Chapter 46

557 56 2
                                    


        _*Romeo Kamal's POV again*_💘

        Cikin sauri Hafiz ya 'karasa inda Kamal yake ,kamar jira yake dama yana ganin ya d'ora hannayensa a kafad'arsa ya bigesu yana mi'kewa tsaye.

   "Kaima kazo kasheta!?"

    "Al-ameen nine Hafiz baka ganeni ba?" Yana nuna kansa yana 'ko'karin fahimtar dashi.

    "Get out! Ka fita ...zan kasheka get out!" Kamal ya soma tunkud'a Hafiz.

    "Yaya ka fito baka jin meyake cewa!" Aunty Mirah tayi maganar kamar zata zuba ihu.

    Amrah da se yanzu ta gane cewa wasu sun shigo gidan dan a tuninta da ko Kamal d'in ne yake surutai yana chanja sunaye."Ku taimakeni!"Ta soma bubbuga 'kofar.

    Kowa kallonsa ya mayar kan 'kofar Hafiz shi tunani yayi ko Al-ameen(Kamal) ne ya shigo gidan .

    Wayyo dad'i a gun Kamal his love bata mutu ba kamar yadda yayi zato mantawa yayi ma da Hafiz dake gabansa tuni ya juya zuwa 'kofar cikeda zumud'i."Amrah love you're back ,zaki rayu dani"Ya shiga bubbuga 'kofar.

    "Yaya tana fa ciki Amrahn"

     "Al-ame..."

     "Shhhh!" Ya d'ora yatsa a bakinsa alamar siyi shiru.

     Wajensa ya 'karasa Hafiz d'in ya ri'ko kafad'arsa yana so ya matsar dashi daga jikin 'kofar ,a fusace ya juyo zey makeshi yayi saurin tureshi chan gefe soyake ya dur'kusar dashi amma abu ya gagara kici-kici suka shiga yi Hafiz ba yau ya saba irin hakan dashi ba sede na yanzun daban ne 'karfinsa bana wasa bane.

    "Mirah ki ...bud'e mata ku fita yanzu!" Ya tsawata mata dan yasan in ba hakan yayi ba seta kwana a bakin 'kofa Aunty Mirah kwai tsoro.

   Ko glass da suke pieces a wajen tsoron takawa take dukda akwai takalmi 'kafarta kamar kaza ta taka kashi ya ma'kale a 'kafar😂 haka ta 'karasa jikin 'kofar gashi Kamal d'in ma kad'ai ganinsa abun tsoro ne ta raba hankalinta biyu batasan waye wannan ba mijinta yake kira da Al-ameen harma gashi yana nuna kualwa a kansa mutumin da yake 'ko'karin kisan kai.

    "Amrah!"Ta kirata.

     " Ki bud'e min ku taimakenk!"Cewar Amrah ta manta ma ita ya kamata ta bud'e  kofar.

    Shiko Hafiz yana dur'kushe a yanzun shida Kamal yanayin yanda ya danne Kamal kamar police ya kama criminal dande ba yadda zeyi ne shiyasa ya 'bullo masa ta hakan yasan idan ba hakan yayi ba to kuwa komai zey iya faruwa,Kamal se mutsu-mutsu yake kansa na 'kadan tile d'in sunan Amrahn sa ya'ki barin bakinsa kamar karatu.

     "Amrah ya'ki bud'uwa ta nan ko ki gwada murd'awa ta nan d'in" Aunty Mirah ta fad'a jiki na rawa.

   Jin haka ta tuna ita ta rufe ,tana kyarma ta murd'a key d'in ta bud'e, ganin Aunty Mirah tsaye jikin 'kofar yasa ta fashe da wani matsanancin kuka.
    
     A gaggauce ta ja hannunta suka nufi wajen 'kofar fita kallo d'aya ta yiwa inda Kamal suke a dur'kushen ta kauda kai tabi bayan Aunty Mirah suka fice daga d'akin.Basu tsaya ba seda suka fito waje bakin motarsu,Aunty Mirah ta ri'ko kafad'unta biyu.

   "Amrah" Ta kira sunanta.

    Sam hankalinta da mutsuwarta basa wajen numafashinta da'kyar yake fita zuciyarta kamar zata fito ta d'ago ido ta kalli Aunty Mirah.

    "Amrah ya akai ya shigo gidan ki?"Ta tambayeta tana kallonta Amrah ko mayafi babu akanta balle hijab se d'an 'kwalin abaya da yake siriri a kanta Allah yasa doguwar rigar baccin dake jikunta mey dogon hannu ce.

    "Mije cikin mota" Ta fad'a har lokacin bata saki hannuta ba,kamar ra'kuma tabi bayanta suka shiga baya dama motar a bud'e take.

     Amrah yanzu idanunta na kam hannunta data d'ora a cinya  har yanzu ta'ki cewa 'kala.Zugin 'kafarta na ratsa ta da broken glass suka shiga bata sani ba ma se yanzu take feeling d'in zafin.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now