Chapter 41

589 37 0
                                    

    *👆Audio of Tagayyara is added*

     *Wannan shafin sadaukarwane gareku BBC HAUSA NOVELS GROUP, DEEJA ONE LOVE da dukkan Members na TAGAYYARA FANS GROUP Aunty Hajara iliayasu,Firdausi kilgory ,Khadija Abubakar ,maman khad,nafeesa,mama yasmeen, naga amsoshinku kun sani nishad'i dayawa-dayawa ina godiya wanda bega sunansa ba ayi afuwa sunayan dayawa.*

*Deeja one love ban manta dake ba nayi farinciki ASHE KECE is back Allah yasa mu kammala lafiya baki d'aya(Ameen).*

    __________________________

       Ta d'auki mintina  dur'kushen kafin ta iya d'agowa taga Mommy juyawa tayi ashe ,ajiyar zuciya ta saki har yanzu bata gama dawowa normal ba, sand'a ta dinga yi tana waige-waige ta fice daga d'akin key d'in na hannunta direct d'akin Appa ta wuce,cikin zumud'i hannunta na rawa ta kasa iya zira key d'in a 'kofar se da 'kyar ta zira murd'awa ta shiga yi amma ya'ki gaba ya'ki baya,dukan mukullan seda ta karad'esu d'aya bayan d'aya amma ba wanda yayi hakan ya tabbatar mata da cewa ba mukullin d'akin ta d'auko ba.Ba'kin ciki da takaici ya mamayeta ta rasa da me zata ji da rashin nasarar samun takardun gidajensa ko kuwa na key d'in d'akin ga waccen shashashar 'yar tata.

     Ji take kamar taje ta sha'ki wuyan Mommy tace ta bata key d'in,ba yadda ta iya dolenta ta koma d'akin ta wurga key d'in 'kar'kashin gadonta ta kwanta gashi bacci ya 'kauracewa idanunta banda tunani ba abinda take.

    ***

     Kamal a 'bangarensa Abu sey ci gaba yake bacci ma ya gagaresa jiyake kamar ana daka a qwaqwalwarsa kuma yasha magani ya'ki sha dan yayiwa kansa al'kawari baze sake sha ba ai qalau yake kamar kowa.Daya gaji da zaman shirun a d'akinsa ya koma d'akin Amrah ,tana bacci ya isketa ,side datake ya zagaye ya zauna 'kasa hannayensa biyu kan gadon ya d'ora ha'barsa kan bayan hannaye biyun daya d'ora d'aya kan d'aya.Kamar be ta'ba ganinta ba ya 'kura mata ido yana zuba murmushi a takaice de daren gabad'aya gadinta yayi idonsa biyu asubah tayi.

    Bud'e idanunta ta saukesu a kansa sosai ta tsorata har seda ta ja da baya a zuciyarta tace "Sekace aljani".

    " Kin tashi wife? "Yadda yayi maganar ma kad'ai ab in tsoro gabad'aya komai nashi ya chanja yanzu yana yin abu kamar wani d'an 13yrs.

    Ta d'ayan side d'in ta sauka daga gadon batace masa komai ba ta shige bathroom,shima se lokacin ya fita daga d'akin ya koma nashi d'akin.Bayan yayi sallah ya tafi kitchen kuma nan fa ya shiga rangad'a musu breakfast ,yana firaye dankali yana murmushi tunanin Amrah yana masa yawo aka.Wasa-wasa haka ya dinga fere dankalinnan jibgi guda kamar 'yan Deeja one love group members ne zasu ci😱 haka ya soyeshi duk uban yawansa.'Kwai ma ba'a magana haka ya fashe yadda kansa ya lissafa masa (nide tun ina irga harna dena ,wanda na irga yayi 11).Besa wani d'and'ano ba se gishiri kawai daya zuba ba awo ba komai (Firdausi kilgory ke zaki d'and'an wannan).

    Breakfast is done wajen 9am ya jere  komai  a tray ya nufi d'akin ta .Tana zaune stool d'in  mirror ta gama shirinta cikin atamfa brown colour mey ratsin milk ko d'aura d'ankwalin batayi ba kawai tade d'ora a kanta gabad'aya bata jin dad'in jikinta tun jiya data kwanta.

     Ta cikin mirror ta gano sigowarsa ,takowa yayi indaa take a kan drawer ya dire tray d'in.

    "Ina kwana My Amrah".

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now