Chapter 18

604 46 0
                                    


           "Arrest him"Jami'in ya fad'a.

       Cikin hanzari guda biyu suka tunkaro kan Shettima zasi saka masa ankwa.

      " Officer mey kuke nifi?"Cewar Kawu.

      Mommy already idanunta ya fara tsiyayar hawaye,Shettima tsaye yayi a gun kamar statu.

        "Yalla'bai mun samu kwalbar poison a d'akinsa Jami'in ya d'aga hannunsa ri'ke da kwalbar poison dake a killace a farar  square shape bag.
  
     Cikin tsananin mamaki da firgici kowa yake kallon 'kwalbar ,Mommy kawai girgiza kai take komai ya jagule ji take ina ma ace mafarkine taya d'anta za'ace ....kai bazey ta'ba yuwuwa ba ko kunnene a jikinta gabad'aya bazata ta'ba yarda ba.

     " Officer ka gane mana ,wannan yaron da kake gani ba wani bane face d'an mamacin taya za'ai d'a ya kashe mahaifinsa idan ma hakan is possible toh nide Shettima na bazeyi kisa ba wlhy"

    "Hajiya a matsayinmu ma jami'an tsaro ,mu d'innan da kike gani ba tafarar d'aya mi'ke fad'ar abuba se minyi bincike ,saboda haka wannan yana d'aya daga cikin binciken da mukai,maganar d'ansa ne wannan ba abin mamaki bane kiga an samu d'a ya kashe mahaifinsa amma nan ba inda za'a tsaya bayani bane idan munje station za'a warware komai"

     Gabad'aya kawu kansa ya d'aure ya kasa sake cewa komai dole se anyi bincike an gano wannan gaskiyar lamarin amma abin da mamaki.Shettima yana ji yana kallo suka d'aura masa ankwa shide kallonsu kawai yake amma a halin yanzu hankalinsa baya jikinsa komai ya jagule masa.

    "Wannan yaron baze ta'ba aikata abinda kuke zarginsa ba bazamu yarda ku tafi dashi ba" Aunty Hannatu ta saka kuka tana 'karasowa inda suke.

   Walida,Mami ma kukan sike Rahinatu mamakin babarta take yau itace da yiwa Shettima kuka anya...

       Mommy ganin da gaske zasu tafi dashi ta ru'kun'kumeshi kamar zata maidashi cikin jikinta gam ta'ki sakinsa hawayene kawai yake ambaliya a fuskarta har wani dishi -dishi take gani 'kwa'kwalwarta tayi mata nauyi.

    Su kansu 'yan sandan kallonta suke su ba abin su fisgeta ba daga jikinsa duk yadda sukai da ta sakeshi ta'ki tayi fafur sede idan da ita za'a kaishi ,ta fad'a musu bashi bane d'anta baze ta'ba kisa ba amma sun'ki ganewa.

     "Fatima ki saki yarannan kiyi ha'kuri bazan bari su tafi dashi ba ba tare da na bisu ba ,za'a dawo dashi ba abinda zey faru nima nasani yarannan bazeyi abinda ake suspecting ba" Kawu yayi maganar cikin tausasa harshe ko zata sakeshi.

   Kai kawai take girgizawa taki cikashi,idan aka d'auke mata shi ina zata sa kanta after all mijinta ya rasu and now ga d'anta ana so a rabata dashi.

      "Mommy" Ya kira sunanta muryarsa a raunane shi kad'ai yasan yanda yake ji a cikin ransa a halin yanzu.

     A hankali ta d'ago da kumburarrun jajayen idanunta ta kalleshi "Shettima ka fad'a musu bakai bane, nasan bazaka ta'ba yin haka ba.." Kasa'karasawa tayi saboda kukan daya ci 'karfinta.

    Hakan ba 'karamin sake karya masa zuciya yayi ba kukanta yana tsorata shi matu'ka ,shikanshi yana bu'katar space da zeyi kukan  daya cika masa zuciya.Yasani a yanzu Mommy tana bu'katar wanda zasu kula da ita ko zuciyarta zata rage rad'ad'in rashin mijinta da tayi.

      "Kidena wannan kukan Mommy komai zezo da sau'ki inde kin yarda bani nayi hakan ba".

    " Nasani bazaka ta'ba yi ba".

      "Zan dawo Mommy kinji"

      Hannunsa dake sa'kale da ankwa ya zame daga jikin Mommy sabon tashin hankali Walida ,Wafah,Sa'adatu da Husna duka sukai raja'u suma suka 'kan'kameshi.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now