Chapter 35

510 42 0
                                    

        Amrah kamar ta dawo kenan haka take ji gida dad'i,yinin ranar tare da ita aka shiga kitchen dede da minute d'aya bataso tayi waisting ba tare da Ummi a gefenta ba,Ummi tana tambayarta 'yan uwan Kamal mata da suka ta'ba zuwa wajen Ummi, Amrah kawai dai amsawa take amma ita bata ta'ba ganin 'keyarsu ba dan ko maganarsu be ta'ba mata ba be ta'ba gaya mata ma wani abu gameda family d'insa ba ko wad'anda ya turo a matsayin Uncles d'insa bata ta ba sanyasu a ido ba Abba ne de ya sansu tin lokacin biki kenan.A zuciyarta tana ta addu'a Allah yasa ya'ki zuwa d'aukanta tayi kwanciyarta dan idan ta tuna gidansa wani abu takeji ya tokare mata a wuya wata zuciyar ma raya mata take ko kawai ta bijire ta fad'awa iyayenta komai a yita ta 'kare ya bata takardarta.

    Bayan maghrib kad'an suka jiyo sallamar Abba,tana rawar 'kafa ta fito tsakar gida tana gaida Abba sosai yaji dad'in ganin d'iyar tasa ,nan yake fad'a mata ai sun gaisa da Kamal d'in a 'kofar gida.Take yanayinta ya sauya Ummi ta fahimci hakan ,shigewa d'aki tayi tayi li'kwi kamar bata shirin fitowa.

      Ummi bayan ta sallami Abba ta kaimasa abincin dare ta shigo d'akin ta tarar da ita a ja'be.

    "Mey kike jira baki shirin tafiya ba?"

      "Zeyi magana idan zamu tafin fa".

     " Au seya maki magana ma,yanzu idan kinje gida ma mey zaki bashi?"

     "Ai nasan a 'koshe yake ma".

      " Gidanku,maza tashi kice ya shigo"

     "Ummi abincin wai zaki bashi?"

       "Ehyyi mana".

       " Nasan bama ci zeyi ba kada ma ku wahala".

      Ummi ta bud'e baki zata sake magana kira ya shigo wayar Amrah,tana duban wayar taga number sa kamar mara gaskiya ta had'a ido da Ummi ta maze ba tare da ta d'aga wayar ba batasan Ummi ta gane ba."Idan kin d'aga seki ce ya shigo"Tana gama fad'in hakan ta fita kitchen had'o masa abincin.

    Seda tayi tsaki ta d'aga wayar murya a cunkushe wani haushinsa na sake dabaibayeta."Sweetheart sekin sa na cire kunyar na shigo?"

   Wannan sunan dayake kiranta dashi(sweetheart) yafi kowanne 'bata mata rai ita kad'ai tasan mey take ji ,ba tare data tayashi waccen zancen ba tace "Ummi tace ka shigo" Tana kaiwa 'karshe ta katse kiran.

     Tana daga d'aki tajiyo  sanda ya shigo ,a ranta tana fad'in munasari se wani kwantar dakai da biyayya yake wa Ummi kamar mutumin arzi'ki.Bayan sun sake gaggaisawa Ummi ta fice ta bashi waje se shi d'aya,da ace dane baze ci ba amma yanzu dayake jin a ransa komai daya shafeta ya damu dashi yasa ya ci abincin.

     Ko motsinta ba'a ji balle ace tana ciki ,bayan ya 'kare cin abincin yayi sallama dasu Abba harda ajje 'yan salalai da bansan ko nawa bane.Seda Ummi ta sake shiga d'akin ta taso ta.
 
   "Banason sakarci ,sekace idan ance ki zauna d'in iya zama zaki".

   A zuciyarta tace" Wlhy da gudu Ummi".

    Kamar wacca 'kwai ya fashewa a ciki ta yafa gyalenta ta rataya jakarta data zira litattafanta na islamiyya.

     Kwalla ce ta tarar mata fuska a tamke ta fito Ummi ta kula da ita amma tayi kamar bata gani ba ,bayan tayi sallama da Abba tayi sallama da Ummi ta fice.Ko kallon inda yake batai ba ta shige motar dukda kuwa shiya bud'e mata gidan gaban.Tana zaman zamanta yayi mata kustse cikin rayuwa ya rabata da gidansu batada damar zama, babban ciwo ya rabata da aboki masoyi da take ji tamkar jininta,ko karen hauka neh ya cijeta bazata ta'ba son Kamal ba.Ita kad'ai take wannan maganar a ranta.

    Shiru motar ta d'auka kamar ba mutune a motar ,jingina tayi da jikin kujerar tana kallon window kwallar data ma'kale ta ziraro.Lokaci -lokaci yana kallonta sede ya kasa cewa komai saboda wani kwarjini datake masa.A wani bakin store taga yayi parking bata waiwayo ba balle taga lokacin daya fita gashi wuyanta ya 'kage da kallon gefen window shiyasa yana fita ta gyara.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now