Chapter 42

603 46 2
                                    


     Waro ido tayi batasan tana da ragowar 'kwarin jiki ba se lokacin ta mi'ke tashin hankali 'karara ya bayyana a fuskarta tana kallon aika-aikan dayake  shirin yi.

     Allurar ya d'aga ya d'an zubar  da ruwa bubbles ya fice an shigangad'u😱 bata sake rikicewa ba se da taga ya kallota yana takowa inda take murmushin fuskarsa yana sake fad'ad'a.

     "Ummi". Ta furta a 'kasan ma'koshinta tana had'iyar yawu.

     " Baby inaso kiyi bacci allurar zata saka kiyi bacci".

      "Kamal yaushe ka zama doctor ban sani ba?" Ta tambaya bata san wane lokacin ta mi'ke tsaye ba tana ja baya.

     "Don't worry ba zafi I promised bazan miki da zafi ba"

     Hawaye ne suka soma gangaro mata a ido ba shakka Kamal ranta zey rabata dashi shikenan rayuwarta tazo 'karshe.

   "Kamal wlhy 'kalau nake na warke karka min allurar mutuwa dan Allah ka bari na ji muryar Ummi da Abba".

   Gira ya had'e kalamanta na ta'ba ransa taya zeyi mata allurar mutuwa duk wannan son dayake mata.

   " Kin manta ke masoyiya tace? Bazan ta'ba cutar dake ba kuma bazan bari wani ya cutar dake ba".

    "Bacci kawai nakeso kiyi".

     " Zanyi amma ka ajje ka yar da allurar dan Allah ".

    Kallonsa ya mayar kan allurar wani haushin allurar ya kamashi taya zata tsoratar masa da Amrahnsa ,take ya saketa 'kasa yasa 'kafa ya mur'kusheta.

   Da hannu yayi mata alamar an gama da batun allura " Bazaki sake ganinta ba my Amrah Hayati".

    Wayyo sanyi a ranta ba'a misaltawa ,zuciyarta har yanzu bata bar bugawa ba a ra'be ta zauna gefen gadon tana ajiyar zuciya.

    Seda ya tabbata ya d'auke allurar da sauran abu daya shafi allurar ya samu gu ya zauna yana zuba mata ido."Are you ok?"

   Kai ta gid'a magana ma bazata iya ba.
   
    "Bacci fah?"

      "Zanyi...zanyi". Ta fad'a gabad'aya ta gama firgita da lamarinsa tana jin sede a fitar da gawarta daga gidan Kamal.

    Badan taso ba ta lafe a cikin blanket ta rufe ido zuciyarta na lugude tana jin idonsa a kanta yana zaman gadi " Lailaha illa anta subhanaka inni kuntum minazzalimin "Take ta nanatawa a zuciya.

    ____________________

      Yau kwana biyu Rahinatu bata gida Aunty Hannatu hankalinta ya tashi saboda ta kirata bata samunta 'kawayenta data sani ta kira suma sunce bata tare dasu bala'i goma da ashirin ya hauta mukulli da takardu ya gagareta sama ko 'kasa ta rasa yadda zata sami key duk yadda tayi attempting bincike a d'akin Mommy bata samu ba harta gaji har d'akin Shettima dasu Walida ta bincika amma bata samu ba ita kuwa batajin zata bar gidan bata samu abinda take buri ba kud'in cikin ba'kar jaka ta rainasu ko dubasu bayi take ba saboda ta raina yawansu.

     ***

     Ahmad yau kwana uku baya gari yau ya dawo gidan,
tun daga parlour yake ramka sallama amma ba amsawa d'akin dayake tsammanin ganin Shettima ya nufa.A gigice ya 'karasa inda yake 'kasantieg yana ta matagugu helpless, ya rasa ta ina zey soma taimaka nlmasa cikin rikici yake magana" Shettima zaka kashe kanka ne kasan mey kake kuwa? Meyake damunka ban sani ba...haka...innalillahi.."

   Gabad'aya ya diririce ganin halin da Shettima yake ,hannunsa dafe a 'kirjinsa tari kawai yake ba 'ka'k'kautawa ,soyake ya taimaka masa ya tashi su tafi asibiti amma Shettima baida alamar tashi sema matsawa yake baya.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now