Chapter 52

642 49 1
                                    


     Yaran dr Muhammad a gida suna tashi daga bacci suka ga Daddynsu ya fita ,Nana ce tasa kukan shagawa'ba wai se an kaisu asibiti wajen Daddynsu haka ta cikawa Hajiya tsohuwa kunne kuma ta fita daga d'akin ta'ki ,kamar had'in baki shima Imran yasa kuka Sameera kuwa itama dama so take su fita yawo dan haka ta fita ta samu driver da tun d'azu ya dawo gidan bayan yakai dr.

    'Karya ta kellara masa tace Daddynsu ne zasu fita unguwa yace suzo asibitin su samesa tace idan kuma be yarda ba ya kirasa jin haka shikuwa ya yarda da zancenta ya amince.Ai da sauri suka shirya nan da nan Hajiya se gani tayi sun le'ko yi mata sallama itanma sukai mata 'karya wai Daddynsu ne  yayi wa driver waya yace ya kai asibitin  dama tasan 'ya'yan Daddynsu ne su shiyasa ta yarda tace Allah ya tsare.

    Koda suka isa asibitin basu san ina zasu samesa ba tunda ba permanent office ne dashi ba tunda ba mazaunin nan d'in bane,Sameera da tafisu wayo ita tunda tasan daddyn nata cardiologist ne seta tamvayi inda zata samu 'bangaren a asibitin, bayan sunje haka suka dinga tambayar nurses ina zasu samesa full name na mahifinsu suke fad'a suna tafiya wasu suna kallonsu cikeda sha'awa.

    Wata nurse ce ta fad'a musu yaje duba patient amma su jirasa ,nan ta kaisu office da yake zama temporarily. Ganin su kad'ai ne sukaita ta'be-ta'ben kayan alatun kan table dake office d'in.

   "Ni wlhy na gaji da zama anan"Nana ta fad'a.

   " Nima haka".Cewar Imran.

    "Seku fita". Sameera ta fad'a tana duba wani text book kan table d'in.

    Gatsen datai musu suka d'auka a gaske su biyu sukai ficewarsu,basu san ina zasu ba kuma sashen ba wani hayaniya se mutane ba yawa da suke shige da fice, su kalli wannan su kalli wancen suna tafiyarsu d'akuna-d'akuna sukai ta wucewa ,wani d'aki Nana ta gani 'kofar ba'a rife take ba ta d'an sa'ba nan ta tsaya tana hango mutanen ciki.

    " Daddyyyyy!"Ta kwalla masa kira.

    Ya juya baya amma dukda haka seda ta ganesa ,juyowa yayi yana so yaga wannan wace mey muryar Princess haka.

   Tana ma'kale jikin 'kofar ganinsu Mommy da Aunty Mirah a ciki yasa ta'ki shiga wai ita kunyarsu tasa tafin hannu tana mutstsuka ido d'aya.

   "Princess". Ya kira sunanta.

   Imran ne ya tureta gefe ya shigo " Daddy muna ta nemanka shine ka gudu ka barmu baka tashe mu ba"

   Hannunsa ya d'ora a baki alamar mamakin yaran "Waya kawo ku Imran?" Ya fad'a yana mi'kawa yaron hannu alamar ya 'karaso.

   "Driver ne sister ce ta fad'a masa... " Be 'kare maganar ba Nana ta katsetsa harta manta da kunyar su Mommy da idonsu na kan yaran suna kallonsu cikeda sha'awa.

   "Shhh! Secret ne fa minyi al'kawari baza mu fad'a ma Daddy ba".

    "Daddy patients ne suma?" Imran ya tambaya yana maida kallonsa kansu.

    "Aunties ne, ga brother yana bacci baya son hayaniya pls"

     "Ina wuni". Suka gaishesu a tare.

    " Lafiya lau ".Suka amsa Mommy tana mi'ko mata hannu.

   " Zo mu gaisa".

    Tana no'kewa ta 'karasa wajen Mommy kunga wani murmushin farinciki da Dr yake yi(😂 harya tafi imagination....).

   Kiran daya shigo wayarsa yasa ya fita Imran ya 'karaso inda Aunty Mirah ta nuna masa ya zauna tana tambayarsa school.

    "Ya school?"Mommy ta tambayi Nana.

     " Lafiya lau...Daddy ne yake shirya ni kullum kullum idan bayanan  kuma tsohuwa"

     "A'a ba tsohuwa ba granny  tace mu dena fad'a mata tsohuwa"Imran ya gyara mata.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now