Chapter 6

892 85 0
                                    

      Bayan sin 'kare dinner suka komo parlour nan aka dasa sabuwar hira kamar ba gobe, se 11:12pm kowa ya koma d'akinsa badan hirar ta 'kare ba.Wayarsa ya d'auka ya lalubo "My Amrah" kamar yayi dialing kuma seya tuna dare yayi zata iya yuwuwa kotayi bacci.Hakannan ya ajje wayar yayi shirin kwanciya,da tunaninta yayi bacci.
 
  
     Washegari  bayan yayi sallahr subh ya koma se around 10:02am ya farka,bayan yayi shower yayi shirinsa cikin shirt blue da ba'kin jeans yayi brushing gashinsa bayan ya feshe turare  a jikinsa ya sakko 'kasa.

       A dining table ya riskesu dukansu,duka su ukun Mommy,Appa da Aunty ya gaisar sannan ya samu seat ya zauna Husna tana gefensa.Suma 'yan matan suka gaisheshi Rahinatu seda Aunty tay mata ido ta gaidasa murya ciki-ciki.

   Yasan dama halin yarinyar kwai rashin kunya shiyasa baya shiga huruminsu Sa'adatu ta fita girmama na gaba kuma yarinyar bata nuna banbancin ba mahaifiyarsu d'aya ba.Shima a gurinsa haka ya d'aukesu a tamkar Mommy ta haifesu .

      Cikin kwanciyar hankali suka 'kare breakfast d'in bayan nan Mommy ta d'akko present d'in data tanadar masa.Anyi wrapping abin bazaka iya banbancewa ba frame ko photo? Gashi babba rectangular shape.

    Yana zaune kan Sofa dake palourn sauran yaran suma suna zazzaune Aunty Hannatu tana one sitter ta zuba ido tana so taga 'karshen abinda za'a iya bawa d'a.

    Hannunta ri'ke da present d'in ta sakko ,daga gefen d'an nata ta zauna."Open up"Ta mi'ka masa a ranta tana tunanin yaya ze d'auki kyautar.

     Cikeda zumud'i ya fara 'bare wrapper d'in a hankali hoton fuskarsu shida Mommy yana fitowa har complete suka bayyana."Mommy"Ya kira sunan a hankali bandan ta amsa ba se dan tsabar farinciki da baze iya misaltuwa ba.

    Har wani 'kwallan farinciki ce ta fito a idanuwansa ,hannu ya d'ora akan fuskokinsu yana shafawa.

    Photo ne da sukai 2yrs back wani zuwa da yayi hutu ,yana sanye da blue black T-shirt haka wandon ma black ya sanya silver wrisk watch yana  zaune kan wani stool Mommy tana daga gefe itama a zaunen take opposite dashi ta gefe sede ta kallo camera kamar yadda shima yayi,tana sanye da farar doguwar abaya tayi rolling da farin mayafi.Duka su biyu sunyi murmushi Wanda ya bayyana kamannin da suke sosai da Shettima.

     Aunty Hannatu ta 'kafe da'kyar take had'iye yawo dan tsabar bakin ciki "Wannan wane irin so take wa yaronnan ,what kind of love?" A zuciyarta take ta tambaya.

    "Mommy you're genius, everything to my world, amazing gift ever" Shikad'ai yake sambatunshi ya kasa dena murmushi .

   Itama tana daga gefe tana murmushi tana jin dad'in yadda yake murna da abinda ta bashi."Kai! you deserved this" Walida ta kyasta musu pic sega hasken flash.

   Ba 'karamin kyau pic d'in yayi ba Shettima ya shagala da kallon babban hoton  Mommy kuma tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi zalla.

     Su Wafah take suka kar'bi photo d'in suka soma d'aukan pic dashi za'a poster a Instagram😢 dukansu suka jeru Mommy ta zauna kusada Aunty Hannatu yaran kuma suna daga gefe  Hussy 'yar 'karama ta ri'ke photo d'in Mami ta d'aukesu duka dan kowa ya'ki yarda ya fita bayan ta d'auka ita ta shiga Wafah ta d'auka haka sukaita 'kyaste-'kyaste Appa ne kawai bayanan.

    Bayan a tsagaita da hoton Aunty Hannatu ta samu damar magana."Abu yayi kyau fa"

   "Mommyn Shetty gara kici lokacinki kafin 'yar wasu ta fara cin nata lokacin mukam se kallo Allah yasa de d'an namu karya manta damu duniya tayi masa kyau ga jan fire a gabansa mey zeyi da  busashshen ganye"

    Shiru d'akin ya d'auka ba wanda yayi tsammanin wannan maganar ,Mommy ya'ke kawai ta d'anyi ta rasa mey zata ce tunda ba gama fassara maganar tayi ba bata gane mey hakan yake nufi sede tasan ba abune wanda za'a d'auka a matsayin abun raha ba.

    Wafah ma a wurinta hakane amma Walida mey wayo 'kwa'kwalwarta tayi alert nan danan ta fassara maganar.

      "Mey abu da abunsa inbanda abinki Aunty taya mara abu zey jiyewa mey abu d'acin abu shida ba hurumunsa ba"Walida tayi maganar fuskarta d'auke da murmushi kamar ba itace be fad'in hakan ba.

    Cikeda mamaki Aunty Hannatu ta kalli Walida tana mamakin yadda ta gane mey take nufi kuma ma waya koyamata irin wannan.

    Mommy kallo tabisu dashi ta d'an gano Walida ramawa tayi amma fassararce ....

     Shettima kan tun farkon zancenta ya gane dad'i yaji da Walida ta mayar mata dan shima yaso mayar mata amma kuma bayason 'kananan zance kuma he is not in the mood a yanzun.

     Ganin Aunty Hannatu na sake so ta d'auko wani zancen yace " Walida kar'bi wayata ki turon pics d'in da aka d'auka yanzu".

     Haka yasa Aunty Hannatu tayi shiru badan taso ba Rahinatu se harare-harare take.Daga baya ma d'aki suka koma su Wafah ma d'akin suka wuce yau ganin Shettima yasa suka 'ki zuwa school.

    Shettima seda ya faki ido wajen 12pm ganin Mommy ta tafi d'aki ya koma nashi ya ma'kala babban hoton nasu a bango sannan ya saci jiki ya fita ko driver be tuntu'ba ya kaisa ba dan bayaso aji fitarsa.

     A napep ya 'karasa gidansu Amrah.Tana d'aki taji 'kwan'kwasa 'kofa  ta fito kuma taga har Ummie takaiga bakin 'kofar dan haka ta juya ciki.Tana daga d'aki ta tsinkayo muryar Shettima shida Ummie suna magana,nanda nan hannunta ya soma gumi.

      Sorry for the late update, jiya na d'an fita and kwana biyu laziness ya kamani😂 typing yana mini wuya inshAllah a yau zanyi updating SALEENA I know some of you are waiting. Lots of love😘

Dijensy❤


  

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now