Chapter 5

887 89 0
                                    

Yau ta kama lahadi komai ya had'e ga farincikin murnar dawowar Shettima ga shirye-shirye bikin Anty Mirah.Mommy yau tunda ta farka bata koma bacci ba ta shirya wannan ta shirya wancen ,Mami ma tare akeyi da ita dukda ma yanzu bata fiya yin girkin gidan ba saboda 'yan matan gidan Mommy su take sawa suyi dukda Rahinatu bayi take ba sede a 'kyaleta.

Girke-girke kala daban daban kamar wani taron walima za'ai,d'akinsa kuwa angyara style d'in komai na d'akin Aunty Hannatu se kallo dukda a fili tana nuna frincikinta.

8:00pm Mommy take tsammani jirginsu zey iso shiyasa har 4pm basu tafi airport d'akko shi ba,shikam Appa shiya had'a wannan plan d'in yana so yayi surprising d'in Mommy.

5:35pm Shettima ya iso 'kasa Nigeria shikanshi ya 'kosa yaga 'yan gidansu more especially Mommy.Yata zuba ido ko ze ganta dan yayi tsammanin tare suke da Appa,cikin girmamawa ya gaida Appa sannan Appa ya zagaye hannunsa a bayan d'an nasa.

"Haka d'an nawa ya girma harya kereni tsaho" Appa ya fad'a.

Shettima bece komai ba illa murmushi dayai har ha'kwaransa na bayyana.Yana so ya tambayi Mommy kuma seyai shiru har suka shiga motar Appa.Shettima shikad'ai yasan irin dad'in dayake ji a halin yazu ,shi bama dad'in ACn dake motar yake ji ba yafison iskar waje harwani 'kamshi take masa a hancinsa(Gida dad'i).

Kad'an-kad'an suna hira da Appa hankalinsa ya kasu uku d'aya yana sauraran Appa ,biyu yana tunanin Mommy uku Amrah fatansa Allah yasa tana gidan Mommy he missed her much about 5yrs anya kuwa ba ayau zeje ba?

Ganin gate d'in gidan ya bud'u sun shiga ya dawo da hankalinsa gu d'aya.

Walida ce ta hangi motar Appa ya shigo gidan,itama a tunaninta ko yazo su tafi tare d'akko Shettima.Zaro ido tayi waje ganin 'kofar passenger seat ta bud'u Shettima ya bayyana."Mommy!"Ta 'kwala mata kira.

A guje ta fice daga d'akinta zuwa na Mommy,ta sameta itada Wafah Mommy gama shiryawarta kenan Walida ta shiga.

"Meye kike tsala min kira?"

"Mommy ...." Katse maganar tayi sakamakon idea data fad'o mata.

"Mommy surprise zan miki a parlour miyi sauri ki gani"

"Surprise? Da ba'ai ba se yanzu ?"

"Mommy akan gift da zan bawa Shettynki ne,mije yanzu".Walida tayi saurin ri'ke hannu Mommy siririn d'ankwalin dake kanta ta cire ta d'aura mata a fuska ya rife idanunta biyu.

"Wannan surprise harda maidani makauniya" Cewar Mommy tana murmushi.

"Mije" Tayi sauri-sauri suka bar d'akin Wafah tabi bayansu ba tare da tace komai ba.

Jagora tayi mata har zuwa parlour ta tarar har sun shigo,su Rahinatu suma da suke parlourn se yanzu suka ga shigowarsu,Wafah ta bud'e baki da ido Sa'adatu zatai magana Walida tayi mata alamar shiru.

Appa dariya ya soma mara sauti ashe bashi kad'aine key sonyin surprise ba.Shettima kuwa murmushi ya soma a ransa yana farinciki.

Seda suka zo gab da gab yana facing d 'inta itama ba tare da ta sani ba amma kuma ta soma jin motsin alamar mutum.Hannun Mommy ta ri'ko ta d'ora kan kafad'ar Shettima tana 'kunshe dariya.

Mommy yanzu ta tsaya da murmushin ta kasa fahimtar komai,a hankali ta soma shafa kafad'ar zuwa kai ta sakko fuska d'ayan hannu ta d'ora a fuskar ya zama duka biyun.Kowa yayi 'kuri jira suke suga zata gane ko kuwa.Shikanshi da 'kyar ya ri'ke dariyar da take so ta ku'buce daga bakinsa.

Mommy de tasan duk dawowa hutun da zeyi zeta taroshi a airport amma kuma wannan ...."Shettyna"Ta fad'a a hankali not sure of abinda ta fad'a.

Hannu tasa zata bud'e idonta Walida tayi saurin ri'ke d'aurin,dukansu dariya sukai Shettima ya matsa gefe.Walida!"Mommy ta kirata cautiously.

"Mommy bafa kowa" Wafah ta fad'a tana dariya.

"Ba Shettima bane" Cewar Walida.

"Shettyna " Ta kirasa.

"Uhm Mommy na" Ya amsa.

Wani 'kwallar jin dad'i taji a idanunta dukda a rife yake, da sauri ta zare d'aurin kafin Walida ta sake ri'kewa.

"D'auke min" Ta doke hannunta.

Tana juyowa taga hasken flash "Shetty" Yasa dariya ya maida wayar aljihu."Mommy "Yayi hugging d'inta ,hannunta ta zagaye a bayansa tana murmushi.

" Tunani ya 'kare "Sukaji muryar Aunty Hannatu.

Bayan sunyi breaking hug d'in ya gaisheta fuskarsa d'auke da murmushi, nan ya gaggaisa da sauran 'kannensa daga baya ya shige d'akinsa yayi shower yayi shirinsa cikin white shirt da black jeans bayan ya feshe jikinsa da turare ya sakko 'kasa dede lokacin Mommy ta hawo steps.

" Aiko daman wajenkan na taho"

"Au duboni kika zo yi?"

" Ehyi idan ka kasa shiryawar sena shiryoka"Tayi dariya.

Shima dariyar yayi suka sakko 'kasa tare,dinning suka wuce.Baki ya saki ganin irin jibgin girke-girken dake kan table d'in.

"Mommy wannan fah?"Yayi nuni da table d'in.

" Is yours ,ka za'bi wanda kake so ,da kaina na dafa maka favorite d'inka "Ta nuna mishi potato roll.

" Mommy thank you I can't pay you"

"You deserved it".

Da kanta tayi serving d'inshi ya soma ci,sega su Appa dasu Wafah harma da 'yan d'aya d'akin kamar gaske,nan suma sukai joining dinner d'in.Daya tambayi Aunty Mirah Mommy ta fad'a masa taje gidan gyaran jiki.

★★★

Amrah ta shige 'kuryar d'aki tun d'azu se tunani take kuma be wuce na Shettima ba,daga gefe guda tana so ta ganshi d'ayan 'bangaren kunya takeji." Ko zey zo gobe?"Ta tambayi kanta.

"Bakije masa barka da zuwa ba bacin 'kin d'aga wayarsa da kike taya zezo" Zuciyarta ta amsa.

Haka tai ta sa'ke-sa'kenta,tana jin sanda Ummie tayi waya da mami take ce mata Shettima ya dawo.


Vote, comment and share.lots of love😘

Dijensy❤





TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now