Chapter 45

656 48 0
                                    

      _Juma'at Kareem_

*Ignore all errors*
          ~~~

       Jikinta na rawa ta waiwayo hannunta biyu data ri'ke wayar kansu rawa suke kamar zata yarda ita a 'kasa gumi ya tsatstsafo a goshinta kamar tana cikin oven.Tunda take bata ta'ba jin tsoron Kamal ba irin yau,da'kyar numfashinta ke fita.

      Har yanzu hannunsa ri'ke da wu'kar tazarar dake tsakaninsu befi taku biyar ba.

    "Amrah meyasa kike gujemin? Nayi laifi neh?

    Ganin ya soma takowa zuwa inda take tsayen ta ingiza baya a ri'kice taji ta jingina da 'kofar bayi,da hannunta d'aya ta soma lalubar handle.Tana jiyoshi kuwa ta murd'a 'kofar ta bud'u da baya ta shige bathroom d'in kamar zata fad'i cikin zafin nama ta rufo 'kofar kafin ya cimmata ta gar'kama key.

    Dukda tasa key hankalinta be kwanta ba zuciyarta kamar zata fito ta jingina da 'kofar ,idanuwanta ne suka sauka kan wayarta data yar a bayin bata ma sani ba.A gaggauce ta d'auka ta soma lalubar number Ummi ,tana samu kuwa tayi dialing.

    _Your account is too low....." Bata gama saurara ba ta katse wayar sababbin hawaye na gangarowa a kumatunta ko tsaiwar ma ta kasa se sulalewa tayi 'kasa tayi zaman dirshan.

     "Amrah Hayati" Taji ya kira sunanta murya 'kasa-'kasa.

     Cikin firgici tayi saurin tashi daga jikin 'kofar dan jitake tamkar a cikin bayin ya kira sunan.Yana tsaye jikin 'kofar shiyasa taji kamar a cikin bayin yake.

    "Please karki gujeni ,ke kad'ai nake da ita banida kowa bayan ke nasan kina sona Amrah please don't leave bazan iya rayuwa babu ke ba"

    Kunnenta ta toshe da tafin hannunta bata ko son sauraran muryarsa.

         ___________________

    
        Aunty Mirah data kwana tare da Husna tun sassafe ta fara shiryawa dan ko bacci komawa batai ba ta 'kagu ta ganta a asibitin,gashi Mommy bata tafi da wayarta ba balle ta kirawo.

    'Karfe 7:20am ta sakko 'kasa a parlour ta tarar da Walida da Wafahn 'kasa-'kasa suke magana wanda be wuce akan su Hannatu ba da Rahinatu.

    "Kun tashi kenan"
  
     "Ina kwana Aunty"Suka fad'a a tare.

      " Lafiya  lau". ta amsa tare da zama kan d'aya daga cikin sofar.

     "Wai kuwa banga Mamin Amrah ba"

       "Ai tunda Ya Shetty ya tafi itama ta bar gidannan tace se idan Mommy ta dawo dashi"Cewar Walida.

    " Toh amma yanzu kuwa ai ya kamata a sanar mata abinda ya faru"

      "Eh Aunty nima wlhy so nake ta dawo zaman gidannan baze mana dad'i ba mu kad'ai idan ba Mommy". Wafah tayi maganar.

    " Nid'in fah"Ta harareta da wasa.

    "Toh aike ba zama zaki ba ko sati bayi zaki ba nasan zaki tafi".

     " Wayace muku ko na tafi Abujan ai sena dawo kafin mu koma kuma ma tunda wannan abun ya faru ai ba lalle naje abujan da wuri ba amma de Mamin ma ya kamata ace ta dawo gaskiya".

    "Amrah tayi aure aka ce koh?"

    "Ehyi tana gidanta" Wafah ta amsa kafin Walida tayi magana dan ta lura da ta'be bakin datake.

     "Toh Allah ya bada zaman lafiya"

     Wafah ta amsa da ameen ,maganar batai tsaho ba suka shiga tasu Hannatu(Hajiya Hanne 'yar saudiya😂).

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now