Chapter 2

1.4K 110 0
                                    

Kwana biyu Shettima ya murmure ya samu sau'ki har lokacin Amrah bata san da rashin lafiyar ba gashi bata je gidansu ba sede duk tabi ta damu dajin shiru nashi.

Yau de ta 'kulla zuwa gidansu Shettima amma bata fad'awa Ummie ba.Ana fitowa sallahr asr daga Islamiyya bata koma aji ba ta saci jiki ta gudu,duk nisan dayake tsakanin gidansu Amrah da Shettima haka ta saiti hanya tayi ta tafiya abinta a 'kafa ko a jikinta ba ita ta isa ba se 4:22pm.

Lokacin data shiga parlour ba kowa tayi ta sallama shiru dan haka ta wuce d'akin Mami ko zata sameta ciki amma bata nan.Fitowa tayi ta duba kitchen bata sameta ba se abokin fad'a.

"Ina su Mommy ina ta sallama shiru?" Ta tambaya.

"Kice de kinzo gani na ko lafiya"Yana daga kan drawer a zaune yayi maganar hannunsa ri'ke da glass cup yana shan orange juice.

" Chabb a dalilin mey? Waya damu ma".

"Ke mana,bakisan kwana biyu bani da lafiya ba koh"

"Da gaske?" Ta tambaya ganin yanda yayi maganar in serious turn.

"Eh mana ko dubiya" Ya ta'be baki.

"Ayya ai bansani ba ,meya sameka?"

"Wai mura" Ya amsa a tak'aice yana durowa 'kasa,daga gefe guda ya ajje cup d'in.

"Au wai ne ma?"

"Ehman nifa nafi tunanin ciwon so neh"

Amrah a take ta ri'ke baki tana salati ,shiko dariya ya shiga yi tare da fad'in."Kina mamaki ne,kawai de ban fad'a wa Mommy ba amma nasan ba iya mura ke damuna ba"

"Mtwhhhh kai wace zata ma kula ka d'an 'karaminka da kai har nawa kake wlhy baka da kunya".

" Ki tuba yarinya,Baki tambayen wa nake so ba".

D'an gyara tsaiwarta tayi kafin tace "Wa?"

"A makarantar mu take ,ina bala'in sonta amma na kasa fad'a mata shiyasa yanzu zan tambayeki shawara idan namiji yana son mace mey ze fad'a mata?"

Baki ta saki tana kallon yanda ya 'kare maganar"Wayyo Allah Shettima a boarding d'in ka koyo wannan maganganun wlhy sena fad'a wa Mommy".

Bata tsaya wata-wata ba ta 'kwalla murya "Mommy Shettima...." Bata 'kare ba yayi saurin rufe mata baki da tafin hannunsa .

"Ke dalla wacce ba'a iya sirri da ita ba Mommy zaki fad'a wa wannnan maganar mtchww toh 'karya nake ma" Ya sauke hannunsa bayan ya 'kare maganar.

"Ba wani tsoro kaji,badan halinka ba amma ka sake maganar soyayya sena fad'a mata bakasan kai yaro bane?"

"Nida ke waya girmi wani?"

"Kai mana amma de ai har yanzu kai yaro ne"

Kafad'a ya d'age "Toh seyaushe zan fara yi?"

"Mey?" Ta tambaya.

"Ita soyayyar mana".

Seda ta d'an harareshi sannan tace" Se bayan nayi aure ma tukun"Tana gama fad'ar haka tabar kitchen d'in tana dariya ta rife bakinta da hannunta.

Ya zama speechless ma banda murmushi daya shiga yi."Se kinyi aure"Ya maimaita maganar a fili.

Aunty Hannatu data shigo kitchen d'in yasa tunaninsa ya katse ,kallo d'aya yai mata ya fita daga kitchen d'in.Koda ya fito parlour be ganta ba dan haka ya wuce d'akin Mami.

★★★

1hr earlier

Mommy ce zaune kan gadonta a yayinda Aunty hannatu ke zaune kan couch d'in d'akin. "Mommy Allah inde ze zamo kin shiga damuwa gameda tafiyar Shettynki a ha'kura da tafiya nesan,dama na bada shawarar ne domin inganta zamantakewarsa da jama'a neh". Aunty Hannatu ta fad'a fuskarta a sake.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now