Chapter 39

429 37 0
                                    

      *TAGAYYARA FANS GROUP AND DEEJA ONE LOVE NVL GRP wannan page d'in sadaukarwa ne gareku ,ina jin dad'in comment d'inku sosai sosai ina ji daku gabad'ayanku ban tsame ko mutum d'aya ba.Lots of love😘*

      ______________________

         Har gari ya waye Kamal be ko motsa ba kamar matacce numfashi dayake ne yasa za'a tabbatar be mutu ba.Amrah duk wani harkokita data saba tayi ta kammala breakfast ta fara cin abincinta tana tsammanin taga ya fito amma harta gama babu alamarsa ,d'akinta tayi shigewarta ba tare da ta damu ba ita da za'a cigaba da hakan ma da yafi mata.

    ***
     
      Har yanzu su Walida basi iya samu sun tunkari Mommy da maganar Shettima ba akan abinda ya faru don ko basu samu fuska ba ,iya kaci su gaisa da ita su fita mata daga d'akin ko wata maganar daban wacce bata shafi Shettima ba.Sun fahimci sauyi gameda ita kana gani kasan tana cikin damuwa amma tana 'ko'karin dannewa,wani abu daya sake 'bata mata rai shine rashin dawowarsa gidan a tunaninta zey dawo ai ya bada ha'kuri ya amsa kuskurensa.Sau d'aya ta dangana zuwa d'akinsa wani abun mamaki taga kaf kayansa na wardrobe babu(Aikin Aunty Hannatu) hakan ya tabbatar mata da kanshi ya kori kansa kenan ya za'bi ya bar gidan, ita kuwa bazata kirashi da sunan ya dawo gida ba sede idan da kanshi ya dawo.Ita yanzu haushin kanta take ji na yadda take nunawa yaron so gani take son da take masa yasa tarbiyyarsa ta samu nakaso.Da ace ya damu da ita ai baze bar gida ba.

    Mami data dawo daga Gombe su Walida ne suka tsaigunta mata a d'aki ranta ba 'karamin 'baci yayi ba dan haka da kanta ta tinkari Mommy ta tace sam wannan maganar bata yarda da ita ba dole ta kira Shettima ya dawo gida taji daga bakinsa ita koh Mommy fafur tayi 'kememe bazata kira shi ba sede idan shi ya kira daga baya ma tasa wa Mami kuka wai d'a yana ta wahalar da ita,daga haka Mami bata sake maganar ba itama ta had'a kayan ta ta bar gidan tace ita data dawo se Shettima ya koma gida, suna ji suna kallo ta tafi su Walida ba yadda basi da ita ba ta zauna amma ta'ki harda kukansu Mommy ta na d'aki duk abinda suke itama tana jiyosu ita kanta kukan take sabo da sha'kuwa shekaru da dama ana tare da Mami tana jinta tamkar 'yar uwa.

    

      ______________________

      Ta 'bangaren Shettima kuwa yana nan ya sake ramewa yayi mugun duhu saboda 'kin cin abinci Ahmad bakinsa kamar zeyi ciwo akan masa magana amma ya'ki ji,haka zey fita aiki ya dawo ya tarar dashi beci komai ba.Ya shawarce shi daya je gida ya d'akko CV d'insa yayi applying job amma ya'ki shi kawai yayi given up life yana ganin baida wani sauran jin dad'in rayuwa a yanzu tinda ya rasa Mommy ,baida sauran Family ya rasa Amrah,Dad,Mommy baida wani kuma sauran farinciki .

       ★★★

    Kwana uku cif yayi kafin ya farka daga uban nannauyan baccin da ya shilla.A hankali ya soma bud'e idonsa har ya waresu tar a d'akin jiki a sanyaye ya mi'ke zaune da sauri ya dafe kai har yanzu da ragowar ciwon kai,kallonsa ya mayar kan wrisk watch d'insa 7:54pm ya gani kansa ya kulle daya tuna lokacin daya shigo d'akin ma gabad'aya 8 ma ta wuce amma yanzu 7 ,kansa ya d'ago ya dubi agogon bangon shima haka ya nuna ya laluba aljihunsa ko zega wayarsa yaji bata ciki.Wani abu daya sake jan hankalinsa shine ciwon wrisk d'insa daya lura harya soma kamewa kwata-kwata ya kasa tuna yanda ya samu ciwon sede be manta da case d'in dayai failing ba yana ransa abin.

   Wani haushin kansa ne ya sake shigarsa besan sanda ya buga tsaki ba.

    Amrah gabad'aya kwana ukun nan ta shiga wani hali ta rasa abinda zatai ,d'akinsa ta fara dubawa jin shirun yayi yawa taga bayanan se pieces glass daya fashe ga bedsheet da pillows yashe a 'kasa tun daga lokacin tsoro ya kamata daga nan ta dawo d'akinta tana tsammanin yana d'akin opposite da nata sede batason yadda zatai ta iya knocking ba ganin an kwashe kwana uku zuciyarta ta bata mutuwa yayi ,fargaba take shikenan da gawa take kwana a gida.

      Wani lokacin har baza hanci take a jikin 'kofar wai ko zata ji wari.Tana zaune yau a d'akinta zuciyarta ce take ta fad'a mata taje ta gwada bud'e 'kofar ,hijab datai sallah yana jikinta ta mi'ke tana addu'a ta fita daga d'akinta kamar wacce 'kwai ya fashe mata ta soma takawa zuwa 'kofar d'akin.

    Chak ta tsaya lokacin data ga an murd'a handle kamar zata zura da gudu taga mutum ya bayyana ,kallon-kallo suka shiga yi ita data gama bayar wa ya mutu batasan meyasa ba setaji ba dad'i ganinsa raye da tunun aurenta dashi ya 'kare ta koma gida su.

    Shi kuwa gabaki d'aya ma se yanzu ya tuna da wata Amrah ,take ya nemi damuwar dake ransa ya rasa ashe Amrahnsa tana tare dashi.Haka kawai yaji ta bashi tausayi baisan tsahon lokacin daya d'auka a d'akin ba 'kila tana ta jiran fitowarsa wata'kil ma tayi kewarsa.

    "A..amrah".Ya kira sunanta yana takowa daf da ita.

    Jitake kamar ta gudu da'kyar ta daure ta tsaya ta kawar dakai daga kallonsa dan wani tsoro-tsoronsa take ji musamman yadda taga sauyi daga jikinsa ya d'an rame gashin kansa ya wani cukurkud'e danma Allah yasa kan nashi ba 'kuda-'kuda bane (Da mutanena sun gudu 😂) irin zibin na fulani ne a kwance yake sede ya taru sosai ba isashshen gyara.

    " Kin fito dubani ne?"Yayi saurin tambaya fuskarsa yana bayyana murmushi irin murmushin yarannan wanda yake bawa Amrah tsoro.

   A rikice ta d'aga kai ta tsorata da lamarinsa kwana uku yana d'aki shiko meyake ? Ya batun abinci? K'alau kuwa Kamal yake? Meyasa ya fasa mirror na d'akinsa?

   Kamar ance kalli ta lura da hannunsa wrisk d'insa partial scratch dayai red alamar ciwo.Kula da inda take kallo yasa yayi saurin cewa "It's nothing Amrah karki damu". Ya zira hannunsa a pocket d'insa yana 'boys ciwon.

    A d'ari-d'ari ta juya da sauri ta shige d'akinta kamar zata kifa da gudu ta fad'a bathroom tana numfarfashi.

     "Laila ha'illa anta subhanaka inni kuntum minazzalimin" Taita jerowa a zuciyarta.

     D'umin hawaye taji a kumatunta yana zirarowa tausayin kanta take ji zallah tana fatan Allah yasa ba abinda take tunani bane,abu   uku take zato.Na d'aya ko aljanu ne da Kamal? Na biyu ko shaye-shaye yake na uku ko yana da ta'bin 'kwa'kwalwa.

   
    *Pls kuyi ha'kuri da wannan banida isashshen charge idan nace zanyi typing mey tsaho bazan samu damar editing ba har nayi posting so zamu tsaya anan.

  
    _Ya kuke gani readers, Ku mey kuke tunani gameda Barr Kamal ? nide nace.....

    #Team Barr

    #Team Shettima

     #Team Amrah

  
   Comment

Dijensy❤

    

    

   
  

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now