Chapter 8

864 68 1
                                    

Larkhi aur Dijensy is all my name,don't get so confused, on WhatsApp I'm larkhi but on whattpad I'm known as dijensy, you can choosed what you wish to call me with.

***

Aunty Hannatu nan take ta hau hura hanci tana masifa"Dan tsabar wula'kanci ya tunzura shine har a gaban idon mu se'an nuna mana banbanci da wula'kanci,yadda Mansur yake ubanshi kema ubanki ne wlhy bazan yarda a cigaba da wannan abin ba ha'kurina ya 'kare".

"Aunty mije ki fad'a" Cewar Rahinatu tana share hawaye.

"Sannu sarauniyar wawaye,yanzun kike tunanin naje cikinsu ina banbami kamar sabuwar mahaukaciya?"

"Toh meye".

" Sakarya,abinda na hango bazaki ta'ba ba yanzu koma can kije ki masa murna wawiya"

"Murna?" Ta buga 'kafa tana cuno baki.

"Eh murna kuma in kinga dama ki tafi a haka da wannan fuskar shanun".

Sedatayi fari da ido kamar harara tukun ta fita daga d'akin ba tare da tasan mey Auntyn ke shiryawa ba.

Aunty tana ganin Rahinatu ta fita tace" Wlhy zakui da kunsani daga ke har d'an naki sena wula'kanta rayuwarku na TAGAYYARA d'anki ,lokacin zaku gane kuskurenku"Tayi maganar a fili fuskarta ba alamar fara'a ko kad'an sai tsantsar mugun nufi.Bata jima a d'akin ba ta suri d'ankwalinta ta fito waje.

Nanta tarar dasu suna ta raha abinsu Rahinatu tana cikinsu se ya'ke take Wafah tana d'aukansu pic jikin motar lokacin Appa ya koma cikin gidan haka Mommy ma bata wajen.A hankali ta 'karasa wajen tayi 'ko'karin bayyana murmushi a fuskarta.

"Rangad'id'i Shettyn Mommy yayi sabuwar Amarya,idona har wani walwali yake dan tsabar ganin wannan carkad'ed'iyar motar gaskiya nayi maka murna matu'ka Appa ya gwangwaje yaron shi".

" Allah yasa albarka yasa rai aka yiwa"Ta d'ora akai.

Shettima fuskarsa fal da farinciki ya amsa da "Ameen" sannan ya gode mata.

Ta d'an tsaya kakkallar motar kafin ta koma ciki,hannun Hussy taja wai su tafi itako ta'ki,tana ji tana kallo yarinyar ta koma cikinsu Walida wani 'kulewar ba'kin ciki ya sake sokarta dan yadda taga yaran a koyaushe sake sha'kuwa sike da yayyinsu Sa'adatu da Hussy tamkar 'ya'yan d'akin Mommy.

Ita kad'ai ta komo parlour har wani sarawa kanta yake mata saboda zallar ba'kinciki, kitchen ta daure ta nufa kafin takai ga kitchen d'in ta hangi Mommy a dinning area tana tsaye a kusada table d'in Appa yana zaune kujera tana serving d'insa abinci,dukansu murmushi ne bayyananne a fuskarsa se hira suke hankali kwance.Aunty Hannatu daba jiyo mey sike cewa take ba se gwalalo ido take tana ji kamar taje ta sha'ke Mommy ta huta da takaici.A duniya Mommy tana rud'ata inde wajen kula da maigida neh bama shi kad'ai ba ,ita haka take ta iya mu'amala da mutane shiyasa take da farin jinin jama'a kowa yafi saninta akan ita Aunty Hannatu.

Ba kasafai take ganin dariyar Appa ba sede idan yana hira da Mommy ko su Shettima amma bade ita ba ,itada koyaushe se ba'kar magana.

D'akinta ta wuce yadda take taka steps d'in benen kamar shiyai mata laifi😂 da karfi ta bugo 'kofarta."Wlhy wlhy sesinyi nadama a rayuwarsu"Kai kawai take kad'awa tana cije le'be kamar zata jiwa kanta ciwo daga baya ta d'auki pillow ta yatsar a 'kasa ta zauna kan gadon ta soma tsiyayar hawaye mey d'acin gaske.(Allah kayi mana tsari da mahassada,'boyayyu da bayyanannu).

***

Aunty Hannatu haka tasha ba'kin cikinta a d'aki ba tare da kowa ya sani ba face Rahinatu itama da ta shiga d'akin bawa uwar tata ha'kuri korarta tayi.

A haka kwanan Mommy ya 'kare aka zagayo na Aunty dama ta gama target d'inta jiran dawowar Appa gida take.

9:16pm ya shigo gida bayan yaci abinci ya tsaya kallon news kusan na 15minute a parlournsa kafin ya komo d'aki, gimbiyar tana shingid'e tun bayan data kaimasa abinci parlounsa ta koma d'aki dama wani sa'in yakanci abinci a parlournsa maimakon dinning.

Tun daga take-takenta yasan akwai dalili dan yaga yanayinta kwana biyu,yayi sallama yanzu ko amsawa batai ba.

"Bakiji nayi sallama bane?" Ya tambaya yana ajje laptop d'insa a kan drawer.

"Ina bora zatai magana ace tayi laifi ai gara na tsuke baki yafi min rufin asiri karna janyowa 'ya'yan bora su rasa uwar borori a gidan mahaifin Yarima d'an mowa". Tayi maganar har lokacin bata mi'ke zaune ba se karkad'a 'kafa d'aye take.

Jin irin wannan maganganun kamar ruwa a bakinta yasa ya jinjina kai,bece komai ba ya 'kwa'be rigarsa yabar yasa data shafal d'in shirt d'in.Komowa yayi gefen gado ya zauna wayarsa dake kan drawer ya d'auko yana dannawa.

'Kwafa tayi ganin ya d'auki waya,mi'kewa tayi daga shingid'ar ta zauna da 'kyau.

" Yanzu ka yadda da abinda na fad'a ka tabbatar min da shakko na koh?".

"'Kwarai da gaske" Ya jinjina kai.

"Yayi kyau amma ka sani se Allah ya tambayeka ,domin wannan abin da kake zalinci ne tsagwaro".

Banza yayi mata ya cigaba da danna wayar dukda ba abu yake mey amfani ba dan maganarta ta tsaye masa " Zalinci".

Tashi tayi daga gadon ta tako side d'insa kamar 'kiftawar ido ta fizge wayar"Kayi min bayanin matsayina a gurinka baze yiwu tsanar da kake mini ta shafi yarana ba".

"Ina ma kin iya biyayya kamar sauran mata nagari da kinsamu anji mey ke tafe dake,matsa min" Ya amshe wayarsa ya bar d'akin.

Dukda bakin cikin data 'kunsa be hana ta'ki binsa parlournsa ba ,shan gabansa tayi ta na huci."Yau dole ka fad'a min dalilin dayasa kafi fifita waccen yaron akan Rahinatu, itama ai ta iya motar kuma takai munzalin da zata ri'ke".

"Sa'anki ne shi yaron da kike magana akai?" Ya tambayeta rai a 'bace.

"Sa'an 'yata ne ..." Be barta ta 'karasa ba ya katseta da"Toh ki barta tazo ta fad'a min da bakinta na zalinceta kinga sena san kuma abinyi".

"Shi wancen d'in da kansa yake fad'a ai masa ? Ai uwarsa ce take tambayar masa".Ta fad'a tana kama 'kugu.

" Kinyi kuskeren za'barwa kanki irin wannan rayuwar ta ba'kin tunani ita kanta yarinyar da kike tsaya mata batada tunaninnan da kanta tazo yiwa yayanta murna ta tayashi farinciki saboda ba irin zuciyarki ce da ita ba,kisani kinwa kanki dan wlhy da niyyata na sake muku mota ku biyun amma tasha ruwa sede kiga anayi tunda kin iya tsayawa a gabana ki fisgen waya kina min ihu aka gobe se duka ai koh? yanzu kin soma fin 'karfina,kiyi barci mey kyau sarauniyar hankali"Yana gama fad'in haka ya fita ya barta speechless.

A zuciyarta take fad'in "Wannan wane irin mutum ne?"

Da tasan yana shirin sake musu mota da batai haka ba amma yanzu ta makara,bata ta'ba tunanin haka plan d'in ta zey ruguje ba a tunaninta zata d'aga masa hankali itama a sayawa Rahinatu, tana zaune dashi amma haryanzu bata gama karantar halinsa ba.Uta kad'ai take maganarta a zuciyarta.

★★★

10:20pm,Amrah harta yi shirin bacci taji 'karar message wayar na daga gefenta kamar bazata duba ba kuma ta d'akko tana dubawa.


E

very night I ask Allah to give you a bright and happy sleep, and a good morning. Every day I thank him for having you in my life. Sweet dreams, your highness. I hope that my prayers will reach your heart and you will feel the strength of my it.Goodnight "

Take ta hau blushing kamar karatu tayi ta maimata karanta text d'in haka kawai ta tsinci kanta dayin reply.

"Goodnight". Tayi sending tana tsoron Allah yasa baze kira ba idan yagani.

Shettima kwata-kwata be kawo zatai masa reply ba amma segashi,tunani yayi ko ya kirata se kuma yaga dare yayi gashi ba lalle ma ta d'aga ba,a zuciyarsa yana fad'in " So,magana ce bata so".yana kallon reply d'in nata yana murmushi.

I'm sick lalla'bawa kawai nayi nai typing. Lot's of love😘

Dijensy❤





TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now