamma duk cikinsu ba wanda yasa abu a bakinsa.Yanzu na'kudar ma ta tsaya ganin haka kawai akwai deciding ayi mata aiki a cire d'an.

      Yana tsaye a bakin gadon hannunta sar'ke a nasa take fad'in."Kayi ha'kuri Shettim amma nasan mutuwa zanyi".

    Kai kawai yake girgiza mata "Amrah bazaki mutu ba ki dena fad'ar haka kinji"

    "Ba'cin operation za'ai min ".

    " Toh waya ce idan anyi operation mutuwa ake?"

     Bata sake cewa komai ba idanunta yana tsiyayar hawaye tana sake karyar masa da zuciya.Har 'kofar d'akin operation d'in dashi aka tura gadon data ke kai d'in yana kallo aka shige da ita 'kafarsa da 'kyar  take d'aukansa.

     Mommy a chan da gari da asubahi ta sake dannowa Shettima kira still ba'a d'aga ba dan haka ta kira Mami itako tana ganin kiran ta'ki d'agawa dan bata san mey zata ce mata ba.

    Mommy bata ha'kura ba ta dannawa Walida kira,a d'ar-d'ar tayi picking baya sun gaisa ta tambayeta ko lafiya.

   Daga yadda Walida ta amsa tasan akwai abinda ake 'boyewa aiko ta matsata har seda ta fad'a mata komai a rud'e ta katse wayar ta sake kiransa shiru dan haka ta kira Ummi tasan ba lalle Mamin ta d'aga ba.

    Allah ya taimaka Ummi ta d'aga,ita da take nesa yasa hankalinta yaso fin nasu tashi."Tun farko da suka ga bata haihun ba ai da anyi aikin amma seda yarinya ta wahala".Cewar Mommy.

      "Allah yasa ayi a sa'a".Ta fad'a duk ta rikice.

    Ummi ta amsa da ameen,nan Mami ma ta kar'bi wayar suka d'anyi maganar da zasi tace a bawa Shettima wayar wanda dede lokacin yake 'karasowa wajensu.

   A  sanyaye  ya kar'bi wayar ya kara a kunne " Shettima".Ta kira sunansa.

  Gefe ya ke'be kansa a 'kasa ya dafe garu da hannu d'aya d'ayan kuma ma'kale a kunnensa da waya gabad'aya ya nemi jarumta da wata dauriya ya rasa hawayen dayake ma'kalewa suka tsiyayo,murya a raunane yace "Mommy ...."

     Shiru yayi ya kasa cigaba da magana Mommy daga d'ayan 'bangaren taji shiru gashi wayar ba katsewa tayi ba hakan ya tabbatar mata da kuka yake.

   "Shettima". Ta kuma kira.

   " Ba abinda zey faru inshaAllah za'ai a sa'a".

    "Allah idan ta mutu nima mutuwa zanyi".

     " Waya ce maka mutuwa zatai ka dena fad'in haka addu'a kawai zami mata inshaAllah komai zey zo da sau'ki".

   Kai kawai ya gid'a bece wani abu ba har ta katse wayar.

      A d'akin operation bayan an ciro babyn Allah ya taimaka yana raye baby boy ne 'kato mashaAllah ita bama tasan an ciro ba duk da idanunta biyu amma tana jinta kamar ba'a duniyar ba.Se da aka kammala shirya shi aka nuna mata shi da ido kawai take binsa ta rasa farinciki zatai ko sa'banin haka dan ita kam ta kanta take.

    Su Ummi suna zaune jugum-jugum nurse tazo musu da labari mey dad'i ta fad'a musu an ciro baby yana cikin 'koshin lafiya itama maman yaron haka  an kaisu d'akin kwanciya.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now