Chapter 4

1K 110 0
                                    

      Wannan type d'in kadanba da wuya ba,nayi about 400+ words ya goge and  you guys don't even bother to comment or vote😧 manage pls short chappy.

    
      Lokacinda Mommy ta shiga d'akin Shettima ya juya baya yana zaune daga gefen gadon,itama daga gefen ta zauna tare da d'ora hannunta kan kafad'arsa.

    "Shettyna" Ta kira sunansa.

      "Da gaskene abinda waccen matar ta fad'a?" Ya tambayeta ba tare daya juyo ba.

        "Hakane shetty amma.." Bata 'kare ba  ya katseta da fad'in"Mommy meyasa? Kunsan bana so nayi nesa da gida ,ko boarding ma baso nake ba balle har wani nisan waje I don't want".Ya 'kare maganar tare da juyowa.

     "Shettyna tafiya wani guri karatu baya nufin bazaka dawo ba kuma ma zaka ke zuwa hutu ga waya ma zami keyi akai-akai  Shettyna za'binka ne ka za'bi country d'in da kake so".

    Shiru yayi kamar mey nazari" Mommy I'm going to miss you ".Yayi maganar kamar 'karamin yaro.

       " I know, be strong my man mana".

       "Mommy amma waccen matar".

      "Next time kai zan fara fad'a ma".

      Gid'a kai yayi alamar "eh" Mommy ta jawoshi jikinta "Now  ka yarda zakaje?"

     "Mommy abinda kikeso shi nake so".

      " That's why I love my son".

       Mommy dad'i taji sosai batai 'kasa a gwiwa ba Appa yana dawowa ta sanar dashi.

    
        ★°~•~★°•~•★°~•~•★°

         Yana sanye da sky blue shirt  long sleeves da blue jeans ,zaune yake akan  couch hannunsa ri'ke da iphone d'insa(Waiting for me to tell you the version, nayy😂 guess!)

      Dukda cewa kansa a sunkuye yake be hana ma gano irin kyawunsa ba ,hooo! kamar bashine yaron da kuka sani ba da.Shettima naku de ,kamannin Mommy sun  sake bayyana a fuskarsa da farinta haka dogon hancinta da yanayin doguwar fuskarta duk irin nashi idanuwansa dede ga gashin kansa mey she'kin gaske kwance luf-luf.Shettima ya zama cikakken saurayi mey jini a jika dukda a zaune yake be hana na gano yanayin tsahonsa ba ya 'kara tsaho fiye da 19th age d'insa a baya ,yanzu kam yana 25 kenan.

     "Come on pick my call" Naji ya fad'a fuskarsa ta nuna alamar disappointed.

       "Amrah please" Ya marairaice kamar zeyi kuka.

     Yayi dialing number kusan sau 20 amma ta'ki d'agawa daga baya ma kashe wayarta tayi.

      Amrah sau biyu ta sake had'uwa da Shettima tun bayan tafiyarsa Dubai karatu ,lokacin daya zo first holiday nashi banda wannan time d'in basu kuma ganin juna ba.Wani zuwa dayayi Amrah tana boarding school haka yasha haushi haka next zuwa tana gombe abu kamar wasa had'uwarsu ta gagara duk tsahon shekarun da aka d'auka ,ko bayan data kammala boarding school d'inta basu had'un ba harta soma karatun diploma a yanzu ta kammala ND,computer science.Shettima ko yanzu maganar da ake ya kammala masters nashi under Engineering.

      Be dad'e da samun number na Amrah ba amma ta'ki d'agawa ya rasa dalili,ita kuwa ta jima da samin number sa shiyasa amma fafur ta'ki d'agawa ita kanta batasan dalili ba,yanzu jin ance ya kusa dawowa gabaki d'aya ta d'auke 'kafa da gidan Mommy har tsoron ranar had'uwarsu take gabad'aya kunyar su had'u take ji musamman idan ta tuna da yarintarsu wani abun setaji dama batai ba,a yanzu tana shekara ta 21.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now