Chapter 48

614 43 0
                                    

     *_Finally! Princess ta iso,baby girl welcome to the world. Allah ya raya mana ke tafarkin addinin musulinci (Ameen)😘😘😍_*

        A wahalce ya sakar mata murmushi ba damar magana saboda tube dake mounted a bakinsa😩

    "Shettyna ka tashi".

      " Sannu koh"Ta sake fad'a.

    Kai kawai ya gid'a mata yana kallonta da guntun murmushi a fuskarsa.Duk yadda takai ga ri'ke hawayen da ke shirin zubo mata ta kasa.Turo 'kofar da akai yasata d'ago kai ,doctor ta gani  tsaye a bakin 'kofar.

   Kafin ta goge hawayen data wanke fuskarta tuni ya gani,kallonta kawai yake yana tuna lokacin da tayi kuka a office d'insa. Wannan kuka nata yana masa tasiri a zuciya ,yana ji kamar yace ta dena (Toh mey kake tsoro doctor no name??)

    Jikin gadon ya 'karaso bayan yayi sallama amsawa ta gagareta saboda rawar murya."Glad you're awake"Ya furta yana duban Shettima kafin ya maida kansa kan life support machine d'in yana duban yanda numbers d'in ke reading.

    Bugun zuciyarsa ya sake aunawa kafin ya ciro wayarsa a aljihu ya kira nurse. Mommy na ganin nurse d'in ta shigo ta zame jiki ta fita daga d'akin saboda basu waje su gudanar da aikinsu dan taga da alamar tube d'in dake connected da life support machine d'in zasu cire masa ita kuma tausayi.

   Bayan kamar 15min taga wani nurse d'in yazo ya wuce cikin d'akin da gadon da ake d'ora patient a take ta tsure da tana zaune kan bench amma yanzu ta mi'ke tsaye tana safa da marwa.Kofar d'akin ce ta sake bud'uwa sega nurse biyun sun fito da Shettima  kan gadon da nurse d'in ya shiga dashi. Bata samu ganin fuskarsa ba  suka wuce dashi balle  ta tantance idonsa biyu,ganin doctor ya fito tayi saurin 'karasa wajensa wani sabon hawayen na gangaro mata.

    "Doctor mey kuma ya sake saminsa?"Tayi maganar murya na rawa.
  
     Murmushi yayi wanda be shirya masa ba kafin yace." Bafa wani abu ya samu sau'ki ne room za'a chanja mishi ne ,relax ple..ase" Please d'in 'kasa-'kasa ya fad'e ta.

    Se yanzu ta soma jin nutsuwa sanyin relief yana ratsa ta.

    "D'an babyn naki ya farka instead naga kina murna senaga opposite of it...ya akai haka?"

    Kunya duk tabi ta isheta watoh ya gano kukanta d'azu ,sunan babyn daya la'kanta wa Shettiman ma ya so bata dariya.(Mommy is blushing... hot..hot ..hot🔥🙊).

     D'an gyara murya yayi yace "Mije na nuna maki room d'in nashi" Yayi maganar ne yana nuna hanyar da hannu.

   Kai kawai tayi nodding yayi gaba tana biye a baya har suka 'karasa d'akin ,farinciki ya mamayeta musamman yanda taga yanzun bawai a kwance yake ba duka a'a yana jingine da pillow a bayansa yadda kwanciyar zatai  masa sau'ki gashi ba wata na'kura da aka ma'kala masa drip kawai aka saka masa.D'akin kam ya banbanta da wancen har yama fi girma babu wani na'urorin tashin hankali  kamar wancen.

      "Mommy" Ya kira sunan ta a hankali.

       "Ya jikin naka da sau'ki koh?"

      "Uhm" Ya fad'a yana gid'a kai.

      "Alhamdulillah" Ta furta.

       Mommy ta mance da wani doctor dake tsaye a gefen d'an space  dayai ragowa ta zauna. Doctor se kallo ba shakka akwai sha'kuwa mey 'karfi tsakaninta da d'anta,birgeshi  komai nasu yake kamar TV haka ya zuba musu ido.

       "Kana jin yunwa?"Ta tambaya cikeda kulawa.

       Kai ya girgiza alamar a'a (Yes,saboda anyi masa allurar da zata hana yaji yunwa a drip).

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now