Chapter 57

677 51 4
                                    

     Wayar na ringing be d'aga ba kafin ta kuma dialing taji MC na magana ga angwaye zasu shigo da Amarensu.

    Nan fa kowa ya maida kallonsa 'kofar da ake tsammnin shigowarsu ,nan DJ ya sauya kid'i fa.

     Abin gwanin sha'awa Amare har uku ga angwayensu Uku su Shettima sune a gaba  kasancewarsa babban yaya.Hasken flash ne kawai yake tashi masu photography nayi masu phone nayi.

    Amarya Amrah tana sanye da Sea green Material d'inkin gown complete colour d'in har head da net daya lullu'be fuskar Amrah, kota cikin net d'in saka gano irin had'uwar kwalliyarta ga sar'karta silver mey stones colourless purse d'inta da takalminta mey tsini suma silver colour.
 
   Ango Shettima yana sanye cikin sky blue shadda dake she'ki hularsa dark blue kamar ka sacesu su biyu.Walida da 'yar biyunta  Wafah suna sanye da peach material angwayensu na sanye da milk shadda suma sun fito 'yan matan Amarya sunyi ankon blue da  pink.

     Bayan sun zauna kowa a mazauninsu  aka shiga zuba musu pic su kad'ai a zaunen.Mata ne d'aya da dangin Mommy d'aya daga dangin Ummi suka fito su biyu ,nan fa akai musu ruwan turare harda angwaye aka kama😹

     Nan fa dinner ta soma akafara gudanar da taro,my ppl  sunyi group Tagayyara fans kaf d'insu suna wajen komai yake gudana.Kowacce ta kasa rife baki saboda murmushi yau gasu ga stars d'in Tagayyara wheuooh!

      Anci ansha an hantse se godiya ,angwaye sun yanka cake sun bawa amarensu suma amare sun ciyar da angwayensu wai da Shettima yazo bawa Amrah ta'ki bud'e baki garin haka ta sake janyo hankalin jama'ar wajen kuwa.A kunyace ta bud'e d'an bakinta dayasha rose red lipstick aka sa tafi.

***

    Maman Kamal(Al-ameen) 9:12pm ta soma shirin fitan bayan ta kammala ta le'ka d'akinsa taga ya juya baya alamar bacci yake amma dukda haka seda ta 'karasa ta duba kan table taga yasha maganinsa taga yasha d'in sannan ta d'auki key d'in motar Hafiz daya barta a gidan su dinga amfani da ita tunda shi yana Cyprus.

     Tana rufo 'kofar d'akin ya bud'e idanunsa dama ba baccin yake ba ,dan besha maganin ba koda ta kawo ta ajje masa yarwa yayi ,tunani ya shiga yi ko ina zataje??

   Mi'kewa yayi daga kwancen ya fita zuwa kitchen, fridge ya bud'e ya Ciro bottle d'in ruwa yasha harya 'karar dashi ya bud'e dustbin zey  idonsa saya sauka kan iv card da Mama tasa a shara tana sauri ko yagawa batai ba duk de dan karya ya gani d'in.

  Yanayin yadda yaga IV d'in tsaf complete ansa a shara yaja hankalinsa ya kai hannunsa ya d'auka yana dubawa.

    Dayake anyi enveloping seda ya zaro shi,kam bala'i sunan Amrahnsa yake gani.

     Tashin hankali shida yake so ya komawa Amrahnsa su dawo normal ta dawo gidansa shine yake ganin katin dinner d'in bikinta,dole yaje wajen dole a yau ya ganta ya bata ha'kuri su koma gidansu.

 

    ~~Gabaki d'aya tawagar gidan Mommy sukai pic sannan tare dasu Ummin da Mommy aka kyasta musu ,Mommy Ummi Amrah Shettima.Su Mami da Hajiya tsohuwa an barsu a baya suna gidan Mommy wai su ina bazasu zo wata dinner ba harkar yaran zamani😂

    Dr fa a wajen taron ya fara isar Mommy da kira wai yana so yaji yaya Allah yasa de ba wani d'an bazawari a gun fa😂

     Su Sa'adatu an danse dasu da sauran 'Yan matan Amarya amma de amare sun'ki rawa Walida de taso yi ganin Wafah ta'ki takawa yasa ta ha'kura de balle kuma akai ga Amrah kamar an dasata a wajen har MC ya gama hayagagarsa ba wacce tayi rawa.
    
    Alhamdulillah anyi dinner an tashi kowa hankali yayi gida dare yayi ,Mommy ta tattara kan yaranta driver ya wuce dasu kafin ta taho.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now