Chapter 27

483 48 3
                                    


   Suna isa gidan ko shigowa basi ba Sa'adatu da Husna suka tattalo da gudu se tsalle,Husna ta ma'kaleshi tana ta zuba masa tambayoyi ina yaje?

    A parlour suka tarar da Mami da  Aunty Hannatu itama da fara'arta ta 'karaso inda suke,se barka take masa yana d'an amsawa sama-sama.Mommy da kanta ta had'a masa ruwa mey zafi tace yaje yai wanka ya huta kafin yaci abinci.

     Tare da ita suka 'karasa yin girki su Aunty harda potatoe ball tasan yana so (Hmm  kuji fa )

      Rahinatu kuwa bata gidan ma batasan dafdalar da ake ba ta gargad'a bikin 'yar kishiyar yar babar   'kawarta😱

      ______________________

    
     4:38pm ya 'karasa gida d'akinsa ya wuce ,bayan ya rage kayan jikinsa ya zauna gefen gado yana sake duban kwalin wayar daya siyo a hanyar dawowarsa.

    Yaude gashi ya cika al'kawarin daya d'auka mata , besan ya zataji ba tunani ya shiga yi koya fad'a mata amma kuma wata zuciyar ta hanesa kar ya jawowa kansa 'bacin rai dan baze iya jurar ganin reaction d'inta ba.

   'Karamar wayar 'kirar Nokia ya ciro daga kwalin ya zira layi a ciki ya ajje gefe guda, sa'ke-sa'ke ya sake tsunduma.Yanzu da kowa ya gama cika al'kawarinsa wane irin zama zasu cigaba dayi? Zama na tsakani da Allah ko kuwa zama wanda ya qudurta a ransa? Tabbas ya sani Amrah ba sonshi take ba idan ma zaman tsakani da Allah ne taya zey shawo kanta ta soshi ?

      Ya shafe fin hr kafin ya tashi ya wuce kitchen,coke ya ciro a fridge yaja stool daga gefe ya zauna yana kur'bar kayansa.

   Food warmer ya gani kan drawer a killace ,kamar baida niyyar ta'bawa seda ya kusa 'kare coke d'in ya bud'e ,take 'kamshi ya bigi hancinsa pride rice ce rayayya se zuba 'kamshi take.Saurin mayarwa yayi ya rife ko mey ya tuna oho,spoon ya d'akko ya sa'ba murfin ya zira cokali ya d'iba  kad'an ,a saitin hancinsa ya shinshina abincin kamar yanaso ya gano wani abu hakade ya gaji ya rufe ya bar kitchen d'in.

     Dukda taji alamar shigowarsa bata damu ba dan tasan ba shigowa yake ba ,tana zaune zaman shiru  ,doguwar rigar atamfa ce a jikinta green colour mey ratsin ba'ki tayi mata cif d'aurin d'an'kwalin ba wani 'kan'karewa a ciki kawai ta d'aura de irin wanda ake d'ora felar dama da hagu a waje guda a soke d'innan.

    Tayi nisa tana kallon waje ta window aka turo 'kofar,a kid'ime ta juyo kamar wacce tayi laifi zumbur ta mi'ke.A hankali ya tako zuwa inda take tazararsu ba yawa befi taku uku ba.Ba tare da yace komai ba ya mi'ka mata wayar.

   Seda ta d'anyi sakanni Tana duban wayar kafin tasa hannu ta kar'ba.Tana so tayi magana amma ta kasa se duban wayar take a ranta tana fad'in Allah yasa ba 'kwalele zey mata ba.

    "Kiyi amfani da ita akwai sim card ina tunanin yafi kiyi amfani da irin wannan dan bana son social media ya gur'batan tarbiyyar matata".

    " Nagode". Ta fad'a.

      Bece komai ba ya kasa sauke idanunsa daga kanta,yau ba mayafin a jikinta karo na farko daya ta'ba ganinta a hakan ba 'karamin kyau tayi masa ba gashi fuskarta ma dukda ba kwalliya amma idonta da kwalli yau.

    Duk setaji ta tsargu jin idanunsa   a kanta ,se addu'a take ya fita.

    Kamar yana so yace wani abu amma beyi magana ba kawai ya juya ya fita tabisa da ido Alhamdulillah ta fad'a a zuciyarta.

     Kallonta ta mayar kan kwalin cikin hanzari ta zaro wayar da charger d'in dad'i ya isheta zataji muryar iyayenta.

   

    _______________________

  
     Cikin dark blue shirt mey gajeran hannu ya shirya da ba'kin jeans ya fesawa jikinsa turare yana kallon kansa a mirror,sosai haskensa ya disashe banda ramar dayayi ,knocking da akai a 'kofar yasa ya dawo daga tunani.

    Mommy ya gani bayan ya bud'e 'kofar tana tsaye fuskarnan fal da murmushi."Saura abinci"Ta fad'a tana dubansa.

   Kai kawai ya gid'a  suka sauka 'kasa ,kowa ya hallara yana jiran sakkowar tasu.Aunty Hannatu kawai ya'ke take ita duk a tsarge take jinta.

    Suna ci suna hira shi abincin ma kad'an yaci yace ya isheshi ,a parlour suka zauna dukansu suna ta hira yana sa baki kad'an-kad'an bayan sallar isha'i ya koma d'aki.Se yanzu ya kula da rashin sauyawa da d'akin yayi ba alamar 'kura data nuna alama an dad'e ba'a zama a d'akin yasan aikin Mommy ne wannan. Kan gadon ya kwanta yayi pillow da tafin hannunsa biyu yana kallon pop.Lokaci guda wayarsa ta fad'o masa a rai ,baze mance ba a gida ya barta tun ranar daya bar gida.

    Mi'kewa yayi ya nufi drawer a ciki be ganta ba ,wardrobe ya nufa yana bud'ewa ya ganta kuwa.Yaci sa'a kuwa sanda ya kunna yaga akwai charge.

    Password daze saka ya bud'e ne ya tuno masa da ita,dukda dama tana ransa d'in sede akwai abubuwa daya kulle masa kai a lamarinta.Notification daya ganine ya katse masa tunani ,a take ya typing Amrah wayar ta bud'u ,message ya gani daga wajenta bayan ya duba.

    Bud'ewa yayi zuciyarsa tana fad'a masa 'kila "Night text ne data ke yi masa  ne tun kafin a kamashin".Nutsuwa yayi tsam ya soma karantawa yaga fasalin sa'kon daban.

   Allah beyi zamu kasance tare ba kamar yadda kowacce zuciya tana da nata babbancin ra'ayin haka lokaci d'aya lamari yana sauyawa yanda ba'a tunani.Minyi wauta da bamu tsaya a iya matsayinmu na abota ba,mun d'auka ko cewa sha'kuwar da mukai soyayyace ashe ba hakan bane.Se yanzu na gane banbancin friendship da soyayya ,a yanzu da kake karanta sa'kona bazaka fahimci abinda nake nufi ba harse lokaci yayi ,lokacin da ka bud'e wa rayuwarka sabon shafi,a lokacin da ka had'u da masoyiyar gaske bata abota ba.Naso ace ka halarci taron d'aurin AURE NA amma Allah beyi ba ,inaso kayi min fatan alkairi a sabuwar rayuwar dana shiga ,Barr Kamal masoyi ne na ha'kika kada kayi shakko 'kawarka ta samu partner na gari kaima ina maka fatan hakan.Nagode daka karanta sa'kona,ka manta mun ta'ba soyayya.PLEASE FORGET ME

  Battery low sorry guys

   
   Dijensy❤
      

TAGAYYARA(Complete)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin