Chapter 64

665 50 2
                                    

   
      Wunin ranar kowa baya cikin walwala,Wafah da Walida gabad'aya haushin Shettima ne ya kamasu shiyasa ita Wafah ko kiranshin ma batai ba.Shi kanshi yasan be kyauta musu ba sede hakan yafi akan ace sunzo gidan nata sanda zata tafin.

     Mommy kanta tun shigarta mota kukan yake so ya 'kwace dannewa tayi ta yi ,dan a yadda ta baro Shettynta ta gani a idanunsa damuwa fal a ciki kawai basarwa yayi.Dr ya kula da yanayinta sanda aka shiga jirgi ne ta saki hawayen daya ma'kale a idanunta.

     Dubanta yayi ya girgiza mata kai alamar ta dena,hannunsa ya d'ora kan hannunta yana murzawa cikin sigar kwantar da hankali.Daga baya de kanta ya kwantar a kafad'arsa yana fad'a mata magana 'kasa-'kasa oho banji mey yake cewa ba amma de naga ta share hawayenta.😝

       ***

      Amrah da shigowarta d'akin kenan ta tarar ya tashi daga baccin da d'azu ta tarar yana yi ,yanzun 'karar ruwa taji a bayi hakan ya tabbatar mata yana wanka ne.

    Bedsheet d'in gadon ta sake d'ad'd'amewa ta gyara pillows d'in ,wardrobe ta bud'e ta ciro masa kayan saw a,blue jeans da red shirt shortsleeves.A bakin gadon ta ajje su dede lokacin ya fito daga bayi d'aure da towel.Murmushi ya sakar mata yana kallon kayan data ajje d'in."Ina kika shige yau my starlight?".

   "Kai de zan tambaya nida kusan sau uku ina shigowa d'aki dubaka sena tarar baka tashi ba".

    " I'm sorry my Amrah yau kin ganni duk se a hankali koh? Mommy ta gudu ta bar 'ya'yanta".Yayi maganar yana 'karasawa jikin mirror.

    "Allah sarki ni su Walida nafi tausayawa wlhy suda basi sallama da ita ba".

    " Toh ko kece kika fad'a musu ne  nide an kira ni ana kuka yanzu ma nasan haushina suke ji".

    "A'a ni ban kirasu ba,dole suji haushi kuwa ni kaina banji dad'i ba".

    Man shafawa ya d'auka ya mi'ka mata tare da kamo hannunta suka zauna daga bakin gadon.

   "Misali kece kina da yara uku zaki tafiya mey nisa ya kike tunani sallamarku zata kasance dasu?"Ya 'kare maganar yana tsireta da ido.

   " Toh ai ni bansan ya ake ji ba tunda ba ta'ba yin 'ya'yan nayi ba".Tayi maganar tana tsiyayo lotion d'in a tafin hannunta.

   Murmushi yayi "Ai imagine zaki ki gani ".

   " Allah ni bansan ya ake ji ba".Ta shagwa'be fuska.

    "Toh zaki sani ai at time da kika haifo mana children 7 biyu Mommy ta kar'ba uku Ummi  biyu Aunty Mirah se mu zauna zero."

    "Hun'uhn".Ta furta.

     " Kin gani ba harkin tsure kalle ki".Yayi dariya tare da kama cheeks d'inta da yatsu biyu amma bada zafi ba.

   "Da gaske bazaki bawa Ummi ko Mommy ba?"

     "Ni ban fad'a ba".

      " Toh ko sha biyu za'ai kinga se a rage miki 5 ai sin isa ko?"

    Batace komai ba ta cigaba da shafa mishi man,kayan ma ita ta taimaka masa yasa sannan suka sauka 'kasa cin abinci dan ko abincin rana beci ba se yanzun.

      Mommy bayan sun isa a wayar dr ta samu ta kirasu Mami take sanar musu sun isa bayan nan ta kira Shettima ma sesu Walida masu fishi.😂

   A wayar kuwa kamar sayi kuka da suna magana da ita ,Wafah ce harda cewa wai Mommy kin tafi kuma nasan ba'kya nan sanda Edd na se shiga.(Lol kowacce ta zama jaruma Mommy tayi nisa kuma😚).

    
    ★★★

     A yayinda Mommy tana chan Amurika ita da mijinta doctor suna cin amarcinsu ,bataliyarta suma suna nan  suna gudanar da harkokinsu yara su Imran suna ta lissafa kwanakin da Daddynsu yace zey sa a taho dasu wajen Mommynsu.Tsohuwa da Mami suna shan bari-bari ,su Sameera da Sa'adatu 'yan mata masu tasowa su yanzu basu a rashin jinnan an girma kuma sede suma ana sa musu ido kan yadda suke tafi da rayuwarsu abinda aka ga zasu kauce hanya a gyara musu Mommy ma tana 'ko'karinta koda bata kusan idan tayi waya dasu tana musu 'yan gyarar raki.Yaranta na gidan aure ma hakan suma tana musu Shettima mah da Amrahn bata barsu haka ba.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now