Chapter 69

676 46 1
                                    


    Ganin haka ya tashi ya fita abinsa sede sam bajin dad'in wannan dramar tasu yake ba dan ya gaji jira yake ta bashi ha'kuri face to face se a shirya amma ta'ki shikuma baze zamo first da ze bada ha'kurin ba yana ganin ita ta fara laifin kuma jiya ta sake yin wani ta bar masa yaro da yunwa.

    Itama ranta a 'kufule  takaicin rashin damuwa da maganar asibitin be tambayeta ko lafiya ba? Haka jiyan ma be sani ba ko bata da lafiya ne ta'ki bud'e 'kofar ba amma ko ajikinsa.

     Seda ya 'karasa mota ya tuna yayi mantuwar wayarsa da sauri ya koma ciki a parlour ya tarar da Aasim ya soma kukannan nashi ransa a 'bace ya duba kitchen yaga bata nan yaron yana hannunsa ya hau sama a d'akin ya hangota a bayi tana ta amai kamar zata amayar da hanjin cikinta.

    A rikice ya 'karasa wajenta "Amrah". Ya kira sunanta.

   Dire Aasim yayi daga bakin 'kofar ya 'karasa inda take ya shiga shafa bayanta tana dur'kushen" Sannu ...dama baki da lafiya".

    Kai kawai ta gid'a kwalla na tarar mata tana fatan Allah yasa de ba abinda take tunani bane.Shiya gyara wajen  tana zaune bakin gado Aasim se 'ko'karin hawa cinyarta yake shi besan ba fine ba.

     "Tashi mu tafi asibiti".

      Bata musa ba ta mi'ke shine ya sauyawa Aasim kaya suka fita gabanta se fad'uwa yake ,ana zuwa asibiti akai mata gwaji.Abinda take gudu shid'inne d'an tayin sati uku,ta fito ri'ke da takardar batasan sanda hawaye ya tsiyayo mata ba ko bi ta kansa batai ba ta wuce mota yana tambayarta tayi masa shiru se takardar ya kar'ba daga hannunta.

   "Alhamdullah".

    " You now deserved sorry baby".Ya waiwayo yana kallonta itako window take kalla.

     "Sorry baby please d'an kalleni".Ya fad'a tana murmushi.

   " Bara naji unborn ".Ya fad'a yana kai hannunsa kan cikinta fuskarsa d'auke da murmushin zolaya.

   Sauri tayi ta ri'ke hannun tana ture shi ta cuno baki.

   " Wow yau za'ai celebrating ke daman kinsan kina 'kunshe da d'an abinki shine kikewa mutane nu'kufarci".

    Aasim yana kan cinyarta ta wani kalleshi."Yaye ba fashi".

    "Ba wannan maganar ki ma dena fad'arta ke bakya maraba da kyautar Allah ne gwara tun wuri ki tuba wlhy".

    Hakan yasa jikinta ya d'anyi sanyi taga be kamata tayi fishi ba sede ita tsoron haihuwar take ga kuma Aasim da ko yaye shi batai ba.

    " Karki yi tunanin wani Aasim Allah zey kawo sau'ki".

     "Yanzu ina kike so muje?"

      "Aikin fah?"Ta kalleshi.

       " Off".

          "Gida zaka kaini".

      " Gida kuma Amrah?"

       "Eh".

      " Ni kuma fah?"

        "Kaje aikinka".

        "Haba Amrah ke baki missing d'in ba ni a iya jiya da yau wlhy na shiga damuwa bake a kusa dani kin barni da yaro".

    " Ba kaine ba".

      "Kece ai nace don't kika 'ki ji".

      " Sorry".Ta fad'a.

     "Kawai?"

      "Kaima ai sorry kace".

       Hannunta ya ri'ko yayi planting kiss a baya " Forgive me".

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now