Chapter 37

482 46 0
                                    

    
     Rahinatu dama abinda take jira kenan shigowarsu wani marayan kuka ta shiga yi da sauri ta soma zame jikinta,besan lokacin da shima ya mi'ke ba wutar kansa ta d'auke sanda ya lura da yanayin suturar dake jikinta yadda tayi wani squeezing doguwar rigace mey santsi wacce bata kai 'kauri ba kowanne side d'in hannun rigar a yage haka 'kirjin rigar ma da yaga ,yanzu ne ya gane inda ta dosa.

    "Wayyo Auntyta ku taimakeni zey kasheni ...wayyo Allah...." Ta sake rushewa da wani kukan ta cure chan loko tana 'kan'kame jiki.

    Aunty Hannatu ce ta nufi inda take ta sunkuya tana dafe 'yar tata cikeda nuna damuwa take tambayarta meyake faruwa.

    "Shine ...shine ...ina cikin bacci ....y..ya tasheni ....ya...ya .. fara...ta'bani.....y..." Bata 'karasa ba ta fasa wani kukan tana ri'kewa Aunty Hannatu.

     D'akin shiru ba abinda ake ji se sautin kukan Rahinatu,iya abinda Rahinatu ta fad'a kad'ai ma ya isa gamsar da mey sauraro ya fahimci mey hakan yake nufi.

   Mommy dake bakin 'kofa kallo d'aya ta yiwa Rahinatu ta d'auke idonta wani irin sarawa kanta yake mata se d'umin hawaye taji yana zirarowa a kumatunta.Jiri-jirin data fara jine yasa ta dafe jikin 'kofa da hannunta ,da'kyar 'kafarsa take motsi ya soma takawa zuwa inda take bata bari ya 'karaso ba ta bar wajen da sassarfa ta nufi d'akinta su Walida da sai yanzu suka zo suma ganin ko lafiya sanda suka jiyo kukan Rahinatu.Kafin su 'karaso 'kofar d'akin suka ga Mommy da sauri tana wucewa Shettima ya biyo bayanta babu wanda suka iya samun damar tambaya se kallon juna da suke zuciyarsu fal da tambayoyi.

    Da da yadda zeyi ya shiga zuciyarta da qwaqwalwarta dan ya fahimtar da ita da yayi da 'kyar ya ke kiran sunanta dan dakatar da ita yanaso ya fahimtar da ita.

   "Mommy dan ..Allah.." Ya kasa ko 'karasawa.

     'Kofar d'akinta tayi saurin turawa tana so ta shige ya 'kan'kame hannunta da hannu biyu batasan lokacin da ta d'auke shi da mari ba ta wafce hannunta ta fad'a d'aki ta doko 'kofar ta murd'a key bayanta ta jingina jikin 'kofar ta sulale 'kasa tafin hannunta a baki tana toshe kukan daya ke shirin 'kwace mata.

    Karo na farko da ta ta'ba d'ora hannu akansa ta bige shi.Yana tsaye ko motsawa ya kasa yi shi inde dan marine ya be'ki ta yini tana yi ba inde har zata yarda ta saurareshi ya fad'a mata gaskiya ,yau ina zey saka ransa?

     Tunda yake be ta'ba shiga tashin hankali irin wannan ba duk abinda ya faru a baya gwara shi da wannan.

      Suna ganin ficewarsu suka dubi juna suna murmushi hawayen ta ta shiga gogewa zata yi magana suka ga su Wafah sun shigo.

   "Aunty meya faru?" Walida tayi 'ko'karin tambaya.

    "Walida wannan maganar baki baze iya fad'a ba".Ta amsa tana girgiza kai cikeda alhini.

   Jikinsu ne yayi sanyi suna kallon Rahinatu data lafe a jikin babarta."Ko wani abu ya sami ya Rahinatu?" Yanzu wafah ce ta tambaya.

   Daga Rahinatu har Auntyn shiru sukai ba mey amsa su har suka fita.

     Jikin 'kofar ya 'karasa yana sake kiranta bata bari ya soma magana ba tace ya bar mata waje bata son jin maganarsa,zuciyarsa na 'kuna ya koma d'akinsa.Ya dad'e a tsaye ba tare da yasan mey zeyi ba ,wata zuciyar ta shawarce shi daya fice daga gidan ko zey ji nutsuwa.Key d'in motarsa kawai ya d'auka ya sauka 'kasa a parlour ya d'auki wayarsa ya fita be damu da daren daya nisa ba ya fita daga gidan.

     Ko Baba mey gadi yana bacci jin bud'e gate ya tashi sede kafin ya dangana da fita  motar Shettima ta bar gidan.

     Su Walida kansu ne ya sake 'kullewa ganin 'kofar d'akin Mommy a gar'kame sunyi knocking batai magana ba  jin alamar mota ta fita daga gidan suka sake shiga wani tashin hankali an barsu a duhu gashi Mami taje Gombe bare su dangana zuwa d'akinta.Haka suka koma d'akinsu suna ta sa'ke-sa'ke dad'inta su Sa'adatu da Husna basu ko tashi ba.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now