Chapter 36

522 44 0
                                    


    Aunty Hannatu a idonta gari ya waye ta kasa ta tsare tana zaune a parlour 'kafa d'aya kan d'aya tana jira taga d'aya daga cikinsu Mommy ko Shettima tasan de Mommy confirmed ta ga hoton Shettima ne batada tabbaci idan ya sani.Can't wait taga yadda uwa zata juyawa d'anta baya,d'anda batada kamarsa tuna gata da kulawar daya sha yana yaro ta shigayi wani sabon ba'kinciki da hassada ya tokare mata wuya,wani 'bangaren zuciyarta tana kwantar mata da hankali "Komai yazo 'karshe ,mey nuna masa gatan ina yake? Uwar ma wayasan halin datake ciki".

   Yau Rahinatu da ba zaman parlour take ba segata ta sakko,tana wani ta'be baki ta 'karaso wajen babar tata.Daga gefenta ta zauna " Aunty yau idan bakiga abinda kikeso ba an ciki wasa yasin"Rahinatu ta fad'a.

   Guntun murmushi tayi tace"'Karshe ya 'kare a kanki keda 'kannanki dan suwa nake yi?"Ta 'kare maganar tana harararta.

   Hakan yasa taja bakinta tayi shiru ,duka su biyun hankalinsu na kan matattakalar bene suna jira suga mummunan al'amari.Rahinatu a zuciyarta harta d'asko Shettima ya sakko yana kuka Mommy kuma tana gaba zata bar gidan.Itako Aunty Hannatu ta gama hangowa wai Mommy  shanyewar 'barin jiki ya kamata.

     Maganganun su Walida ne yasa suka dawo daga duniyar tunanin da suka tafi.

     "Wafah ki bani nasa biro na mana a ciki" Cewar Walida tana mi'ka hannu zata kar'be school bag d'in hannun Wafahn wacce sike sharing su biyun basa ta'ba raba jakar makarantarsu yanzu waec suke zanawa ma.

    Sa'adatu da Husna ma suna biye dasu a baya wanda school d'aya suke tare suke zuwa,yadda su Sa'adatu suke dasu Walida yafi yadda sha'kuwarsu take da Rahinatu ita da abi kad'an d'ura ashar ko ta dakesu shiyasa basa shiga shirginta ,hakan yana 'kona mata rai hatta Aunty Hannatu sede tana ganin ai komai zezo 'karshe wataran ma bazasu ga su Walidan ba.Ita a yadda ma ta tsara plan Saudiya zata kwashesu su duka.

    Wani dogon tsaki Rahinatu taja,a jam'u suka gaisheda Auntyn ta amsa da "Lafiya" suka wuce dinning dan karin kumallo suka ga wayam.

    Husna ce ta tattalo wajen Aunty da gudu kamar zatai kuka "Aunty ba'ai abincin breakfast ba kuma na makara".

    Ta bud'e baki zata zageta sega Walida itama ta fito zuwa parlour "Naji yau Mommyn shiru bata sakko ba".Cesar Aunty Hannatu. Dama yawanci Mommy ita take girkin safe Aunty Hannatu tafi yi da rana wani lokacin tare ko su Walida idan ba school su tallafa.

     " Mommyn? Ai nayi knocking a d'akinta naji kamar bata ciki nayi tunanin ko tana 'kasa".

     Abinda take tunani ya faru kenan.Aunty tayi tunani.

    "Toh ko..." Bata 'kare ba sega Mommyn tana sakkowa 'kasa ,daga yadda suka ganta sunsan akwai damuwa a tare da ita yadda take takawa a sanyaye fuskarta tayi zuru-zuru alamun batai bacci ba kenan.Rahinatu da Aunty Hannatu kad'ai suka gane hakan suda suka san mey suka 'kulla.

    Sam ba haka taso gani ba wani abun mamaki suka ga Shettima ya 'bullo shima a baya.A tare suka had'a ido da Rahinatu.

    "Mommy ko yau lafiya baki sakko da wuri ba?" Ta tambaya dan ta kasa iya yin shiru.

    Murmushin dole tayi tana fad'in"Lafiya lau baccine yau ya zaunar dani".

    Kai ta gid'a a ranta tasan ba hakan bane tana mamakin yadda akai ta iya danne wannan al'amarin bata kawo zata iya 'boye mata ba,ga dukkan alamu Shettima baisan komai ba dan ba suga alamar sa'bani ba.

     "Wannan wane irin son d'ane da har laifinsa 'boyewa take"

     Tunani ta shiga yi ko sun kashe matsalar a d'aki ita sikewa pretending.Amma ai Mommy batada wannan wayon ,ba lalle hakan bane.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now