Chapter 13

718 57 0
                                    

  Cikin razana da firgici ta dafe kumatunta ,cikeda mamaki take kallon Appa abinda bata ta'ba tunani ba ko a mafarki.

 
      "Meyasa bakya tauna magana kafin ki furta? Shin raini ne ko kuwa kinyi hakan ne dan ki ba'kanta mini?"

   Ransa a 'bace ya cigaba da magana"Toh ki sani idan kinyi hakane du dan ki ba'kanta min kinyi kuskure babba,kin wula'kanta kanki kin dangana kanki da kalma mafi muni ,kinga...."Ya nunata da yatsa cikeda warning tsabar 'bacin rai ma ya kasa fad'ar abinda ze fad'a ,zuciyarsa tana masa 'kuna ya fita daga d'akin.

    Wani dogon ajiyar zuciya taja tare da zama gefen gado,sosai  marin Appa ya shigeta dan harda guntun hawaye ido d'aya."Mari ,ni zaka mara ni..Hannatu ke aka mara"Abinda take ta maimatawa a ranta.

   Ta d'ora hannu aka ta sauke haka tayi tayi yana jin-jina kai.

        ***

Appa yana fita ya koma d'akinsa ya rasa meyake masa dad'i kalmarta tayi mugun tsaya mata dukda cewa bawai yana zarginta bane da wannan amma be cire kalmar "Karuwanci" A zuciyarsa ba.Yana cikin wannan yanayin akai knocking 'kofar d'akin.

    Da'kyar ya iya cewa "Shigo".

    Mommy ce ri'ke da tray a hannunta ,bayan tayi sallama ta  karaso ta ajje abincin kan table na d'akin." Barka da dare"

    "Yawwa" Ya amsa.

     Daga yadda ya amsa ta gano da damuwa a tattare dashi dan haka tace"Lafiya kuwa?"

    "Uhmm ,kawai nad'an gaji ne ina bu'katar hutawa".

    " Ayya ,Allah ya huce gajiya ga ruwan wanka ma chan a bathroom na tanadar maka nashigo d'azu baka d'akin idan kuma abinci zaka fara ci to".

    "Yawwa sannunki bara zan fara yin wankan".

    Da " Toh"Ta amsa sannan ta fita daga d'akin.
  
          
           ★★★

      Amrah tana tsaka da yin game a waya kira ya shigo wayarta da wata ba'kuwan number. Kiran farko bata d'aga ba se'a na biyu ta d'aga da sallama.

     Ko amsawa ba'ai ba daga d'ayan 'bangaeren aka soma magana"Amrahn Barrister"

    Gira ta had'e kamar tana gaban mey maganar kafin tace"Waye?"

     "Haba Ranki ya dad'e karkice baki gane Barr Kamal da kuka had'u a dinner ba".

    Amrah jin haka tayi saurin katsewa ,ita mamaki ma ta shiga yi ta yadda ya sami numberta.Tana wannan tunanin Miranda yake ta shigowa ba adadi ba 'ka'k'kautawa,ko minti 5 ba'ai ba da katsewar kiran sa'ko ya shigo.

    " Amrah a duniya ban ta'ba jin son wata 'ya mace kamar ki ba,ina masifar sonki a zuciyata Amrah ki d'aga kirana pls.Ba tafarar d'aya kake sha'kuwa da mutum ba ki bani dama pls Amrah muradina I love you very much".

     Zaro ido tayi tana saka maimaita text d'in ,tana mamkin daga had'uwa sau d'aya kuma ma son ba harda 'ina masifar sonki"Kalmar ta tsaya mata a rai.

    Sauri tayi ta goge text d'in ta koma temple run d'inta.Ba'ai 15min ba wani sa'kon ya shigo.

     "Goodnight abar 'kaunata wacce ta sacen zuciyata, bazan iya numfashi ba muddin baki karanta sa'kona ba.Ina matu'kar 'kaunarki,pls kiyi mafarki na".

     " Tohh!"Ta furta a fili.

     Game d'in ma jitai ta fita daga ranta dan haka ta ajje wayar ,tayi addu'ar kwanciya ta kwanta bacci.

      ------

Da asubah 'kara kirar Barr Kamal ne ya tasheta daga bacci ,idonta ya mata nauyi ta d'auki wayar taga number jiya already ta gane ,silent tasata kafin ta tashi.Bayan ta idar da sallah kamar ta sani ta duba wayarta taga text ya shigo."Hasken idanuna barka da safiyya ina fatan kin tashi cikin 'koshin lafiya da tunanin Barrister a zuciyarki ,albishirinki...jiya nayi mafarkinki kin bani firen soyayya.I love you Amrahta".

    Tsabar takaici batasan sanda tayi tsaki ba."'Karyar banza"Ta furta.

      'Yan mintina kad'an sa'kon masoyinta ya shigo ,tana karantawa tana murmushi kafin itama tayi reply,ita harta manta da wani Barr Kamal.

        ------

   Da yamma wajajen 5pm ba zato ba tsammani taji sallamar Husna ,tana tsakar gida ta juya baya.Waigowar da zatai taga tare suke da Shettima. Kamar wal'kiya ta 'bace se d'aki,tana numfarfashi,wani 'kwarjini yake mata kunyar ganinsa take musamman idan ta  tuna yadda take sakewa dashi a waya.

    Ammie seda Husna ta shigo parlourn ta gane gudun da take.Cike da girmamawa ya gaisheta,har lokacin murmushin fuskarsa be gushe be na ganin Amrah.

    Husna har d'aki ta shiga wajen Amrah,'kasa-'kasa Amrah take magana ta'ki d'aga murya kar Ammie tace tazo.Ganin surutun Husna ya isheta yasa ta kunna mata game ta bata.

    Basu wuce 30min ba ya  tashi ze tafi,Husna tayi saurin bata wayar ta fita waje karya tafi ya barta.Dad'i taji ganin Ummie bata kirata ba har suka fita.Kiran daya shigo wayarta ne ya katseta daga tunaninta.

      "MLV" Meaning My Love.

       Kiran farko ta'ki picking se a na biyu ta daure ta d'aga.

      "Queen pls mana so kike rashin lafiya ya kamani,gaskiya bazan iya tafiya ban ganki ba".

      " Na cewa Ummie mey?"

      "Zamu gaisa mana,kece yadda wani guduwa d'aki koh?"
 
       "Ka bari next time".

        " Da gaske fa nake ba tafiya zanyi ba,ki fito kawai ke baki missing d'ina bama,ki fito kawai dan bazan bar unguwarnan ba ba tare da na saki a idona ba yau kinji ma na fad'a miki".

    Be jira tayi magana ba ya kashe kiran,ta rasa ya zatayi ta soma
   

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now