Chapter 29

547 50 2
                                    


    Kwata-kwata ta kasa sakewa a table d'in musamman daya zama opposite da ita yake zaune gashi idonsa na kanta time- time.

    Kamar ba yason cin abincin a wani wula'kance yake ci se wasa da spoon d'in yake."Baki ce komai ba kuma na tabbata kin samu labari"Yayi maganar yana kallon spoon dake hannunsa.

    Shiru tayi dan bata gane zancen nasa ba ta cigaba da sipping tea d'inta.

   Idonsa ya mayar kanta yaga ita abincinta ma take ci lokaci guda ransa ya 'baci cokalin dake hannunsa ya matse tamkar yana huce haushinsa a kai ,zuciyarsa se tafarfasa take, take idanunsa suka yi jazir.

   Jin kamar ya tsaya da wasa da cokalin a plate yasa ta d'ago idonta sukai ido hud'u.Da sauri ta sunkui da kai tsoro ya hanata ko motsa spoon d'in hannunta wani abu daya sake bata tsoro shinen yadda ya matse spoon d'in hannunsa kamar zey 'balla danma na 'karfe ne.

    "Na cika miki burinki  mey kikace akai?"

     Se yanzu ta fahimci inda ya dosa,cikin sanyin murya tace."A tunani na baka bu'katar na sake magana a kansa".

    Yanayin yadda tayi maganar yasa ya kasa sake wata maganar cokalin dake hannunsa ya sakeshi kan plate yayi 'yar 'kara ,tashi yayi yabar wajen yayi d'akinsa tabisa da kallo ta sake kallon plate d'in tana nazarin abinda yayi niyyar yi ,da wata'kila ko cokalin zey buga mata.

    Dama ta soma 'koshi da abincin dan haka ta mi'ke ta tattare kwanukan ta d'auraye,gyara gidan ta shiga yi a tsanake ko ina yayi fyass ta kunna turaren wuta ya gauraye gidan da d'akinta ,'kofar dake opposite da d'akinta ta kalla ,bata ta'ba ganinta a bud'e ba koyaushe a rufe batasan ya tsarin d'akin yake ba batasan ko na miye ba dan shima bata ta'ba gani ya shiga ba.

    D'akinta ta koma ta zauna ta cigaba da aikin tunanin duniya.

      ____________________

    Kwana yayi be runtsa ba yana zaune a tile ko kan gadon be koma ya zauna ba,da 'kyar ya lalla'ba ya fita masallaci yayi sallah ya koma d'aki.Yanzu kan gadon ya kwanta yanaso ya tursasawa kansa bacci gam ya rife ido zuciyarsa na masa suya.Ya juya can ya mirgina can bacci ya'ki idanunsa ,tunaninta ya'ki gushewa a cikin kansa ,haushin kansa ne ya kamasa na ganin ya kasa tsaida kansa daga tunaninta.Kofa da aka turo ce yasa ya juyo ,Mommy ce tsaye a bakin 'kofar sam batai zaton ganinsa ido biyu ba a wannan lokacin.

    "Harka tashi?" Ta tambaya tana tsayen.

     "Uhmm banajin bacci". Ya amsa da 'kyar.

     Murmushi ta sakar masa har yanzu tana jin tausayin d'an nata musamman idan ta tuna maganar auren Amrah da batajin zata iya tunkararsa tayi masa bayani.

    A hankali ta 'karaso ciki bayan ta jawo 'kofar ta rufe.A gefen gadon ta zauna shikuma ya mu'ke zaune.

    " Mommy ina kwana".

    "Lafiya lau Shettima ka tashi lafiya?"

     "Lafiya Mommy karki damu I'm ok".Ya 'kalo murmushi.

    " Haka nake so,mey kake so kaci?"

    "Komai da kika za'bamin" Ya amsa.

     "Ok ,amma da ka kwanta ka sake hutawa kafin anjima".

    " Toh Mommy".

     Hannu tasa ta shafo gefen fuskarshi tana murmushi qwalla tana so ta tarar mata,da 'kyar ta had'iye tace"Ko mey ze faru ina tare da kai Shettima kada wata damuwa ta zame maka ciwo alhali ina kusa da kai".

    Kai kawai ya gid'a yana murmushin 'karfin hali shi kad'ai yasan mey yake ji a ransa.Bayan ta fito ya tashi daga gadon  ya d'akko laptop d'insa ,wani abin takaici password na jiki ma Amrah ganin haka ya fasa ta'ba laptop d'in ya rifeta ma.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now