Chapter 60

833 51 6
                                    

    
       Itako ta saki jikinta baccin yayi nisa ,wuyanta ya gyara mata ya sake mata peck a goshi ya rufe idanunsa shima baccin ya kwasheshi.

           ★★★

     Kawu ganin an 'kar'kare biki yasa ya kira Mommy a waya yake fad'a mata fa Hannatu ba lafiya.

    Ashe tun dukan da mahaukaciyar nan tayi mata a asibiti ba'a sani ba ya ta'ba mata liver.Se bayan ya koma dubata likita ya fad'a masa bayan tests da akai mata aka gano hakan ,sosai tausayinta ya kama Mommy kwarai dan haka tace wa Kawu zataje dubata.

     
   Kamal kuwa da kansa ya dawo gida tamkar kurma baya cewa komai ,photo d'insu da akai framing shida ita ya d'akko da mayafinta ya zame masa kamar mirror.Duk sanda Mama  ta shiga d'akin  photon yana hannunsa  sede ta fita daga d'akin cikeda tausayin sa.

      ***

    Bayan sun shafe kusan awa biyu da rabi Amrah ta farka ,jinta a jikinsa yasa ta d'ago idonta ta d'ora a fuskarsa idanunsa a rife da alama har yanzu baccin yake,a hankali ta zame jikinta daga nasa gudun karya farka ,zuciyarta fyas take kallonsa.Ita se yanzu ma ta tuna da wayarta data mance a gida tasha haushi kuwa ,bayi ta fad'a ta wanke fuskarta daga nan ta d'auro alwala ,bakin mirror ta 'karaso ta sake gyara fuskarta sannan ta koma kan couch na d'akin ta zauna tana kalloshi time-time tana d'auke ido karya farka.

     Befi 10min ba wayarsa tayi 'kara wacce ke kan drawer side na gadon.Kallonta ta mayar kan wayar sannan ta dubeshi har yanzu be tashin ba,mi'kewa tayi ta 'karasa wajen.

    "Kashe wayar baki d'aya  mu huta". Taji ya fad'a.

    " Mommy ce fah"Ta fad'a tana kallonsa.

      Murmushi yayi yace "Toh d'aga kiji".

    "Na d'aga fa kace ? Nace mata meh ta tambayeka?"

   "Kice angonki bacci yake yana hutawa". Ya 'kare kamar zeyi dariya.

    " Allah bazan iya ba kunya nake ji".Ta fad'a a shagwa'be.

    Hannu ya mi'ka mata ta mi'ko masa wayar ,bata kawo komai ba a rai ta 'karasa tana mi'ka masa ya had'a da hannunta ya jawota ta fad'o jikinsa.

     "Mey akai da zaki ji kunya  ,yanzu ba lokacin jin kunyar bane se gaba...."

   Wani kiran wayar ne ya shigo karo na biyu ya d'aga idanunsa a kanta daga ta had'a ido dashi seta d'auke.

    "Hello Mommy".

     Nan take fad'a masa driver ze kawo musu abinci base Amrah tayi girki ba.Yana yin sallama da ita yace.

   "Yar gatan Mommy baseta yi girki ba".

     " Muna maganar a ina aka tsaya?"

     "Ya akai kika tashi baki tashen ba nima?"

      "Naga kana bacci".

      " Wow! Bakyaso mijinki ya tashi koh? Ko kuma de kina tunanin wani abu ba"
  
     "Lokacin sallah fa yayi".Ta fad'a tana so ya saketa.

     " Toh madam  na sake ki kije ki alwala kenan"

     "Ai nayi ma kaine zakai"

      "Wai ke mey wayo koh? Hmm" Daga haka ya sauka daga gadon ya fad'a bayi.

      
      Bayan hr d'aya sega driver ya iso da abincinsu.Bayan sun gama cin abincin suna zaune kan sofa a parlour  take fad'a masa ta mance wayarta a gida .

    "Dad'i gidan miji Amrah hadda manta waya saboda zumud'i,ashede.."

    "A'a walhy ba zumud'i nake ba lokacin fa kuka nake"Tayi maganar a shagwa'be.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now