Chapter 54

657 50 6
                                    


         'Karfe 10:00pm kusan shine lokacin baccinta ko yaushe amma yau 'kiri-'kiri har 12pm ta kasa bacci se juyi take kan gadon kalaman Shettima na mata yawo aka ,sam bataiwa kanta tunanin auren saurayi   a rayuwarta a yanzu da take bazawara ,tana ganin sede auren mey mata idan ba haka ba toh babban mutum amma de ba saurayi kamar Shettima ba ,tana ganin an an kamar ta so kanta.

    _Flashback_

     
      Yana daga bakin 'kofar gidan ganinta da yayi tana fitowa ya 'karaso inda take a soron be bari ta fito ba dan bayason ake kalleta a waje shikad'ai yasan yadda yake jinta a cikin zuciyarsa.

     Kallonta yayi idanunta a 'kasa  se wasa take da yatsunta.An d'au 'yan seconds kafin ya soma magana.

     "Amrah .....I still love you".

     " Har e zuwa yanzu kina cikin zuciyata kuma....bazan iya cireki ba"

    Itade tayi shiru tana sauraran kalamansa.

      "Amrah, zaki aureni?"

       Tunda ya fara maganar bata d'ago da idanunta ba se yanzu 'kwalla ta cika su 'kiris take jira su zubo.

    "Amrah please ki amsa min".

       Da'kyar ta iya bud'e nannuayan bakinta tace" Bazan iya aurenka ba Shettima"

     Dama yayi tsamnanin wannan amsar kuma bega laifinta ba yana ganin shid'in  ya zama lanjare ba kowa ce zata iya aurar mey ciwon zuciya ba.

        "Auren bazawara  be kamaceka ba ni yanzu....."

      "Kawai? Wannan itace hujjar dayasa bazaki amince da aurena ba?"

     "Banga abinda zey sa na gujeki ba Amrah,koda ace zaki 'ya'ya d'ai-d'ai har d'ari inde ina raye kina raye ba abinda zey sa na'ki ki"

     "Kai zaka ga haka amma a wajen mutane fah"

      "Mutane su zasu zauna dake?"

      "Amrah kiyi tunani ,this is our second chance...."

    Bata jira ya sake wata maganar ba ta juya ta shige gida saboda kuka daya ke neman ku'buce mata,har ga Allah tana jin qaunarsa a ranta musamman yanzu data gansa komai ya dawo mata sabo.

     Presently

        Ganin tunanin bame 'kare bane ta tashi daga kwance,bayi ta nufa ta d'auro alwala ta soma gabatar da nafilfili tana mey ro'kon za'bi mafi alkairi.

        Shima de a gurin shi hakanne ya kasa bacci ,shima nafilfilin ya gabatar yana ro'kon Allah ubangiji ya za'ba musu alkairi.

      ★★★

     Washegari da safe 7:43am lokacin ya kammala shirinsa na fita aiki ,yau cikin T-shirt longsleeves dark blue yake sanye da ba'kin trouser yayi tucked in turare kawai ya feshe jikinsa dashi ya sakko 'kasa dan briefcase d'insa jiya a mota ya barta ko shigowa da ita beyi ba wayarsa kad'ai ya d'auka.

      D'akin Mommy ya nufa dan gaidata yaga ko ta tashi yawanci idan bata farka ba se a officer yake kiranta dan bayaso ya tadata.Koda yayi knocked bata d'akin a 'kasa ya jiyo hayaniyarsu duka da alama suna kitchen ma ba shakka yaran Dr jiya anan d'in suka kwana dan se idan sun zo ake jin irin wannan hayaniyar.

       Yanzu da babansu ya koma America basuda wajen zuwa se gidan Mommy da yazama tamkar gidansu ,hajiya tsohuwa kakarsu itama ta huta da hayaniyarsu suma sun huta da fad'anta.

     Wani sa'in idan yana so ya kira yaji lafiyar yaran Mommy yake kira dan yasan ba'a rabasu da gidan ko be barsu sunje ba toh kuwa Hajiya tsohuwa da kanta take kiran driver ta sasu su tafi saboda ta huta ,Mommy ma tana maraba da hakan sam bata gajiya dasu ga sha'kuwa mey 'karfi tsakaninta da yaran kamar itace mahaifiyarsu musamman Imran da Nana da sune basu san mahaifiyarsu ba sosai ba kamar Sameera ba  wacce da d'an wayonta Amminsu ta rasu amma itanma rayuwar gidan Mommy tafiye mata dad'i saboda akwai Sa'adatu da kusan itace sa'arta gasu Wafah suma kamar yayyinta haka ta d'aukesu.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now