Chapter 22

504 48 1
                                    

   
      Ina jin dad'in comment d'inku masoyan littafinnan.Phew!😰 naga comment iri-iri fah😱 Barr Kamal yasha tsi....😯

   Readers 'boyayyayyu na gaisheku fah,hmm! muje zuwa my ppl😘

     
      ~~~

        Wafah da Walida suna d'ankin Mommy ,d'aya tana sauya bedsheet d'aya kuma tana gyaran lotions na kan mirror, Mommy dake kan couch tana kallon yaran nata.

       "Walida wai kekam da gaske kike bazaki bikin Amrah ba"

    "Ai na riga da na rantse ki dena ma tayar da maganar dan ba zuwa zanyi ba"Cewar Walida.

    "Amma de kam ba dad'i"

    "Ba dad'i? Mu tayi mana ras
hinsa ai wlhy abinda tayi wa Ya Shettima baze ta'ba gogewa ba"

     "Ke ya ta'ba zuwa yace miki suna son junansu ?"

     "Ai ko ba'a fad'a ba munsan suna soyayya"

    "Toh kuda kuke wannan maganar kada ku manta halin dayake ciki a yanzu ,kwanaki kad'an suka rage wata uku.... ta cika ... "

    "Mommy ki dena wannan maganar jikina yana bani  Yaya Shettima za'a sakeshi"

    "Muna fatan hakan".

     " Mami mey tace?"Wafah ta tambaya.

     "Itama bazata ba ko waya batai da ita ba fishi ma take dasu ,d'azu ina kallon Ummin Amrahn ta kira amma ta'ki d'aga wayar.Ai tasan basu kyauta ba".

    " Allah ya kyauta yanzu de ayi a gama gyaran"Mommy ta fad'a.

    "Aiko inde bazaki ba nima na fasa zuwa"Cesar Wafah.

    "Zaki dawo hanya ne"Cewar Walida.

    Da sauri suka 'karasa aikinsu sannan suka fita,Mommy batasan ya zata d'au zancen nasu ba,dan ita kanta tana tausayawa d'anta bazata so ya samu labarin hakan ba.

      _____________________

        Tunanin Amrah ya kasa gushe masa a rai,musamman idan ya tuna Barr Kamal ,shi dama tun farkon had'uwarsu a wajen dinner sanda ya 'baro masa lemo a jiki yaji beyi masa ba.So dama tun lokacin suna tare da alama wajenta yazo a lokacin ,yaushe Amrah ta fara shiga motar wani harya kaita wani gurin? Amma Amrah bazata so wani bayan shi ba,tayi masa wannan al'kawarin ." No sede shi Barr Kamal d'inne yake sonta" Ya fad'a a zuciyarsa yanaso yayi calming heart d'insa amma dukda haka wata zuciyar tana fad'a masa negative.

     ***

    
   Ita duk wata hada-hadar biki da sike kawai kallonsu take ,families d'insu daga gombe ma yau suka zo hayaniya ta cika mata kunne ,ta shige 'kuryar d'aki it's kad'ai tasan abinda take ji a halin yanzu.Barr Kamal harda bugo uban card na lunch tace bazata ba bekoh damu ba yace mata yaji dad'i kud'insa ya huta.

  

    BAYAN D'AURIN AUREN  BARR KAMAL AL'KALI DA AMRAH  MUHAMMAD
    
    
        Fuskarta a lullu'be cikin mayafi wayarta tana ri'ke a hannunta se jujjuyata take, itade tasan da mutane 'yan rakiyar Amarya a d'akin datake amma ba jinsu take ba saboda hankalinta baya gurin.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now