Chapter 16

664 53 0
                                    

    
       Gidan ya d'au shiru kowa jugum - jugum 'yan tsirarin mata na 'kus-'kus,wasu suna tattaunawa akan sanadiyar mutuwar Appa wai yasha poison da kansa.

       Yau kwana biyu  kenan da rasuwar,duka iyalan nasa suna parlourn ba'ki Mommy na zaune gefe guda kan carpet na d'akin gefenta sister d'inta,zuwa yanzu ba kukan sede tsantsan damuwa dake bayyane a fuskarta a kwana biyunnan tayi mugun ramewa a haka har ruwa aka 'kara mata bayan suman datai.Aunty Hannatu ma idanuwanta sun kumbura tana daga gefe guda Rahinatu na gefenta dasu sa'adatu su Walida ma suna parlourn kowa ka kallesa seka tausaya masa.

       Shettima dake a premises na gidan a rumfa tare dasu Kawu se amsa gaisuwa suke,da'kyar yake amsawa dan tsabar rashin 'kwarin jiki rabonshi daya sa abinci a baki baze sheda ba.

      Amrah da'kyar ta iya tunkararsa tayi masa gaisuwa ko bari taga fuskarsa ta'ki yi saboda tausayi,tana gama barin inda yake ta shige d'akinsu Walida tayi ta kuka tana ji dama zata iya cire masa damuwarsa.

    --------------------

      A yanzun ma Amrah tana d'akin Mami ba abinda take se tunanin Shettima tana tambayar kanta koya ci abinci?

    Qlin! Sa'ko ya shigo wayarta.

     Nasan a halin yanzu kina cikin damuwa domin kuwa damuwar abokinki ta shafeki,Allah yaji'kan mahaifinsa.Yakamata ki shawarci abokinki ya koyi jure damuwa yayi min kalar tausayi ta wani 'bangaren ya ban haushi domin ya bada maza.Allah ya bani sa'a na had'u dake a gidannan da nafi kowa jin dad'i.Barr Kamal.

     Mamaki ne ya kama Amrah she can't believe it yana cikin gidannan.Taya ma ya sani? Shine abin tambayar.

     A sanyaye ta tashi ta gyara fuskar hijab d'inta ta fito ,kitchen ta nufa kamar wasa ta d'an le'ka window dan tanan ma zaka iya hango maza dake premises a rumfa.

    Wani irin fad'uwar gaba taji ganin Barr Kamal zaune gefen Shettima,saurin kauda kai tayi dukda tasan su ba hangota zasi ba itace kad'ai zata iya ganinsu.

      Tafin hannu ta d'ora a baki tana mamakin wannan mutumin.Wani sashen na zuciyarta ne yake fad'a mata "Kila yasan shi"

    Dukda haka de bata gama yarda da batun ba sad'af -sad'af ta koma inda ta fito.

    ~15min later~
  
      "Muddin kina gidannan bazan d'auke 'kafa daga zuwa ba ,mey nema baya fishi,I love you".

      Gefe guda ta ajje wayar wayar ta dafe goshi halin Barr yana bata tsoro.Ganin ta kasa dena tunani yasa ta fita zuwa wajensu Ummie a parlour.

        ----------------

     Zuwan 'kawar Aunty Hannatu, Furera yasa ta tashi daga parlourn. D'akinta ta wuce da ita tana biye a bayanta se d'an bigin hannunta take kamar rad'a-rad'a take cewa"Ya ake cik.."

    "Kiyi shiru mana mu 'karasa d'akin" Aunty tayi maganar 'kasa-'kasa.

    Key tasa a 'kofar kafin su samu gu su zauna.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now