Chapter 61

808 56 2
                                    

   
     8pm Mommy ta kira Shettima kan maganar Aunty Hannatu  dan da tayi tunanin zey je gidan amma taji shiru sau biyu ya le'ka gida tun bayan biki.

     Dede lokacin kwa suna zaune parlour kallo ta d'ora kanta a 'kirjinsa suna enjoying kallonsu.

    Tana sanye da riga da skirt na english wears white shirt mey dogon hannu da skirt sea green ta d'aure kanta da farar hula.Wannan kaya za'bin Shettima ne dan ita  a yanzu tafi son taita saka atamfofinta da lace idan an kwan biyu ta fara saka English wears d'in  amma shi kam wai yana son ganinta cikinsu da kansa ya za'ba mata.

      Yana sanye da ba'kin three quarter da farar shirt mey gajeren hannu.

    "Ana kira a waya" Ta fad'a dan wayar tana kan center table.

    "Ina ji basshi kawai".

     " Kasani ko kiran mey mahimmanci ne".

    " Nifa banson damu wlhy,mi'kon naga".

   Hannu ta mi'ka ta d'akko wayar ta bashi .
 
   " Mommy ce".Ya fad'a sanda ya kalli screen d'in.

    "Kagani ba". Ta fad'a kafin tace " Ina zuwa".Ta tashi ta shiga kitchen ,tayi hakane dan ta bashi guri.

   Fruit salad ta shiga had'a musu da wannan damar daman tun d'azu ya ma'kal'kaleta neh ya sa bata had'ad'in ba.

    Bayan sun gaisa ta soma kwararo masa bayani ta 'kare da fad'in yaje asibitin ya dubata.

   Shiko tunda ta fara maganar ya tamke fuska kamar be ta'ba murmushi ba shi be zaci wannan maganar ba da ace yasan ita zatai masa da ba abinda zey sa yayi picking kwata-kwata ya goge su daga shafin rayuwarsa daga Hannatun har 'yarta Rahinatun.

    "Baka ce komai ba". Cewar Mommy daga d'ayan " bangaren jin yayi shiru.

   "Mommy,idan naje mey zanyi mata akwai wata ala'ka ne tsakanina da ita ? Suyi rayuwarsu nayi tawa dama qaddara ta had'a aka sansu toh yanzu ta raba wanda suke zaune dan shid'in ta kasheshi ta huta toh kuma mey zan mata?".

    " Banason jin irin haka Shettima ,kai bakasan abu ya wuce ya wuce ba kenan ita kanta tayi nadama koh ban gayamaka halin data ke ciki ba a yanzu?"

   "Mommy kin fad'a min amma zuwana fa bashi zey cire mata ciwo ba".

    " Kai baka yafiya ne?"

     "Kaje na fad'a maka ka dubata bana son dogon zance".

     "Toh".Ya fad'a a ciki-ciki.

       Ding! ta kashe wayar ta barshi da takaici yana zamansa za'a haifa masa 'bacin rai da be shirya masa ba.

  Koda Amrah ta dawo seta lura da sauyin yanayinsa ba'a yadda ta barsa bane bade ta tambayesa ba ajje bowl d'in fruit d'in kawai tayi ta zauna.

      Bowl na fruit d'in ta jawo  tayi alamar susha,d'an harararta yayi hakan yasa ta gane mey yake nufi.Spoon d'in ta d'auka ta fara bashi a baki  ,zuwa yanzun de ya d'an saki fuskar amma maganar na ransa.

     ★★★

     Yau Shettima zey koma kan aikinsa sati biyu cif da aurensu shi duk seyaji hutun yayi masa kad'an kamar wanda zeyi tafiya haka yake ji ,ita kanta Amrah tun wayewar gari ta soma jin ba dad'i batasan ya zata jure zaman kad'aitannan ba.

     Fitowarsa kenan daga bayi towel ne d'aure a jikinsa ya 'karaso bakin gadon idanunsa akan kayansa da Amrah ta za'ba masa bayan shigarsa bayin,ganin bata d'akin yayi murmushi watoh gudu tayi kar yace ita zata shirya shi.

    Gudun 'bata lokaci ya hanzarta ya shirya cikin kayan data za'ba masan.Black suit shirt d'in ciki blue da black nectie amma be d'aura ba ya ajjeshi se Amrah ta shigo yau zey titsiyita itace mey cewa ta iya d'aura nectie.Wannan maganar kam da dad'ewa suka ta'ba yi shikuma baya mantuwa be manta ba.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now