Chapter 24

561 43 0
                                    

   
       "Ki amsa mini?"

         A fusace ya daki bayan kujerar da hannunsa har cikin ranta amma ta'ki bud'e ido.

    Matsawa baya yayi ya maida kallonsa kan wayar wani abun haushi seda ya sake typing password d'in tunda wayar ta sake shiga security,a 'kuntace ya rubata Shettima ta bud'u nan ya shiga message.

    Ba adadi abinda yake tsammamin shi idanunsa suka gano masa ,messages ba adadi kamar an tilasta masa bud'ewa the more yana dubawa the more zuciyarsa na tafasa komawa yayi sent messages nan yaga itama text iri-iri Allah yasa ta goge wanda ta tura wa Shettima a daren jiyan.

   

     Jin alamar ta dena jin d'uminsa ta bud'e ido tana kalloshi ta mirror yana duban wayar yana fad'in " Huhnn Juliet lover girl, Romeo and Juliet... "

  
      Kamar 'kiftawar ido taga ya maka wayar jikin bango har ido ta rintse ,nan take wayar ta tarwatse kamanninta suka sauya tayi pieces.

    Zuciyarsa a 'kufule da 'kunci ya fice daga d'akin.

 

    A hanki tabi wayar da kallo qunar dake zuciyarta bawai kan wayar yake ba dukda de tasan akwai lokacin bu'katar hakan.Anya kuwa rayuwa zata yiwu a haka? Duk yadda take tunaninsa ya wuce hakan ta rasa gane so ne ko 'ki? Inde yana 'kinta meye zesa ya dinga kishi inde abinda ya akaita a yanzun kishine ya tunzurashi,a tunaninta idan kana son mutum bazaka cutar dashi ba.

      Mi'kewa tayi daga kan kujerar ta 'karasa inda pieces d'in wayar yake ta tsuguna a gun ,hannu tasa ta soma hahhad'a wayar d'ayan-bayan d'aya screen d'in yayi scratch yafi a 'kir'ka.Sanda ta kunna ta kawo amma data tapping screen d'in ta'ki dannuwa tayi iya naci amma ta'ki.Tsintar kanta tayi hawaye na kwaranyo a kumatunta.

    A d'ur'kushe ya tarar da ita lokacin da ya shigo d'akin ta fad'a cikin tunani batasan ma ya shigo ba.Takawa yayi har inda take beyi tsammanin zata nufi inda wayar take ba balle harta d'auka.

    Da 'karfi ya cakumo hannuta ya fisge wayar tare da d'ago da ita ya juyo da ita tana facing d'insa amma bata bari sun had'a ido ba illa hawaye da take tsiyayarwa.

     "Bazaki sake ganin wannan abar ba,Amrah kinshiga cikin sabuwar rayuwa rayuwarki tasha banban data baya kisa wannan a ranki".

    Yana gama fad'in haka ya saketa,sim card d'in ya cire harma da memory d'in ya nufi toilet yayi flushing d'insu.

  Bayan ya fito ya fita minti 'kalilan ya dawo d'akin ba wayar a hannunsa shikad'ai yasan inda ya kaita.Wani abu daya bawa Amrah mamaki yanzu yanayin fuskarsa ya sauya ba kamar d'azu ba ,yanzu  ba wannan shan kunun kamar d'azu daya harzu'ka ,innocent face ce 'karara a fuskarsa.

    " Amrah wife ,mije na nuna miki bedroom d'inki kinga seki sauya kayan jikinki koh?"

    Dayake ba chanja kayan ne a ranta ba shiyasa bata bujuro da tunanin inda kayan yake ba.

     "'Karasawa yayi ya kamo hannunta a tausashe yace mije. Zuciyarta fal da tunaninnika ba tare da tace 'kala ba ya jata suka fita daga d'akin parlour ta iske wacce take d'auke da sofa lemon green da adon milk haka labilen d'akin ma se sauran kayan TV da flower vase da sauran frame manne a jikin bango,wani corridor suka nufa wanda  ke d'auke da 'kofa biyu a right da left side,wance take hannun daman taga sun shiga.

     Furnitures d'in  irin na wancen d'akin sede sun babbanta ta launi shi wancen milk colour wannan ko sky blue ne da fari.

    Da kanshi ya bud'e wardrobe d'in nan taga jerin kayanta tsaf ,tundaga kan set na farko yake binsu da yatsa har zuwa 'kasa alamar za'bowa yake son yi se a karo na biyu ya sake maimaita hakan ya tsayar da yatsansa kan wani ash d'in swiss lace mey torches pink.Hannu yasa ya zaro ya ajje kan gadon yana sakin murmushi " Wow kinga minyi anko ba"

TAGAYYARA(Complete)जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें