Chapter 67

619 45 1
                                    

     
    Juyo da ita yayi suna facing juna har yanzu ta'ki sakin fuska.

     "I'm sorry Umman Wasim".

      Gira ta had'e tace " Ni ba Ummah bace kuma ba Wasim ba Aasim".

     "Bakya san Ummah se me ?"

      "Ammi".

       "Yanda kika ce rakin ya dad'e,amma yanzu ayi min murmushi ko zanji sa'ida".

    Murmushi ta saki  yana sake matso da ita kusa sukaji 'karar fashewar glass,dukansu suka maida kallonsu wajen.

    Basusan lokacin daya sauka daga kan gadon ba ya zagaya jikin mirror kwalbar humrah d'inta ya ciro daga cikin locker na mirror ya sake ta a 'kasa da turaren duka.

    " Kai!".Ta 'karasa wajen da sauri ta kama kunnensa se raba ido yake duk ya rikice da tsawar datai masa.

    Saurin janyeshi yayi ya d'aukesa "Sekin firgita shi akan wani turare".

   " Au baza a 'kwa'beshi ba".

    "Shi meya sani d'an 'karami dashi,rabu da ita".Ya 'kare maganar yana goge masa hawayen daya soma tsiyaya.

    " Sannu baban shagwa'ba kuka ma kake,anjima ai zaka nemeni neh d'annan" .Tayi 'kwafa ta fita daga d'akin d'akko kayan da zata gyara wajen.

    "Bye-bye". Sukai mata waving.

    " Zakuga bye-bye".Ta fad'a tana huci haushi ya isheta humrahnta mey 'kamshi ya mata asara.

    ***

    Mommy sati biyu da zuwanta Nigeria ita da 'ya'yanta suka fara tahowa ,murna a cikinsu ba'a misaltawa barin ma su Walida da a yanzu 'ya'yansu sunyi girma sun taso kusan kai d'aya gashi Wafah ma ta sake haihuwa ta biyu ta haifi namiji a yanzu yana da 6 months an saka mashi Muhammad.Sede fa Mommy bada iya yaranta uku tazo ba harda d'an boy Abdallah 🙈 wannan dalilin yasa ta'ki zuwa Nigeria da wuri har seda ta haife dan kunya take ji ko yanzun ma haka ,su Walida kansu sunsha mamaki dan abin yazo da bazata se haihuwa suka ji doctor ne ya fad'awa tsohuwa Mami taji Mommy kunya yasa ita ta kasa fad'a.Su Walida anyi 'kani,sunyi gumm da baki sanda suka je mata sannu da zuwa suka ganshi d'an beauty watansa 3 duka ya had'a kamannin iyayen wani sa'in seyai kama da Nana wani lokacin kuwa Shettima🙊(Su Shetty fa anyi 'kani😂).

    Ai lokacin da yaji Mommy ta haihu 'kin fad'awa Amrah yayi ,se a bakin Ummi taji ita kanta abin yaso bata dariya harma da kunya da'kyar ta iya yin waya da ita tayi mata Allah ya raya.

    Shiko doctor ko oho murnarsa ma yake ko a jikinsa.

     Yau doctor zey duro shima gida Nigeria Mommy se preparation ake,'yan mata Sameera da Sa'adatu sune masu taya Mommy dan tunda ta dawo suka komo nan suma ,su Nana  sun sake girma an d'an fara rage 'kiriniya suna jida 'kaninsu akansa suyi ta fad'a kowa yana shi zey d'aukesa.

    Imran yanzu baya shiga shirginsu shi wai ya zama big boy.Da misalin 7:20pm driver ya d'akko doctor a airport,suna parlour suka  jiwo shigowarsu kusan a tare suka fita harda Sameera garjejiya ta ruga da gudu ta d'are  Daddynsu kusan shekara uku rabon data ganshi.

    "La'ila zaki yarda ni Samee haka kika zama ?"

    "Daddy nid'in?"

    "Eyyi kin zama 'yan mata"
 
   Tafin hannu tasa ta rufe fuskarta tana dariya,Nana ce ta ri'ko masa hannu ta gefe tana fad'in."Daddy ni baka d'auken ba".

    "Duk girmannan naki,yanzu ai sede Abadallah kuma".

    " Shi ai yayi bacci".Ta fad'a suna takawa zuwa ciki.

TAGAYYARA(Complete)Where stories live. Discover now