Chapter 68

631 54 1
                                    


         Kasa shiga tayi ta koma d'akin baccinsu ta kwanta ita d'aya daren ranar baccin rabi tayi shi.Wajajen 4:43am Aasim ya tashi da kuka se d'akkoshi tayi ta dawo d'akin da'kyar ta iya lalla'bashi ya koma bacci,Shettima yana jiyo su amma ko le'ke dan shima rabi da rabi yayi baccin.

      Da asubahi bayan tayi sallah wajen 6:10am ta fita duba Rahinatu sede taga wayam bata nan ,Bello data ga ya fito yana bawa shukeshuke ruwa ta tambaya koya san sanda Rahinatu ta tafi yace mata ai mey gidanne da kansa ya kirasa a waya yace ya koreta idan ba haka ba zey rasa aikinsa.

    Jiki a sanyaye ta d'akko blanket data basu da plate da cups ta komo cikin gidan ,kitchen ta nufa ta shiga had'a breakfast amma hankalinta baya wajen tunanin yadda zata fuskanci Shettima take tasan ta gama 'bata masa rai.

     Da wuri yayi shirin office ya d'auki key da breif case d'insa ya sakko 'kasa 7:25am agogon parlour ya nuna Wanda rabonsa da fita irin wannan lokacin anjima se yau ,ko kallon inda hanyar kitchen d'in yake be ba ya fita ,Amrah tana kitchen ta jiyo fitar motarsa abinda ba'a ta'ba ba.

    Tun tana daurewa harta kasa 'kwallar data tarar mata ta tsiyayo kuka wiwi ta shiga yi a kitchen d'in dama da guntun ciwon kai datake ji abin ya had'e mata kafin ta kammala girkin zazza'bi ya rifeta da'kyar tayi breakfast ta koma d'aki ta kwanta tana addu'a kar Aasim ya farka.

    ***

Daga gidan Shettima Rahinatu direct gidan Mommy ta wuce ,sede bata iya knocking gate d'in ba seda taga rana ta d'an fito gudun karta takurasu.Kallon gidan ma kad'ai 'kara sata zubar hawaye yake gidan data taso a ciki.

    Yanzu dayake sun sallami mey gadi tun bayan tafiyarta basu da gateman shiyasa ta jima tana bugu kafin a bud'e,Imran da besan ta ba a d'ari-d'ari yake kallonta besan wace ba itama bata san waye ba.

  "Sannu yaro".

    Kai kawai yayi mata nodding yana jira yaji ta fad'i ko ita wace.

    " Mommy tana nan?"

     "Auhh..wajenta kika zo?"

     "Eh ita nake nema".

     " Wace ke d'in?"

       "Kace mata Rahinatu ce Rahinatu d'iyar Hannatu".

     Kai ya gid'a ya maida 'kofar ya rufe ,a kitchen ya tarar da Mommy ya shiga mata bayani yana fad'in Rahinatu ta gane , ya manta d'ayan sunan.

   Ba shiri ta fita zuwa bakin 'kofar ta bud'e gate d'in." Rahinatu ".

   " Mommy".Ta fad'a murya na rawa.

     Kallonta Mommy ta mayar kan yaron dake ri'ke a hannunta ya lafe a jikinta."Mommy kinga yanda rayuwa ta ta koma".

    Hannu ta bud'e mata bata jira wani abu ba ta 'kan'kameta se kuka ba 'ka'kautawa ranta kamar zey fita.Imran daga nesa yana kallonsu ya rasa meyake faruwa dan haka ya shiga gidan ya fad'a wa su Sa'adatu.Kafin ya gama bayaninsa Mommy suka shigo tana ri'keda yaron beyi mata 'kiwa ba.

    Sa'adatu ta rasa mey zatai kuka koh farinciki lokaci guda haushin yayarta ta ya fad'o mata tuna tsahon lokacin da aka d'auka bata gida har mahaifiyarsu ta rasu.

    Murtu'ke fuska tayi ta bar wajen Mommy ta bita da kallo Rahinatu da farko bata ma gane Sa'adatu ba ganin tayi girma tunda 'yan matan biyu ta gani harda Sameera daba ta sani.

  Husna ce ma kamarta bata 'bace mata ba ."Husna baki gane ni ba".Ta fad'a tana kallonta.

   Kai Husna ta gid'a alamar Eh,seda Mommy ta fad'a mata kowa ce ta 'karaso inda take tana fad'in."Yaya ina kika je?"

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now