Chapter 34

549 43 0
                                    


     Lokaci-lokaci tana duban agogo gashi har magbrib tana tunkarowa amma ba alamar Shettima ,data kirashi wayar na ringing amma ba'a d'aga ba daga baya ma taji switched off .Gajiyatai da jiran bayan sallahr maghrib da kanta ta fita ta tsari napep ta koma gida.

    Koda ta koma gidan ta tarar baya gida,sau d'aya ta sake trying number sa a kashe ta ha'kura.A rayuwa batason sa'ba al'kawari dayasan baze samu damar komowa ya d'auketa  ba ai da seya gayamata ko ya kira ya sanar mata amma ba hakan ba se kashe wayar sa da yayi bacin da a kunne take daga baya aka kashe.

   ***
   
       A hankali ya soma bud'e idanunsa har ya ware su tarau kansa dake kife a steering ya  d'ago yana so ya tuna abinda ya faru.Ga mamakinsa yaga gari yayi duhu alamar darene agogon hannunsa ya duba ya nuna 10:12pm sosai yake mamamakin wannan lamarin ,yarinyar daya d'auka a motarce d'azu ta fad'o masa rai ya kalli gefen kujerar passenger babu alamar ta sede har lokacin 'kamshin turaren be baje daga motar ba kallonsa ya mayar inda tayi 'barin jakarta yaga babu komai a wajen kamar ba'ai ba kansa ne ya kulle wata zuciyar tana ce masa ko aljana ce? Amma kuma ga 'kamshin turaren be baje ba ai.Tun yamma be farka ba se irin wannan lokacin? Tuna handkerchief datai amfani dashi wajen goge turaren yayi, irin yadda ta hargitsa wajen shide daganan yasan be sake sanin inda kansa yake ba,toh hakan yana nufin ita tasa shi haka? Amma meye manufar hakan tunda de gashi cikin motarsa daya duba wayarsa ma yaga tananan sede a kashe take sa'banin d'azu.

     "Ya salam!" Ya furta lokacin da ya tuna da al'kawarin dayai wa Mommy zey koma ya d'auketa.Yasan tayi ta kira bata sameshi ba a waya.

    Ganin lokaci na sake ja jikinsa ba wani 'karfi ya kunna motar ya bar wajen qwaqwalwarsa a sar'ka'ke ya kasa tantance exactly abinda ya faru.

     Yana shiga gida d'akin Mommy ya fara wucewa yayi knocking yaji shiru ,a hankali ya murd'a handle ya shiga d'akin dund'um ba haske hakan yana nufin ayi bacci kenan.Juyawa yayi yaja 'kofar a hankali karya tasheta,itako tana jin sanda ya shigo harya fitan.

    A d'aki da'kyar ya iya gashi ya shiga bathroom yayi wanka ya saka kayan bacci tunani ya cika kansa  ya rasa inda zey samu amsar tambayoyinsa  ,sam ya kasa bacci daga baya ya d'auro alwala ya soma gabatar da nafilfili.

      _____________________

    Barrister Kamal sosai yake nunawa Amrah kulawa yana  bata mamaki dukda bata gama yarda da gasken yake ba dan gani take halinsa yana nan kawai wani takun ya sauya wanda shiyasan ma'anarsa.Duk yadda yake 'ko'karin faranta mata sam baya birgeta balle ta nuna masa a fuska itade abu d'aya ta sani ko mey za'ai bazata ta'ba amsar soyayya daga gareshi ba koda kuwa zey mutu, d'igo d'aya bata ta'ba jin son sa ba dede da second d'aya.Bini-bini idan ya fita da wuya be siyo mata wani abun ba ,har yanzu ta'ki bari wani abu ya sake shiga tsakaninsu tana gani ya soma kauce hanya take saka kuka shikam inde ba'a son ranta bane yayi al'kawarin baze mata tilas ba.

    Tana gaban mirror ta gama shirinta cikin doguwar riga ta bacci me dogon hannu pink colour ta d'aura hula a kanta lotion take shafawa a jikinta kafin ta kaiga kwanciya.Tana kallon shigowarsa d'akin ta cikin mirror, tattaki yayi har zuwa inda take ta cikin mirror d'in shima yake kallonta.

     "My starlight kinyi kyau".

      Bata d'ago da idonta ba dama ta saba jin haka idan taga dama tace thanks wataran tayi shiru ,yanzu de tace "Thanks".

       Zagayowa yayi gabanta,ba zato ba tsammani se gani tayi ya tsuguna gwiwoyinsa a 'kasa hannunsa d'aya yasa cikin aljihunsa na jeans ya ciro  wata 'kan 'kanuwar box blue hannu biyu yasa ya bud'e zobe ya bayyana ,silver mey green stone ba 'karamin kyau yake dashi ba kallo d'aya tayiwa zoben tai 'kasa da idonta.

    Hannunta ya ri'ko na dama a d'an yatsanta na hud'u ya zira mata gwanin sha'awa ya fito da hannun farar fatarta ta haska gashi cif  a yatsan.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now