Chapter 14

739 58 0
                                    

 
  ~~~

     Amrah al'amarin Barr Kamal ya soma damunta,ba dama  wayarta tayi 15min a hannu ba tare da kira ko text nashi ba, wani lokacin ma suna waya da Shettima zata ga kiransa yana shigowa.Ga sa'konninsa barkatai wani lokacin ma tsoro yake bata da kalamansa,wani lokacin idan ta fita Ummie ta aiketa seta ganshi a 'kofar gida sede ta komo gida.

     Yau ma wani sa'kon ne ya shigo;_Rashin kar'bar soyayyata babban illace garemu baki d'aya,da kinsan irin yadda zuciyata take sonki da baki 'ki amince min ba.Amrah bazan ta'ba rayuwa ba seda ke,qaunarki nake ba 'kiyayya ba ya kamata kiyi adalci kada ki jefa bawan Allah cikin wani hali...Barr Kamal love you_"
      

       Kalmar 'adalaci' ita ta tsaya mata a rai."Mey yake nufi da hakan?" Tunani ta Shiga yi kota fad'a a gida amma kuma wata zuciyar ta haneta dan haka ta goge dan bata ta'ba barin messages d'insa a wayarta.

       ***
 
       Yana daf da shigowa layinsu ya hangi mota dake parke daga farkon layi kafin a 'karasa gidansu,ba sau d'aya ba ba sau biyu ba yasha ganinta an sauketa a motar kawai bede ta'ba tambayarta bane.

    Rahinatu tana fitowa tayi waving bye wa mai tu'kin bata kula da Shettima ba ta 'karasa gida.Yana yin parking motarsa ya shiga gida da sauri-sauri yake tafiyar yarda ze isketa.

      Bata 'karasa hawa upstairs ba ya tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta,seda tayi rolling eyes sannan ta juyo."Waye wannan d'in?"Ya tambayeta fuskarsa a tamke.

    Cuno baki tayi ta soma 'kun'kuni a ciki-ciki"Wanine".Ta amsa a takaice tana kallon gefe harda kama 'kugu.

    "Wanin bashida suna kuma meye had'inki dashi da zeke d'akko ki daga wani gun yana ajje ki?"

      "Gidanmu fa ya kawoni ba wani waje ba kuma ma...idan saurayinka ya d'aukeka a motarsa wani abune..." Ta 'kare maganar 'kasa-'kasa tana hararar 'kasan ido.

    "Naji saurayinki neh amma ha'kkinsa ne ya dinga kaiki unguwa? Kokuwa a gidanku bakuda motar da za'a kaiki?"

    "Ni..fa ba..yarinya..bace ,kuma mutum ma shi wayasan..meya je yayi a 'kasar wajen inda ba uwa.. ba uba.." Ciki-ciki tayi maganar amma karaf a kunnensa aiko be 'bata ko seconds ba ya make bakinta.Tsabar azaba har du'kawa tayi tana dafe bene.

     Sotake tace Allah ya isa amma tana gudun abinda zey biyo baya ,da sauri-sauri ta haye bata tsaya a ko'ina ba se d'akin Aunty.

    Shettima da ransa ya gama 'baci cikin zafin rai ya wuce d'akinsa ya rufo.

    "Mey ne haka?" Aunty ta fad'a ganin Rahinatu ta fad'o jikinta tana kuka.

    "Dukana yayi" Ta fad'a cikin kuka.

      "Shi wa d'in?"

         "Shettima"

         Ta d'ago da fuskarta Aunty ta kalli bakinta taga ya d'an fashe ta gefe.

     "Dole ya dake ki tunda ya gani ana yi a gidansu ,idan beyi halin ubansa ba ai banace d'ansa bane"

     Rahinatu da bata gane mey babarta ke fad'a ba ta kalleta cikeda rashin fahimta tana share hawaye.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now