Chapter 17

603 54 0
                                    

   Washegari

  
      Gidan yau kam yafi cika da 'yan gaisuwa a shiga a fita haka ake tayi.Rahinatu dataga parlourn ba'kin ya cika seta tafi d'akin Aunty dan nasu d'akin ma taga da akwai mutane.

     D'akinta taje ta d'akko kayan sawa ta komo na Aunty ,take ta soma shirin shiga wanka.Ta murd'a handle ta bud'e 'kofar .....

            "Ke! ..ke! k..e!" Taji an fuzgota baya.

    Tana tangal -tangal ta d'ago a razane "Aunty mey ne?"

   "Bakida hankali zaki shiga toilet d'ina"

      "Yanzu akan ban d'akin kika sa hantar cikina kad'awa"

    "Toh meye na shiga min toilet? Ga naku can"Yanzu a hankali Aunty tayi maganar.

    "Mutanene fa a d'akin ni banason takura"

     Matsawa tayi ta rufo band'akinta harda sa key."Nide bazaki shiga min ba ,kije nasu Walida ko Mommy".

    Kallo d'aya Rahinatu tayiwa babar tata ta cuno baki ta fita daga d'akin kayanta ri'ke a hannunta.

     "Phew! Zata jamin jafa 'i"Ta share goshi.

      _____________________

 
       Shettima da yake premises na gidan ya hangi shigowar Ummi amma fa bega Amrah ba,time-time yana hangen hanya ko zata shigo amma still batai show up ba.

   Amrah kam Ummi ta barota tana   'yan gyare-gyare na gida kafin anjima seta taho.

       qlin!

     My love hasken idaniyata barka da hutawa.Barr love you.

       Mtchwww! Tayi deleting nan take.

      Se wajen 11:13am ta kammala komai sannan ta shirya zata fita,tana yin sallama da Abba ta fita.

    Tayi nisa da tafiya kafin ta tsari napep kamar daga sama taga mutum yasha gabanta.Ganin fuskar data sani tayi saurin kauda kai gabanta na fad'uwa.

    "My Amrah ya kamata ki saurareni ko na minti 3 ne dan Allah walhy Amrah bana iya bacci sabida tunaninki a zuciyata" Duk wannan maganar da numfashi d'aya yayi ta.

   Yadda yake tsaye kusada ita yasa ta ja baya tana ji kamar zey ru'ko hannunta yana pleading like almost begging.

    Sam ta'ki bari su had'a ido addu'a kawai take napep yazo ta bar wajennan saboda ba jama'a a wajen sosai.

     "Amrah ina bala'in sonki"

      "Bala'i" Ta furta a zuciyarta.

      "Mey sonka baka 'kinsa Amrah,da gaske nake aurenki zanyi bada yaudara nazo ba,Amrah idan kika aureni zaki ji dad'in rayuwarki..."

   Ganin baze dena wannan surutan ba yasa ta bud'e baki ta soma magana."Bawan Allah dan Allah kayi ha'kuri,amma ni inada wanda zan aura please kayi ha'kuri"
  
      Wani murmushi taga ya saki cikeda rashin nuna damuwa."Amrah in banda abinki aure ai nufi ne na Allah ,rayuwarnan fa competition ce kika sani ko ba alkairi bane wanda kike so d'in"

    A yanzu ya kaita bango kamar zata bud'e baki tayi magana kuma tayi shiru ,cikin sauri ta bar wajen ta soma tafiya tana Addu'a d'an sahu yazo.

     Ba zato ba tsammani taji an ru'ko mata hannu ,a fusace ta waigo instead ya  saketa a'a sema magana daya fara.

   "My Amrah n..." Be 'kare ba ya dakata da maganarsa dan marin daya sauka a fuskarsa.

     Ita kanta bata zaci zata iya marinsa ba ,a tsorace ta kalli hannunta ta kalli Barr Kamal da hannunsa ke dafe a kumatunsa.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now