Chapter 63

672 54 0
                                    

*Not edited*

    Washegari da safe ta gwada kiransa a waya dukda batayi tsammanin zey d'auka ba kiran farko taji ya d'aga.

    "Sweet darling". Ya fad'a cikeda walwala tamkar ba shine jiya mey fishi ba.

    Tayi mamaki jin hakan amma de ta basar itama ta saki rai" Ina kwana".

   "Lafiya lau my Amrah,ya su Ummi?"

    "Lafiya suke".

    " MashaAllah".

    Hira yayi ta janta da ita hankalinta ya kwanta tana ganin ya sakko daga fushin.

    Haka ta 'kare kwanaki biyunta dad'i ya cikata ,kasancewar ranar yana da aiki dan haka yace bayan ya tashi zey zo d'aukanta.Fulawar Jan 'kunshi mey kyau na bayan hannu ta kira aka tsantsara mata ,wajen 4:30pm ya kirata yake fad'a mata ya taho.

     "Ummi ji nake dama na 'kara 'kwana d'aya".

    "Toh seki zauna d'in kinji mukuma su zuba muku ido daga ke har shi d'in".Ummi ta fad'a.

    Dariya Amrah tayi dan yadda Ummi tayi maganar tana harararta.Mintina kad'an sega kiran Shettima koda ta d'aga yake fad'a mata yana 'kofar gidansu.

    Iso tayi masa ya shigo gidan suka gaisa da Ummi sannan ya fita yana jiranta ,dama sanda tace masa ya shigo a waya ta fad'a ba wai ta fita bane Dan haka bata ganshi ba dan d'aki ta shige.Tuna shekaran jiya tayi maganar daya fad'a mata na ai zata dawo gidanne zata shigo hannu haka yasa kuma ta soma kame-kame.

     " Amrah mey kuma kike a d'akin?"Cewar Ummi.

   "Gani". Ta fad'a tana gyara zaman handbag d'inta da gyalenta.

    Tana sanye cikin riga da skirt na atamfa dark blue mey ratsin pitch tasa mayafi pitch colour tayi yafen aka.

    Kamar batason takawa haka ta fito ,Ummi girgiza kai kawai take tana ta'be baki.Nan tayi sallama da ita dama tun kafin Abba ya fita da safe tayi sallama dashi.

    Yana tsaye jingine a jikin motarsa yana sanye da navy blue suit ya hard'e hannyensa a 'kirji yana binta da wani kallon zan kama ki ne.Itakuwa kallo d'aya tayi masa ganin yadda yake mata tasha jinin jikinta kamar mufuka ta zagaya 'bangaren side na mey zaman banza tasa yatsa a baki tana jira ya bud'e.
   
    Bece da ita komai ba ya danna key ya bud'e ta shiga shima ya shigan,'kamshin turarenta ne ya soma tashi a cikin motar.Zaman kurame sukai harya soma driving, satar kallonta yayi idanunsa suka sauka kan hannunta daya sha jan fulawa dayai rad'au a farar fatarta.Sosai ya birgeshi amma seyayi 'ko'kari ya basar nan ya maida kallonsa kan titi sede fa ya kasa sharewa,hannunsa d'aya ya kai ya ri'ko hannun nata ya murzawa a tausashe.

    "Gidan Mommy za muje ta 'kosa ta ganki wai".

   Mommy ce da kanta ta kira shi seda tayi masa tsiya wai rowar matar yake wa mutane tunda de Amrah a gaisuwa suka had'u wannan kuwa ba zuwanta bane ,shiko dan kar ta saka wata fita ta biyun yasa ya yanke shawarar kaita yau d'in a de huta.
  
     Jin yace gidan Mommy zasu ta saki murmushi dama bata gaji da yawon ba dan tasan idan ta koma gidan kuma ita data sake wata fitar....

     " Itama kwana biyun zanyi koh?"Ta tambaya cikide tsokana.

    "Wani abune? Duk d'aya walhy meye a ciki idan mun kwana se miyi kwanciyarmu a d'akina that's all ke zaki ji kunya bani ba yarinya abinda zanyi a gidana shi zan gudanar a gudan so what".

    Tsit tayi tana tsuke baki dan ta tsokalo shi daban abin yana cinsa.Yana gaba tana biye dashi a baya suka shiga gidan kamar batasan gidan ba se sunne kai take.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now