Chapter 62

802 57 1
                                    


     *Gasky na tabbatar wasu sunyi falling ma Shetty dan a page 61 comments ma kad'ai  sheda ne😝,nide nace banda jealousy ...lokacinta neh,ko kun mance ansha gwagwarmaya ne*😂😂

     ____________________

      Da misalin 4:36pm Amrah ta gama kammala komai abinda ya kama daga girki har shirinta ,yanzu ta sauya cikin doguwar riga red cotton lacey material mey V neck ,  anyi mata adon flower ba'ki.Kwalliya mey kyau ta tsara a fuskarta ,bayan powder data sa da kwalli se eye liner da lipstick rose red, fashion d'in earing ba'kin stones  gashin kanta da farko tasa hula ba'ki taga de beyi ba sosai dan haka ta cire ta d'akko band ta saka ya d'an sa'ba d'innan jelar gashin ta saketa daga 'karshe ta d'anyi mata lan'kwasa.Siririn abin hannu golden tasa  yanada stones shima black,'karshe ta fesa turare mey soft 'kamshi ta d'akko wayarta ta sakko 'kasa.

    Kan sofa ta zauna time-time tana duban lokaci dukda tana amfani da wayarta.

      Ba'a fi 10min ba tajiyo shigowar motarsa  ai tuni ta saki wayar gefe,duk seta tsinci kanta da jin kunya kuma da bata lura gown d'in ta kamata ba se yanzu.A ranta se shawarwari take ita fa batasan ya ake tarbannan ba ,nan ta shiga muttsuka yatsu tana a tsaye duk take hakan.

    Qlin! Taji door bell yayi ringinging,da'kyar ta saita kanta ta 'karasa 'kofar ta bud'e ta wani ma'kale daga baya tana 'kasa da ido.

   'Kamshin turarenta ne ya fara masa sallama,idanunsa  sekace zasu zubo 'kasa ko 'kofar baya kallo ya rifeta Amarya kam an kasa d'agowa.

    "Sannu da dawowa" Ta fad'a cikin siririyar muryarta.

    Taku d'aya biyu ta ganshi a kusa da ita dama batada tazara sosai da bango taku d'aya tayi tajita a 'karshe.

    "My kyakkyawa wani salon ne haka ,jan rai ne ko kuwa 'kwalele ake mini?"

    Tana d'agowa suka had'a ido tayi saurin d'aukewa bata zaci kusar tayi haka dayawa ba.

    Hannu yasa ya d'ago ha'barta komai na fuskar ya 'kayatar dashi musamman idanunta data sauke 'kasa dasuka sha eyeliner eyelashes d'in sun kwanta.

    Saukan  kiss taji a kai kafin a lips d'inta,duk ta rasa nutsuwa ,no'kewa ta soma yi nanne ta dawo dashi daga duniyar daya shulla.

     "Kai Amrah rowa?" Yayi maganar murya a raunane.

    "Abinci fah"Ta fad'a.

     "Ni nace miki ina jin yunwa?"

     Shagwa'be fuska tayi kamar zatai kuka "Abincin nawa ne bazakaci ba?"

    "No baby ni na isa ,ba haka nake nufi ba" Ya kamo hannunta.

    "I mean ked'in kad'ai you're enough sede kin fiya rowa".

     " Nide mije kaci abinci".

      "Kafin abincin kin mata da wani abu".

     " Mey ?"Ta tambaya tana kallonsa jiran ya fad'a.

     "Wanka".

      Murmushi tayi dama a zuciyarta ta tuna da hakan amma kuma gudun abinda zey biyo baya take.

    " Kuma ke zaki mini".

     "Shikenan".Tayi maganar a ranta.

     Kalar tausayi tayi tace"Kana so na 'bata kwalliyar da nai".

    " So kike ki zille de".

     "A'a ni ba haka bane" Ta kare kanta.

     "Toh se yaushe?"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now