Chapter 3

1.1K 87 0
                                    

     Amrah a tsorace ta fara magana"Ummie..."Katseta Ummie tayi da fad'in"Karki ce komai banason ji".

    "Ummie dan Allah kiyi ha'kuri,wlhy tun d'azu mun rasa abin hawa shiyasa muka taho a 'kafa". Shettima ya d'iga aya.

   " Sannu da 'ko'kari kai mey rashin lafiya har kana da bakin magana ko Shettima? Kana biye wa wannan sakaryar".

    "Nina saki kiyi gudun islamiyya?" Ummie ta jiyo kan Amrah.

   "A'a" Ta girgiza kai.

    "Toh meyasa kikai?"

     "Ganinai kwana ..biyu banje ba shine..shine naje gaida Mami" Tayi maganar cikin 'in-ina kanta a sunkuye.

    "Yayi kyau".

     " Ummie kiyi ha'kuri bazata sake ba ,banda lafiya shine fa taje..dubani"Ya 'kare 'karshen sentence d'in a hankali.

    "Ohto kana so kace ta fimu damuwa dakai kenan wannan sakaryar koh??"

    "Ummie..." Kayimin shiru! kana fama da kanka ka biye mata yanzu dubi yadda ruwa ya zane ku, ita wannan ba lalle ta kwanta rashin lafiya ba amma kaifa?"

     Haka Amrah ta tsaya daga bakin 'kofa fafur ta'ki shigowa shima yana daga bakin 'kofar se sunne kai suke dukansu.Ana haka suka jiyo sallamar Abbanta  ,Amrah ganin Abbanta ya shigo gidan taji sanyi a ranta tasan baze bari Ummie ta daketa ba.

    Koda Abba ya tambayesu bacin ganinsu dayai a ji'ke Ummie ta labarta masa komai.Ummie maimaikon taga yayiwa Amrah fad'a setaga ba hakan ba,dede wannan lokacin Sega driver na Mommy,nan Shettima yayi musu sallama driver ya jashi suka tafi gida ita ko ta wuce d'aki ta sauya kaya.

      A gidan Mommy kuwa duk suna parlour dasu Mami da Aunty Mira banda Aunty Hannatu da tuntuni tayi shigewarta d'aki.Tun daga bakin 'kofa Shettima ya soma jero attishawa cirkoko ya tsaya yana kallon Mommy dasu Mami cikin mamaki dan beyi zaton ganinsu a parlour ba a ransa yana fad'in "Bade danni suke a parlour haka ba?"

    Be gama 'karasawa  inda suke ba Mommy ta taso "Shettima mey zangani ruwan sama ne yaji'kaka haka ?" Ta shasshafa rigarsa tana jin danshin ruwa.

    Fuskarta ta nuna damuwa 'karara jitake kamar ta cire masa jin sanyin ta d'orawa kanta.

    Shi kunya ma ta bashi yadda take nuna matu'kar damuwa akansa kamar shine d'an da ta mallaka a duniya kad'ai."Mommy bafa wani sanyi sosai yanzu zan cire kayan ai"

    "Mije maza ka sauya yanzu zan had'a maka tea jeka" Tayi sauri ta wuce kitchen yabita da kallo.

     "Kagani ko jibi yadda ka d'agawa Mommy hankali" Anty mirah taja kunnensa cikeda wasa.

    "Atoh de ni bazance komai ba tunda tun farko seda nayi muku kashedi" Cewar Mami.

    "Kai Mami bakiga yanda Amrah itama ta ji'ke ba".

    " Banason sauran bayani jeka cire wannan"Tayi nuni da rigarsa.

    D'akinsa ya wuce Rahinatu 'yar Aunty ta bishi da kallo tana ta'be baki hud'ubar babarta tana mata yawo akai dan ba ruwanta dasu yarane haka zata zauna tayi ta fad'a mata su Appansu baya sonsu yafi son Shettima.

            ★★★

    Mommy bayan an d'an kwana biyu kad'an tayiwa Appa maganar fita da Shettima waje bayan ya kammala secondary school d'insa.Da farko ya nuna bayaso amma kuma ganin ta takura ya rabi da ita ya yarda dukda ba wani so yake ba musamman daya san Aunty Hannatu ce ta tsara hakan.

   Shikuwa Shettima sam baida masaniya akai,be 'kara three weeks a gida ba lokacin komawa school yayi haka kamar koyaushe yaje gidansu Amrah yayi musu sallama jiki ba 'kwari Appa ya maidashi ,wannan kusan koyaushe ne inde zey koma makaranta kamar ranarsa ta farko haka yakeji.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now